DARAJAR ‘YA’YANA PART 1

Ban gane na neke ta share ki ba?Ta ce na gane
yau duk ka canza ko na ce abubuwa sun canza
kamar ba mijina ba maita rairayata?Ya dago ya
dubeta baki min komai ba.Ta dora hannunta a
kan cinyarsa, abba kausar to naganka ne ni yau
irin kamar banyi kyauba din nan.Ya kalleta Dan
Allah ki barni ina yin abu mai muhimmanci ne.Ta
ce, amma dai da aka saurare ni bai fi abin da ka
ke yi muhimmanci ba?Ga mamakinta sai kawai
taji ya daka ma tsawa,kin san me kike fada kuwa
dan Allah tashi ki bani guri a nan,ta zaro ido,
mikewa tayi ta nufi kan gado ta kwanta a ranta
tana cewa ka gama kazo ka same ni ina nan
kwance.Abin ta’ajibi ranar dai haka ya raba dare
yana harkokinshi a internet sabon abu ga Sadiya
mutumin da in yazo satin karshen mako hatta
wayoyin shi kashewa yake suna manne da juna
har sai ya tafi yana cike da kewarsu.Ko da ya
kashe laptop ya kwanta juya mata baya yayi,don
Allah babban kausar me yake faruwa ne?Dan
Allah in wani abu ya faru ne ka sanar dani zan
baka hakuri, ban saba da wanan rayuwar
ba.Cikin zafin rai wanda banta ba ga ni ba ya ce,
nace bakiyi mini komai ba, kina son dole sai nayi
maki karya ne?Dan Allah ki bar ni in huta ki barni
na ce.Ta rike kai to banyi maka laifiba me yasa
ka canza min?Nasanka kai mutun ne mai bukata
a marmatse ka ke zuwa in kayi saty daya, wanan
satyn har saty biyu kayi amma sai naga kazo
bana gabanka.Ya zoro ido to yau ban da bukata
ko dole ne?Ya ja tsaki, tashi dan Allah taf dakinki
bana son jaraba kada ki dameni.Kuka ne ya
subuce mata, ta fita a dakin tunda aka kawota
gidan yau ce rana ta farko da zata kwana a
dakinta ita daya.Dan ko haihuwa tayi basa raba
makwanci, ta fito falo ga mamakinta sai taga
kausar tsaye a falo tayi saurin dai daita fuskarta
tare da share hawayenta ta nufi kausar.Me kika
fito yi?Kausar me kike so?Ta ce, mome naji abba
ne yana fada ne, me kika yi masa?Ta kama
hannun yariyanyar suka nufi dakin yara.Kan
katifarsu ta kwantar da ita ta kuma ta kwanta a
bayanta tare da rungumeta, kausar ta sake
tambayarta momi kinyi laifi ne Abba ya ce ki fita?
kasa magana tayi don al’ajabi ne ke dankare cikin
ranta, ta danne hawayenta ta ce kausar laifi nayi
masa.Kausar ta ce, momi ki bashi hakuri
mana,’to’ Sadiya ta ce zan bashi sai da safe in ya
huce kinji?Kausar tace, eh.Sadiya ta ce ki daina
tashi cikin dare kin ji, tadinga shafa kan yarinyar
tana lallashinta hartayi bacci ita kuma ta koma
duniyar tunani tuno farkonsu.Iya mahaifiyar Aliyu
ya ce ga mahaifiyata, uwarsu daya ubansu
daya,su ‘yan asalin jahar jigawa ne, a karamar
hukumar Hadeja.Mahaifiyarsu ta rasu ta barsu su
hudu mazabiyu mata biyu, kawu Adamu da kawu
Dauda duk iya ce babbar su.Lokacin da
mahaifiyata ta na budurwa, dan haka iya ta
dauketa lokacin suna zaune a Dutse da mai
gidanta da yaranta hudu.Yaya sulaiman
yayazakari, yaya sani, sai cikin yaya Aliyu.Mijinta
ma’aikacine a ma’aikatar gona ta jahar Jigawa,
daga baya yayi ritaya inda ya dawo kaduna da
zama sana din dan uwansa dake noma.A
unguwar mu’azu ya sai gida madaidaici a ciki aka
haifi Aliyu kuma a nan aka aurar da mahaifiyata
inda ta auri mahaifina wanda yakasance
ma’aikacin gidan Raidio kaduna.Amma dan zariya
ne kuma zariyar aka kaita,yana da mata biyu da
yara kusan goma, ko a lokacin.Maimuna
mahaifiyarta ta kasance mai hakuri da juriya, duk
da cewa bai kasance mutum mai cika hakkokin
iyalansa ba.Amma bata taba kawo kararshi gurin
iya ba,don tasan iya tana da fada sam bata da
wasa.Shekarar da yaya sulaiman yayi aure
shekarar ce mujin iya Allah yayi mai rasuwa,sunji
mutuwar ta farat daya yana cikin sallah yayi
sujjada a masallaci har aka idar bai dago ba.An
dago shi sai gawa, ashe mutuwar kenan.Yaya
sulaiman koyarwa yake yi a makarantar yan mata
dake Tudun wadan wada wato Sai yaya zakari
kasuwanci a babbar kasuwar kaduna, duk da
cewa ba wani babban dan kasuwa bane,Sani
kuma da ya gama secondary sai kurum ya shiga
wurin gyaran motoci dan a lokacin babu halin ci
gaba saboda yanda karatu ya zama a kasarmu sai
yayan masu shi.Talaka yana so yake hakura.
