Uncategorized

HAJNA 29-30

 ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE :29-30

*************************

Babban yayan su Joseph ne ya ja su a mota wanda zai yi shekaru 19 a duniya, Elizabeth ce ta zauna kujerar gaba, Momy da su Katrina kuma suka zauna a baya, wanini babban shopping mall suka nufa dake lagos, shiga suka yi ciki, kowa yana duba abunda yake so, wanda dama al’adar su ce, idan aka zo kowa zai ɗauki abunda yake so sai momy ta biya, momy kuwa gurin siyen snacks ta nufa, cakes ta siye kala daban daban, sannan ta wuce gurin siye gift, wani tsadadden

agogo ta siye mai masifar kyau da tsada, su Elizabeth ne suka zo, ko wacce daga cikin su ɗauke da kaya niƙi-niƙi, umurni ta musu akan suje su kai kayan yanzu, atm card ɗinta ta miƙawa Joseph, “ka basu su cire kuɗin su “ta faɗa, ni kuwa mamaki ya kama ni dama tana jin hausa ashe, kuɗi suka biya, itama tazo ta biya nata, sannan suka wuce, “momy hala Uncle zai zo gobe?” Joseph ya tambaya, “eh Joseph, gobe zai zo”, Juliana tace “momy what are you saying “(momy me kuke cewa), murmushi maman tayi sannan tace “your brother is asking about ur uncle” (yayan ku yana tambaya na akan uncle ɗin ku), “ohhh mom, when is he coming “Katrina ta faɗa(mom yaushe zai zo?), “tommorow” (gobe) ta faɗa a taƙaice, se yanzu na fahimci cewa yaranta ƙanana basa jin hausa. 



    Gida suka koma, inda tun cikin daren momy da Elizabeth suke aiki a kitchen, kuma tun da safe ta tashi, yau su Elizabeth ba zasu makaranta saboda ana good Friday, ba’a makarantu, wanda haka yayi matuƙar yiwa yaran daɗi. 



   A ɓangaren Hajna kuwa bata nemi Qaseem ba haka shima, abun yana damun ta, kenan ita kaɗai ta damu da Qaseem ko minene, wanka tayi ta shirya cikin riga da wando waɗanda suka yi matuƙar yi mata kyau, wayar ta, ta ɗauka ta fara chart. 


  Qaseem kuwa rashin ganin Hajna na yau yana damun shi, sai yake jin haushin ta da bata zo ta neme shi ba, gashi shi dama haka yake, idan yayi fushi dake baya neman ki sai bayan kwana uku, gashi ze yi tafiya, tunani yayi ko yaje ɗakin ta, amma sai ya fasa, kuɗin ta ma Favor ya ba dubu ɗari biyar ta kaima Hajna, shi kuma ya nufi airport, jirgi ga hau zuwa Lagos. 


   Hajna tana ɗaki zaune Favor ta shigo, kuɗi ta miƙa mata tace “gashi inji boss “, karɓa tayi tace“nagode” a je su tayi cikin drawer dan ita bata da buƙatar kuɗi, Favor ta fita dan ta isar da saƙon ta, yadda aka bata haka ta kai su. 



  ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^


Fahna! , kwance  take akan gado inda take ta waya hankalin ta kwance, bayan ta gama wayar ne tunanin kiran Hajna ya zo mata a rai, kiran ta  tayi, aka yi sa’a wayar na hannun ta, ɗagawa tayi “hello Fahna “Hajna ta faɗa, “hello Hajna, ya kike?” Fahna ta tambaya, gaisawa suka gama yi sannan Fahna tace “Hajna gobe zamu shigo Abuja zan so gidan ku “, Hajna tace “ohk Allah ya kaimu, dama ina da damuwa wallahi”, Fahna tace “damuwar me”, Hajna taja dogon numfashi, sannan tace “Qaseem ne Fahna, baya kulani tunda muka zo, aka yi na marmari”, Fahna tace “ke bazan ce, baya samun abunda yake so gurin ki ne shiyasa”, Hajna tace “kamar ya kenan”, Fahna tace“ki bari sai nazo na baki shawara “, nan suka taɓa hira, knocking ƙofar ɗakin Fahna aka yi,“Hajna alhaji Kabeeru ne zai  shigo muyi magana gobe in na zo”, Hajna tace “waye kuma alhaji Kabeeru? “, Fahna tace “wani sabon alhaji ne na haɗu da shi, ina gaya miki ƙawata ya haɗu, ga daɗin harka ga sakin aljihu, kinga bari na buɗe mishi kar na barshi yana jira” ta ƙarasa maganar tana sauka daga kan gado, ƙofa ta bude mishi, rugume shi tayi, cikin salo irin nata tace “Alhaji na sannu ta zuwa “, “yauwa shalele na, gani nazo”, ƙara narke mishi tayi a jiki, cikin rikitaccen salo tace “me za’a bani “, “zuma” ya faɗa yana me turata kan gado, ba shiri ta jawo shi ya faɗa mata a jiki, haɗa bakin shi da nata yayi, wanda ya sani gaggawar ja musu ɗaki kar in ga abunda ya fi ƙarfi na. 


