DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

      Rungumeta yayi yace bazaki mutu ba my wife ina tare da ke sai data yi kusan 1hour ta huta sannan ya taimaka mata tayi wanka yabata magani…

      ” kwanciya tayi bacci na kokarin kwashe ta taji yana kokarin zura hannunsa sai ta tureshi ni bacci nakeji..

     ” Murmushi yayi ba abunda zanyi miki kibarni ajikin ki kawai….
 
     ” addua yayi mata har bacci ya kwashe ta shi kuwa dakyar yasamu yadanyi baccin…

Assalamu alaikum

   Kuyi hakuri da rashin rubutuwa akan lokaci..!!!

      Sak’onin ku suna isa garine wannan shafin sadaukar GAREKU MUTANEN GIRKI..ANTY MAI JIDDA (MAMAN TWIN) DA KHADEEJA NA’ABBA , DA READER’S DINA NA WATTPAD DANA FACEBOOK KAI HARMA NA  WHAT’SAPP SOYAYYAR KU GARENI BAZAKA MISALTU BA  AMMA KUSANI TUKWUICIN ALHERI..ALHERI NE, ALLAH YABIYA BUKATU NA ALHERI…Nana Diso lurv you s much

  Let  me all know your view about story and about this page..I will be waiting for your comments and please and please this time I want more comment on this page!  So please kuyi comments..

    Please do vote comments and like ????

   Urs Nana diso

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:18 PM] ‪+234 703 475 7034‬: 78-80

DOCTOR
SAGEER

NA NANA DISO

http://nanadisoo.blogspot.com

© HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Gurin karfe 7 dr sageer ya shirya ya sakko kasa nan ya tarar da ramlat tana ta mutsu mutsu zama yayi akusa da’ita yace sannu mai ciki ko nakuda ce?

” wani kallo ta zabga masa mai cike da riketarwa, bayan kaje kayi zamanka sannan tasha kuka baka damu dani ba…

” haba maman unborn uwargida sarautar mata mata gurin doctor ai kema kinsan ina mutukar sonki…

Yasmin ce ta sakko daga sama hannunta rike da flask tana ina kwana?

” ramlat tayi mata banza, yasmin ta matso kusa da doctor tace saboda ita nagama abincin nan fa kasan mai tsohon ciki baa so abarta da yunwa, harara ramlat kawai take aika mata, ki dauri maman unborn ki tashi muje kiyi breakfast please..

” Dr sageer ne yashiga duniyar tunani tabbas Allah yabashi mace kamila mumina mai sonsa cikin murmushi yace oya muje gaba daya muci..

” Suna cikin karyawa yace jiya yan fashi sunji gida amma babu abunda sukayi sai su alhaji haruna da suka daka..

” Yasmin da hankalin ta gaba daya ya tashi cikin kinkina tace Baffa na fa tasa kuka…

” Babu abunda sukayi masu fa yanzu ma can zanje..

” DanAllah zan bika, aa yasmin kiyi zamanki..

” kuka ni gaba daya ya kauce mata cikin gigicewa ta hau sama garin tsoro sai kuwa ta gangaro da gudu dr yaje kafin yakaraso ta wado kuka takara sakawa ai kuwa jini duk jikinta ihu tasaka…

” Ramlat kuwa dariya tasaka har sai da dr yadaka mata tsawa..

” cikin yanayi yakalli yasmin yace yanxu kin kyauta kinyi min asara komai ke kuka..

” itama kuka takara sakawa bai ajiyeta ko ina ba sai toilet after sunfito yasa mata ledar ruwa yayi mata allura sannan ya zauna kusa da’ita sai da tayi bacci sannan yasakko ya fita…

” ramlat ce tace ai daman an asirci ka anyi maka asirin gado ka gyarata to sai kagyara kafar binin ma…

” tsaki yayi sannan yayi ficewar sa ramlat tace kai naji dadi cikin nan ya bare shigu har sunyi ciki kai wannan yarinya da jaraba take….

Lokacin da dr sageer yashiga gidan bai tarar da kowa ba sai da yashiga part din su haruna nan yatarar suna kwance a shime inna sai dariya takeyi…

Bayan sun gaisa sai cewa tayi sageeru kaga karshen mugaye ko to DanAllah dan annabi kada kabada kwandalar ka a kaisu asubuti…

Dr sageer ne yace duk wanda zai ce zai kwace arzukin da Allah yayiwa wani to yana cikin nada ba karama ba kuma shi zaita wahala,tun muna yara kuke cutar baffa kun cinye masa gado kun wulakanta sa Amma daidai da sakan bai taba ramawa ba ku duba kuga bakuda koma yanzu shi kuma sai gaba yakeyi to idan kun hankalta to idan kuma ba kuyi ba DUNIYA CE…

kuka suka saka sannan yabar bangaren su nan yatarar sun shirya bayan ya gaishe su yace baffa ina zakaje haka??