Ya
Aliyu karamin su kuma suna tallafa mashi don
ganin ya samu karatunshi, kwanci tashi suma duk
suka yiyyi auransu.Lokacin da mahaifiyata tana
dauke da da tsohon cikina don ta jima bata haihu
ba, har lokacin iya bata gane yar uwarta tana
cikin matsala ba, sai bayan ta haife ni.Lokacin da
taga komai babu, abin ci a gidan gashi ya sake
yin aure ya ciko mace ta hudu,iya ta same shi ta
ce, yanzu tsakanika da Allah Abubakar hakan da
kake yi dai dai ne?A ce ka ajiye mata babu
kulawa ba abinci badai baka da shi ba sai don
zalunci?Ya ce ai za a siyo.Tace, gara ma ka siyo
don ba zan dauki zama da yunwa ba, in an ganka
a waje kwas kwas har da mshin din hawa gareka
amma a gidanka da yunwa.A daddafe akayi suna
inda aka rangada min Halimatu Sadiya, iya ta tasa
mahaifiyata ta tafi da ita, tace ba za a bartaba
haihuwar fari ba kulawa ba,Ita kenan gareni dan
wadan can yan uwan namu sai munyi tafiya mai
tsawo kan mu gansu.Sai da mahaifiyata tayi
kusan wata shida lokacin ni da ita munyi bulbul
tamkar kada iya ta bari mutafi, amma yanda
mahaifina ke ta suntirin zuwa yana kuma turo
mutane don baiwa iya hakuri sai ta hakura tace
mu koma.Amma ta ja masa kunne sosai, to dan
saukin yanzun ba kamar da ba, hakan yasa ki
shiyoyin jin haushinta suna ganin ya fifitata shi
ko tsoron karr a dauke ta ne don iya ta tabbatar
masa in tazo taga ba daidai ba to zata tafi
damu.Shakarata biyu ta sake samun wani cikin
tun yana karami take fama da laulayi iya tana
zuwa tare da yayanta akai akai suna duba
mahaifiyata tare da kawo mata abubuwa.Iya taso
ta tafi dani amma lokacin an ce inna da kalafucin
uwa, kulafaci gareni sosai ta hakuraKu ziyarci blog
dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Gurin haihuwarta kuma taji jiki da kyar ta haifi
yar bubu rai.Sanan itama jini ya balle mata ya
dinga zuba kafin aje Asibiti rai yayi halinsa, ance
iya taji mutuwar nan kaman me.Bayan anyi
bakwai aka raba dan abinda ta bari sanan iya
tace ba zata barni ba dani zata tafi da kyar
mahaifina ya yarda don shima yaji mutuwar yayi
kuka tamkar ranshizai fita , to mafarin zamana a
gun iya kenan.Na taso cikin gata da tarbiya duk
da irin son da iya take yi min, bai sa ta kasa bani
tarbiya ba.Lokacin da aka kawoni gidan yaya Aliyu
yana shekararshi ta karshe a makarantar kwana
ta barewa kwaleji dake zariya.Sam yaya Aliyu
halinsa ba iri daya bane da yayyansa, don su
suna da sakin fuska da fara’a, amma shi kullun
rai a hade ta bakin iya in tana masa tsiya takan
ce na rasa inda ka gado wanan halin naka na
shegen miskilanci, kullun cikin bacin rai sai kace
jakadan yan wuta. Tunda nake gidan bai taba yi
mun wasa ko hira ba, magana in ta hada mu to
bata wuce yazo bai ga iya ba, yace Sadiya ina
iya?Tare da haka ba shi dai raini ko rashin kunya,
sai dai kafi ya ga saurin fushi gami da zafin
zuciya. Yanada matsananciyar tsafta da ibada Iya
na yaba masa a nan, tunda na taso Allah baitaba
nuna mun bacci iya na dare ba, sai dai na rana,
bayan azahar. Duk lokacin da na farka zan ganta
tana yin nafilfilu.
Yaya Aliyu akwai iya saka kaya, bani manta
kawayena in sun biyo mini makaranta suka ganshi
sai kiji suna cewa, sadiya yayan nan naki dan
kwambo ne, ya cika yanga gashi baya
fara’a.Nakan ce kurufa mini asiri kada yaji.Burin
yaya Aliyu aduniya bai wuce ya zama police ba,
kalmar da Iya ta tsana duk lokacinda ya ce mata
shifa in ya gama karatunshi zai shiga makarantar
horar da yansanda.Sai ta ce masa ya daina
wanan tunanin don ita bata son dan sanda, wai a
nata ganin sharri kullun ake koya musu, kullin
suna kan titi suna karbar cin hanci.Wani lokacin
tace, dan sanda da aka ce ko ya mutu gawarsa
tana fita da ban, dan baki take to ban amince
ba.Shi kuma sai yace, iya kiyi min adu’a buri na
kenan zancen zancen ace kaza kaza duk sharri ne
babu ma’aikatan da babu na gari, kuma babu
inda ba battace.Kimin adu’a in zama mai kawo
gyara a cikinsu kuma in na zama dan sanda in
sha Allahu sai kinyi alfahari dani.