BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

Granny itace ta dauki nauyi komai na gidan tunda anyi anyi dani kan na dawo gidan da zama har Mimi ta haihu naki ya Umma ma babu yanda bata yi dani ba, Amjad da kanshi ya turo Jahid gurina wai ya rarrashe ni naje na kula da Mimi fafar naki nace nima makaranta, lokacin mujahid har fushi yayi dani ya daina kirana a waya, kwana uku, nima shareshi nayi na cigaba da sabgata, da yaga Uwar bari ne yazo har inda nake ni kuma a lokacin na butsare masa sai ya dinga bani hakuri muka cigaba da sosyayar mu Cikin aminci da yardar juna.


Tun da watan azimi ya kama yake zurga-zurga har sai da ya tabbatar komai ya kammala ta fannin company shi sosai ake aiki tare da fidda kaya samfura iri-iri abun sai son barka sosai jama’a suke tsallakowa daga garuruwa suna zuwa d’aukar kaya.

Yaduka na mussaman ya sanya company ya shirya masa mai manyan zane ko wane kusan bandur dubu aka futa dashi gidanan yari(prison) bayan nan ya sanya aka futa da bandura na tampopi aka dinga shiga kauyi ka ana rabo, hatta da takalma sai da aka futa dasu aka rabawa mabukata.
Farkon wata kenan tsakiyar wata ma haka ne ya kasance, karshen wata ma haka.
Addu’a da fatan alkairi babu irin Wanda bai sha ba abakun mutanan gari

Yau saura kwana bakwai sallah.
Muna ta shirye-shiryen sallah. Lokacin Cikin Mimi ya futo sosai tunda yana matakin watanni shida tayi kiba sosai sa sosai kuma ta kwantar da hankalin ta.

TV muke kallo inda muke kallon tafsiri daga bakin Marigayi shak Isa Waziri Allah ya jikansa.

Kawai. Umma ta kunna redio murya wani shararan Dan jarida muka ji yana fadin”Salamu alaikum jama’ar jahar kano, labari da dumi-dumin sa, an yaka dai ta tashi yanzu-yanzu muka samu labari daga majiya me k’arfi shararar mutumin nan Wanda yayi suna a jahar kano, wato Young millionaire Amjadu Abul Abbas mai nasara wato mamallakin wannan shararan company me kawo muku nauin kayan sawa kama daga atamfoffi yadiga lesuka mayafai dogwayen riguna bulawus kayan yara hijab da sauran su, wannan company mun samu labari yanzu yanzu daga bakunan wadanda suke sari a cikinsa, cewa company ya hada baki da yahudawa nasara masu yak’i addinin musulunci masu adawa da fad’ar Annabi Allah wato Annabi Muhhamadu Slw a takaice dai an samu jikin takalman da company ya ke kerawa kasan takalmi an rubuta sunan Allah da manzon sa wato Allahu Muhammad, Jama’ar gari me zaku ce da wannan shirkar da wannan yaro da kuka amunce masa ya aikata.””

“Innalillahi wa’ina ilahi raji’un shine abunda Umma take fad’a, take ta fashe da kuka tana gyda kanta take fad’in” Wannan zan sharri ne tswagaran sa na tabbatar yaron nan bazai aikata wannan danyan aikin ba.”

Nima jikina wani irin shocking yake jin abunda Dan jaridar yaje fad’a, Cikin zuciya ta nace”Anya kuwa guy nan zai aikata Wannan Abu, duk da dai nasan Duk ak’idun shi na nasara ne kuma Duk yawanci abokan shi turawa ne, wata zuciyar tace min tabbas zasu iya rinyarsa dama ba wani tsoron Allah yake ba, tunda yana aikata zina.” Kuka Umma take yi sosai da sosai Ya Aminu ya shigo gidan hannunshi rike da Leda me zane-zane da Lemo da a yaba a ciki.
Ganin Umma na kuka ya tabbatar labari ya same su
Umma tace”Kaji sharrin da jama’ar gari sukaiwa wannan yaron mijin Mimi ko.”?
Ya Aminu ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya yace.” Duk naji Umma gashi can ko ina ana surutu zancan ya cika gari.
Matasa sun fara gazgatawa domin wani Dan kasuwa ya futo da takalma na company an duba an ga gaskiya al’amarin.
Umma tace.” Karya ne sharri ne aka shirya masa ni na tabbatar.
Ya Aminu yace.” Umma sai ta iya kasamcewar gaskiya ne Wallahi mutane da basa tsoron Allah, ni dama wannan uban kud’in sa suna tsorata ni, akan ya samu duniya babu abunda ba zai yi ba.”
Nace”Wallahi Ya Aminu nima na gasgata saboda d’abi’un sa duk na turawa ne.
Gaskiya gomnati ta shiga maganar kuma kamata yayi a dauki mataki akan sa, domin Allah da manzon sa ba abun wasa bane.”

