DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

   ” Nan suka shiga wata duniyar cike da soyayya da farantawa juna…

   Da safe baffa ya shirya zai tafi kasuwa sai yasmin tace baffa kudin wayar anjima zanje nasiyo…

    ” Auta kenan gwara da kika tunamin sai kisiya biyu ke da maryam ko??

   ” Hajiya suwaiba ce tace wannan marasa mutuncin kaima dai narasa irin ka dakake jin tausayin su Alhalin su basuji naka ba…

    ” baffa ne yace haba babbar yaya ai komai rubewar hannu baka yanke ka yarba…

    ” Sallamar dr sageer ce ta katsesu nan suka gaggaisa sannan ya zauna yasmin dake barandar tsakar gida tana gyara wasu abubuwan ta …

   ” mama ina yasmin ta shiga ne ko tana makaranta?…” aa tana can baranda kaje ku gaisa mana…

    ” Ita dai hajiya suwaiba takasa cewa komai sai adduar Allah yasa ta amince…

     Amincin Allah ya tabbata ga sarauniyar sarakai hasken zuciyata…

    ” Dagowa tayi ta kalleshi nan idonsa yakara rikita ta ta, can tace katashi lafiya…

    ” lafiya kalou ina mamakin kin yarda dakikayi da maganata yasmin kuma ke kanki kinsan bazan yaudareki ba…

    ” Shiru tayi sannan tace idan ma ka yaudare ni ai kaikaga zaka iya domin shi alhaki kwuikuyo ne ai…

   ” yasmin kalli cikin idona magiya nake ki kauna ce ne danAllah!!! Banda ke bazan yabi kowacce ‘ya ba kinsani..  tabbas tun kina karama nasa kaki acikin zuciyata.. kinsan zafin soyayya tunda kinyi kuma kinsan wahalar ta..yasmin dita mai kyan hali ga kuma kyan halitta kwayar idonk’i yana riketar dani har na k’asa dauk’e idanuwa na akanta……

    Shiru tayi sannan tace danAllah doctor ka rufamin Asiri ka hakura da soyayyar mu…please sannan ta goge hawayenta…

     ” Tabbas yasmin idan kika yimin haka baki kyauta ba kuma zaki sakani halin da yafi nada…DanAllah ki taimaka min sannan ya zauna …yau zakiji labari na

   Sunana sageer…

Assalamu alaikum

    Naga Sak’onin ku nagode Allah yasakada alheri…kuyi hakuri da shiru na da kukeji..lurv u oll
  
   I can’t stop apologized for the  spelling and grammar mistake’s

     How was the page???

    _Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM….DS

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com 

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:24 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 30-35

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

  Yanayin da momy ta tarar dashi ko motsi bayayi nan takira mai gadi ya taimaka mata suka nufi asubuti directly emergency sukayi nan akayi dak’in dashi sannan babban amininsa wato dr khalifa yashiga domin ya dubasa…

    Mumy dake faman sintiri da salati abunda yafi tsaya mata ina ramlat tashiga?? Aikin tatafi mijinta na wannan halin?? Cikin kankanin lokaci takira dady nan yakaraso yanata salati da fadin sai ya sabawa ramlat…

     ” mumy ce ta kalli Dady idonta cike da hawaye tace to yanzu yaya zamu sanar da mahaifansa??

     ” Tun ahanya nakirawo baffa dan shine mai sauki kuma sai yafi fahimtar abun cikin sauki….

    Baffa dake faman sauri mama tace ina zakaji ne??

    Au namanta bangaya miki ba sageeru ne babu lafiya rai ahannun Allah suna can asubuti…

     ” Innalilahi kuma yasmin tacemin jikin da dan sauki kaga yanzu yayi tsanani to innakarasa aiki matawo ko??

     ” tohm bari nasanar da alhaji haruna da isa ko??

      ” Toh a sanar dasu kuwa kasan dai halinsu dama dai ka kyalesu ko??