” zamu koma sabon gida ne akusa dakai..

” Kaddai gidan kusa damu wanda aka gama gini??

” Eh… ” Amma baffa bakagaya min ba?

” Sageeru kenan shi sirri wani abuni da idan ka iya shi to zaka zauna lafiya kuma zakayi abunda zakayi cikin kwanciya hankali amma mutanen yanzu ai da baki suke lallata mata lamurukan ka…

Hakane baffa ashe kuma abunda yafaru kenan Allah ya kiyaye gaba..

Ameen bari naje inyi musu yajiki sai ki fito muyi musu sallama..

” Mama ce tace tohm sageeru ina matar taka ince dai ba matsala ko??

” wallahi inason yasmin mama amma yawan kukanta daga nace bazan barta tafita ba sai ta dinga kokarin fushi dani kokuma tadinga kokarin kuka mai tsanani, amma duk wani jindadi ina samu daga matata, yanzu haka ma tayi bari garin sauri ban barta tazo taganki ba..

” subhnallahi hukunta ta zakayi kuma zanyi mata magana ai kai yayanta ne zan kiraka anjima sai kabata…

” karkuma tace na hadata dake..

” Dariya mama tasaka tace au tsoronta kakeji.?

” dariya yasaka yace ai ita ce farin cikina banson bacin ranta…

” sai da mama ta shirya itama ta shiga rayi musu yajiki sannan tace mu Allah ya yimana tashi ga bangaren mu nan sai ku hada duka…

” mamee da gabanta yawadi tace kamar yaya??

” Allah ya hore mana munyi sabon gida…

” Mamee ce tace munshiga uku wato dai Allah ya daukaka ku..

” mama batace komai ba ta fito suka tafi…

” mamee tace Allah ya isa tsakani na dakai Alhaji haruna kai kajawo min kaine mugun miji kuma ka dorani akan mugunta wallhi van yafi maka ba…

” Inna ta kalli isa tace to babban azzalumi nima anjima gaba zanyi garin mu ke kuma mamee bakiga komai ba, khalil kuma dashi zan tafi nagyara yarona ka cuceni ka lallata masa rayuwa Allah yaisa tsakanina da kai…

Lokaci daya nakuda tazowa ramlat sai kara takeyi tana ihu yasmin ce ta cere abun hannunta ta liko nan ta ganta sai ihu takeyi ba’a dadi ba ta shirya taja mukullin motar ta dakyar tasamu suka isa mota tsaka ramlat sannan taja mota cikin kankanin lokaci suka isa asubuti nan Likitoci sukayi ciki da ita nan yasmin taketa kokarin samun dr sageer awaya amma shiru bata shiga…

Linda ce ta shigo tace yasmin ko??

Eh nice ya akayi..

Yanzu akayi mana waya dr sageer ba lafiya anyi gida dashi batasan lokacin da ta shiga mota ba taja sai da ta’isa gida taganshi kwance babu alamar buguwa Amma baya hankalinsa dan ko ganeta baiyi ba kuka tasaka tanata addua tana kallonsa mijina wayyo kamar daga sama taga mama da baffa akanta..

” na shiga uku wannan ba asiri bani ba kuwa?

” baffa ne yace asirin lafiya?

” Antaba yiwa mahaifin mu…

” yasmin dake faman kuka tace baffa akaishi asubuti aa yasmin wannan abun bazamu fitar dashi ba sai mungwada na musulunci mungani…

Ina ramlat?? ” tana asubuti tatafi haihuwa..

” Nan mama takira mum tagayamusu ramlat na asubuti ta kuma gayamusu suyi gida daita idan ta haihu…..

” Baffa yagayawa hajiya Da ita da Aisha ba shire suka shirya ..

” Mama ce tace wai ke bakida hankali yasmin wannan uban kukan maganin me zaiyi miki??

” Toshi bakinta tayi tahau sama babu shiri tayi alwala sallah take tanayi wa Allah kirari yabawa abokin rayuwarta lafiya…

Kamar daga sama taji ance ke ke ke…

” Atsoraci tace Allah yafiku azzalumai…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button