Ya Aminu ya bude baki zai yi magana kawai mukaji ihu!!! Da hanayi ana gudu radadada!!! Da gudu nayi waje ya Aminu ya biyo ni a baya.
Gungun matasa majiya k’arfi ne suke tada k’ura ko wanne hannunsa rike da makami wasu jarkar fetur da kalamzir da tayoyi suna fadin “Billahillazi sai mun k’one company mu zai yaudara! Sai mun konashi mu kashe shi!! Mu kashe banza.”!!!!!!!!!
D’uuuuuu suke wucewa sunfi su Dari ga magariba ta gabato ana shirye-shiryen shan ruwa
Umma ta tsorata mutuka fad’i take” Asma’u maza buga wa Mimi waya ta tawo gida innalillahi wa’ina ilahi raji’un. ” Jikina na kyarma! Na koma cikin gida zuciya sai harbawa take yi mutukar wad’annan matasan sukayi arangama dashi to babu shakka sai sunga bayan sa, hannuna na rawa nake Neman numbar Mimi, kiran duniya taki shiga. K’afafuna na rawa na futo in na fadawa Umma halin da ake ciki.

Hannunshi rike da jarida yake zagaye parlor bashi, Rambo da doh Mimi da granny duk suna tsaye suna tararrabi da al’ajabin wannan Abu.wayoyinsa kuwa tuntuni ya sanya rambo ya kashe su, saboda a halin da yake ciki magana ma bazai iya yi ba. Shin wai me ya tsarewa mutane ne a duniya.?

Granny kuka take yi tana fadin”Wannan kaddara da masifa Allah ka ije mana ita, Ubangji kaga zuciyoyin mu bamu aiktaba Allah ka tona asirin masu San su ga bayanmu.

Granny ya rungume a jikinsa yana d’an dukan bayanta da hannunshi ya ma kasa cewa komai, idanunsa sunyi wani irin jajazur! Tsabar tashin hankalin da yake ciki.

Tv suka k’urawa ido inda suke ganin jama’ar gari kofar company sa sune turareniya da rigima da masu gadi kan lallai sai sun shifa ciki wasun su kuwa tuni sun soma k’ona tayoyi suna watsa fetur da kalanzir jikin company, ihu! Da hayaniya ya cika gurin, ‘yan jarida sai dauka suke yi. Tuni wani tsagera daga cikinsu ya k’yatta ashana ya yi wani tsalle hade da jefa ashanar sama, kafin k’iftawa da bisimillah wuta ta kama fa!fa!fa! Jikin gatangun company har ta soma haurawa ciki, hucin wuta yasa jama’a darewa kowa na gudu domin ceton ransa, ciki kuwa har da masu gadi.

Tuni matasan suka samu damar shiga ciki kasancewar gurin ya hargitse kowa na ceton ransa.
Take ‘yan jarida suka rufa musu baya domin dauko rahoto.
Lungu da sak’u ko ina sai da suka bi suka watsa fetur ko zafin wuta basa ji, da gudu ma’aikatan suka dinga futowa suna kama Katanga suna haurawa domin ceton rayukansu, ganin yanda wuta take ci ne ba!ba!ba! Yasa ‘yan jaridar dasu matasan suka dinga gudu suna kama Katanga suna dura kasa, duk da haka wasu sun jikkata kuma sun k’one cikinsu sudai kawai burin su ya cika ganin sun rusa company.


“Hahahahahaha” wata mahaukaciyar dariya na juyo a ofis din me girma governor, da sauri na lek’a ta k’afar mukuli, na gansu sun fi su goma zaune Cikin kujeru tsakiyar su kwalebe ne da cup reras kan wani makeken teble. Mai citta ya dauki abunda yake cikin cup din gaban sa ya kurba tare da ajewa fuskarsa cike da annuri da farin ciki, naji yana fadin”Shegen kaya! Wa yaga masa barno gabas take! Ai sai ya daina motsi a duniyar nan sannan zamu saurara masa.”!! Dariya suka shek’e da ita “Hahhahahahahaha.”!!!!


Har aka sha ruwa yana tsaye a tsakiyar parlor babu yanda granny bata yi dashi ba kan yazo ya karya yak’i kamar ma kurma ya zama Wanda baya ji ba ya gani, kawai ya zubawa guri guda ido .Su Kansu Rambo da doh-doh sun tausayawa masa.
Mimi na kuka tazo ta rungume shi tana rarrashin sa, da sauri ya juyo jin tsinin cikin ta yana zungirin shi a bayan sa.
Tsungunawa yayi ya kasa kunnesa cikin NATA yana lumshe ido.
Kamar wani zautacce ya d’aga rigar ta yana shafa cikin nata, a hankali yace.” My boy ina cikin damuwa!!!! Innalillahi wa’ina ilahi raji’un. “!!! Kalmar da ya kamata ya fad’eta tun farko fara abun bai fada ba sai yanzu Allah ya bashi iko.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button