DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

    Su ramlat suna sauka tace rabia mijina fa babu lafiya muyi sauri ji nakeyi kamar wani abu zaifaru…

    Ke kinfiya matsala wallahi aikin banza zo muje suna shiga sai kuwa sukayi karo da dady nan yakifa mata mari sau biyu da sauri baffa yace haba alhaji menene haka???

    Dan ubanki mijinki bai baki daman fitaba kike fita ?? Sai yanzu kikaga damar zuwa??

  Gabanta ne yayi mummunan faduwa sannan tace wallahi …

    ” mumy ce tace kada kice komai munafuka…

    Rabia ce ta salallaba tayi sauri tafita bata tsaya ko’ina ba si motarta cike da dariya hahaha har iyayenki sai nasaka sun tsinemiki hahaha taja motarta tatafi….

Ramlat ce ke kuka tana fadin nashiga uku ina mijina yake??

     Mumy ce ta dakatar da ita mijinki din uban wa mara tarbiya??

     ” hajiya ce tace haba mumy ai bahaka ake ba har yanzu fa yarinya ce ramlat kiyi mata ahankali kikasani ko wane case din takeyi mai mahimmanci…

    ” mumy ce tace wane irin case ne daya huce cutar mijinta eh??

    Haka sukayi jugum jugum mumy tace ramlat bazata zauna dashi ba mama ce zata zauna ….

    ” Har karfe tara shiru har ya huce 20hours har yanzu bai farka ba…

     ” hajiyar sageeru ce tayi cikin dakin nasa ta zauna akusa dashi inbanda kuka da addua babu abunda takeyi…

   Yasmin dake zaune a palour tarasa menene yake mata dadi, tun dazu sai tunanin dr sageer takeyi cikin yanayin kunci tace why my heart nan hankalinta yakara tashi taga har goma basu dawo ba abinci ta zuba sannan ta nufi hanyar fita tare da rufe kofar su tana kokarin fita bilal yace uwar gantali inakuma za’aje??

     ” Gidan uban da ka aikine sannan ta bude kofa tafita nan tasamu mota tahuce asubutin…

     Lokacin data isa gaba dayansu sunyi jugum jugum tana karasawa dakin taga hajiya tanata kuka… cikin tashin hankali tace hajiya lafiya shiru tayi mata sai alamar kuka…

     ” a tunanin ta mutuwa yayi cikin tashin hankali ta matsa kusa da gadonsa tana kuka hannunsa ta ruki tace ya sageer please karka mutu danAllah karka barmu tana wani kuka mai cike da tashin hankali…

  ” A hankali ya bude idonsa kalmar da tazo bakinsa shine yasmin…yasmin..yasmin….zaki aure ne???

   ” batasan lokacin data miki sannan tayi waje ba tana kuka nan dukk’an su suka tashi sukayi hanyar ciki ba kowa yana kallonsa yana Alhamdulilhi ramlat ce ta matsa gurinsa tana kuka…

” likitane yashigo sannan yakara yimasa allura..

   ” Alokacin hajiya suwaiba ta miki tabi yasmin…

Assalamu alaikum!!!

       Please and please kuyimin afuwa da yawan shuruna da kukeji,Allah yasaka muku da Alheri ina ganin sakon ninku….Nana diso love u so much….

  
   I can’t stop apologized for the  spelling and grammar mistake’s

     How was the page???

    _Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM….DS

Wato haqiqar haquri shi ne bãwa ya gudãnar da rãyuwarsa a lõkacin musiba/balã’i kamar yadda yake gudãnar da rãyuwar lõkacin zaman lãfiya !

Dõmin Allah SWT bã ya qar’bar wani abun daga wajen bãwa; fãce sai dan ya bãwan yayi haquri, haqurin kuma ya sanya Allah SWT ya so bãwan kamar yadda Allah SWT ya fad’a cewa:
(( Kuma Allah Yana son mãsu haquri )).

Bisa ga haka idan Allah SWT Yana son bãwa sai ya zã’bar masa abin da yafi alheri gare shi da ma duk abin da zai zama maslaha a gare shi, don haka sai bãwa ya yarda da hakan.