    **************************************

Kasancewar jirgi Qaseem ya hau, awa ɗaya yayi ta kaishi Lagos, murmushi yayi lokacin da ya hango sister da Joseph tsaye, da alama shi suka zo tarba, tafiya yake cikin taƙun ƙasaita har ya iso gaban ta, buɗe mishi hannu tayi murmushi ɗauke da fuskar ta, rungume ta yayi yace “i missed you sister “, haƙoran ta suka bayyana sosai tace “i missed you more”, murmushi Joseph yayi yace “good afternoon uncle “, “good afternoon Joseph ” Qaseem ya faɗa yana rungume shi, daga nan sai suka ɗunguma zuwa mota, inda suka nufi wani haɗaɗɗen estate, cikin naga sun dannan kai, gaba ɗaya, daga cikin ginin naga sunyi parking mota, ciki suka shiga, da gudu Katrina da Juliana suka zo da gudu suka rungume shi, a tare suka ce “you are welcome uncle, we missed u”(sannu da zuwa uncle, munyi kewar ka”, a tare ya ɗaga su  sama, sannan ya sauke su, gaisawa suka yi da Elizabeth, sannan suka zauna a dining area, a tare suka ci abinci suna ta fira, shi kuwa Qaseem sai tsonar Elizabeth yake, “dama haka kike bakya son magana, ƴar ƙauye kawai”, momy tace “taji kar ka dame ta “, Katrina tace “Uncle why are u speaking hausa, what are you saying”(uncle miyasa kake yin hausa me kake cewa) , dariya ya fashe da ita yace “hey u aunty, yaran ki akwai gulma “, dariya tayi sannan ta ja kumatun shi tace “gado suka yi gurin ka”, “kema kinsan bana gulma ai “, Juliana tace “Uncle i think she was just asking u something”(uncle ina tunanin yanzun nan ta tambaye ka abu) ta faɗa tana nuna Katrina, dariya ya sake yi yace“Aunty duk gulmar yaran ki sai sun barni, in zaki koya musu hausa ki koya musu, ba wanda zai sani yin magana da Hausa, kuma in fassara da turanci “ya faɗa yana dariya, Elizabeth tace “abeg let’s go, u guys are disturbing uncle” (muje kuna damun uncle “ta faɗa tana kama hannun yaran, Qaseem yace “good bless u my kurma daughter” (Allah ya miki albarka ɗiya ta kurma), Momy tace “kai dai kana nan baka canza ba, kayi ta tsokanar mutane”, murmushi yayi yace “i learn that from u”(na koyi wannan daga gare ki ne), parlor suka koma, nan ta ke tambayar sa Trisha, murmushi yayi yace “Trisha tana can Abuja, yanzu ai nayi sabuwar beb ina gaya miki yarinyar ta haɗu”, “dan Allah fa? “Aunty ta tambaya, murmushi yayi yace “yeah sunan ta Hajna Ibrahim”, “wow Hajna, nice name, muga hoton ta, nan yake nuna mata, sosai Aunty ta yaba da kyan Hajna, “amma Qaseem miyasa bazaka aure ta ba? “, murmushi yayi yace “ai ban shirya aure ba, ni kawai so nake na mori jikin ta yadda ya dace”, duka ta kai masa, sannan tace “Qaseem listen to me attentively, Hajna ba kalar matan da ya kamata ka ɓata bane, Hajna kalar macen da kowa ke so ya aura ce, ka kalle ta a hoton nan, dubi shape ɗin ta, duba dirin ta, Trisha da kake so wallahi ko zaka mutu bazata aure ka ba, kuma wannan Hajnar tafi Trisha kyau”, dariya ya soma yi har da riƙe ciki, harara ta kai mishi sannan tace “ duk yadda zan faɗa maka ba zaka gane ba, ina fatan ka gane lokacin da guri be ƙure maka ba, yanzu faɗa min yaushe zaka koma “, “kora ta kike yi”, murmushi tayi tace “ni da nayi kewar ka, ya zanyi na kore ka, so nake nasan kwana nawa zaka min “, murmushi yayi yace “sati ɗaya zan miki kamar ko yaushe”, aunty tayi farinciki sosai da jin haka. 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button