    ” Ai shi zama da mutum sai kayi hakuri ballantana hakkin maqotak’a…

    Yana fitowa daga part dinsa yatarar dasu harda su maryam bilal da mamee zasu fita babu wanda ya k’alli shi sannan ya dubesu yace sageeru babu lafiya ankwantar dashi asubuti…

     ” Alhaji haruna ne yace wannan matsalarka ce, Alhaji isa kuma yace ai da mutuwa yayi kaga sai muci gado ko??

    ” mamee data tamutse fuska tace ku dayake wahaltawa ai sai kuje kuyi jinyarsa sannan suka fita…

    ” Dai dai lokacin da zai shiga mota hajiya suwaiba tashigo nan yace mata tatawo suje asubuti, Akan hanyarsu tatafiya tace kaddai ciwon sageeru ne ya tashi???

    ” Eh hajiya shine abundai sai addua… ” D’ana bai samu macen kwarai ba ina tabbatar ita zata karasa shi…

     ” Baffa ne yace hajiya kamar yaya?? ” Nan ta kwashi labarin duk abunda ramlat take masa ayadda aka bata labari…

      ” kidaina kuka Allah yana sani dashi kuma za’a daidaita su inshaa Allahu…

      ” kallon baffa datayi tace babu yarinyar dakake ganin za’a hadasu??

     ” Shiru yayi yace kina nufin yakara aure wai?? Haba hajiya abu abun asannu tukunna…

     Suna karasawa asubutin sukayi gurinsu nam suka gaisa dasu mumy sannan likita yafito yace ina mahaifansa??

   ” Gamu cewar baffa daga nan suka bisa office shi da hajiya kallonsu yayi yace kunsan yanada ciwon zuciya ko??

     ” Kwarai kuwa cewar hajiya… ” To yanzu dai jikin nasa Alhamdulilahi zai farka nan da 10hours inshaa Allah amma inasu ku lura kukuma kula sosai akwai matsala atare dashi…

      ” Kamar ta tunani saka abu arai da damuwa gakuma yunwa har ulcer takamashi yana da kyau alura da lafiyarsa..

      ” Inshaa Allahu za’ayi…

Brstr ramlat da ita da rabi suke hira nan ramlat tace kawata cikine fa dani???

    ” Wani bakin ciki ne ya tokari mata wuya wato har ramlat tasamu jindadi da mijinta tabbas tasan abunda zatayi…

     ” Dake fa nake magana brstr rabia??

  ” Nan da nan kwallar bakin ciki ta cika idonta nan ta goge hawayen ta tace ina tausaya miki ramlat ace ashekarunki kin haihu? Mijinki zai gujeki daga nan yafarayi miki wulakanci daga karshe kuma sai kishiya…

    ” Ramlat ce tace anya kuwa kinsan yadda dr yakeson haihuwa kuwa?

     ” Tohm shikenan zakiga yanason haihu akan idonki zai wulakanta ki kuma babu yadda zakiyi kuma acikin manyan mata ma kallon raini zasu dinga yimiki kina babbar hajiya araina ki…

   ” wallahi hakane yanzu yaza’ayi to??

    ” ki tashi muje azubar shine kawai mafita…

     ” To wanne asubutin zamuje??

      ” Babban asubuti zamuje akwai kawata acikin asubutin ai… ”  awanne bangare take?? ” tana bangaren emergency…

     ” Okay tashi muje sannan suka huce zuwa asubutin …

   Yasmin dake k’an gado tana tunanin irin kalaman dr sageer tabbas namijin mazaje ne mijin da kowacce mace ke fatan ta samu wani murmushi tayi sannan tace ya Allah karabani da auren da ba soyayya…

     ” yasmin zanje asubuti kafin nadawo ki dora abinci…

   ” Mama wane babu lafiya?? ” Sageeru mana …
  
    ” Shiru tayi sannan tace tohm Allah yabashi lafiya sannan taje tayi alwala nan tayi sallah tare da addua Allah yabashi lafiya..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button