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:24 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 45-50

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Dago k’anta tayi sannan ta k’alli yadda ya rike hannun ta, cikin kuzari ta zare hannun ta sannan tace lok’aci fa yana kurewa?

     ” batare da yace mata komai ba ya cigaba da driving sai da yaje daidai kofar jami’ar sannan yatsaya…

     ” jiyowa tayi tace nagode… ” har tayi gaba sannan yace yasmin?

    ” Cikin nutsuwa ta karaso har inda yake sannan tace Naam!

     ” cikin daure fuska kada taki gayamasa yace karfe nawa zaki tashi???

     ” sai lokacin da malamar tazo nayi mata submitting ai…

     ” Okay to kikula da kanki bye bye…” wata harara tayi sannan tace tuntuni bai taba cewa in kula da kaina ba sai yanzu…

  Wallahi mamee dr son yasmin yakeyi Allah bazan yarda ba sau dai ni ya aure ne…

  ” ke ki kwantar da hankalin ki indai nice bai isa ya aure yasmin ba tabbijan ki kwantar da hankalin ki nasan me zanyi…

     ” Maryam ce tace yauwa mamee ta ai yasmin da mai gadi ta dace wallahi…

     ” Alhaji haruna ne yace ai sageeru sai nasa yan fashi sun nakasa shi ina tambayar sa bashin kudi sai cewa yayi kowa zai bashi kudi amma banda ne ai wannan raini ne zaici ubansa….

    ” lallai wuyansa yayi kauri Daman ai shi dan Adam butulu ne…

   Barister ramlat dake zaune a office dinta duk cikin yanayin damuwa, irin rashin kulawa da dr yake mata har yafara taba mata zuciya tana cikin tunani sai ga rabia ta shigo….

    ” ke dai sai kinsawa kanki hawan jini baki da tunani sai na namiji to sai kiyi tayi su hada miki hawan jini ai ki rabu dashi nahada ki da sugar dady wanda sukafi miji ki komai….

     ” me kike Nufi rabia?

Dallah ina nufin maza mana ki rabu da dr nahada ki da wasu ku shakata akwai wani sabon Alhaji da aka hadani dashi sai na barmiki shi…

    ” Allah yakiyaye wallahi ai ni bana zina ingayamiki ko shekara nawa dr zaiyi baya kulani bazan bi maza ba…

   ” kinga kar kigayamin babu dadi kikasan irin shi matan dayake kula? Ya dirka miki cikk yabarki da sha’awar sa kuma yayi ficewar sa dan love dinnan bai nunamiki shine zaki dinga fiffiga akansa??

     ” aa rabia komai fa lefe nane abubuwa nawa nakeyi baya kulanani yayi hakuri dani sai yanzu zanje haushi, ciki kuma kinsan babu maganin da ban shaba yake barewa ke duk ba wannan ke damuna ba aure da zai kara…

   ” ke kikasani malama ainaga nakya daukar shawarata sai kiyi abund kikaga shine daidai…

    Mtsww ke fa rabia matsalata dake fushi dallah kigayamin zan dauka…

    ” kinsan namiji ba’ayi masa sanyi in kin koma ki yimasa rashin mutunci kikuma yimasa kashidi ke in san samune ki gudu gida zakiga ya janyi ko kefa yanzu kikayi magana me kyau ni bari natafi sai gobe…

   Okay bye bye…tana fita rabia tasa dariya tare da fadin ai sai na kashe miki aure bake kawa ba…

Karfe 5 yasmin ta dawo daga skull abinci tace sannan tazauna bakomai take ba sai tunanin dr sageer tabas tabbas tana tsoron shiga tarkon soyayya Amma kuma gwara tayi aurenta itama ta huta cikin wannan tunanin hajiya tashigo tace yasmin?..

   ” Naam hajiya  …. ” wai meke tsakanin ki da dr ne? Naga duk ya mutu akanki ko soyayya kukeyi…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button