DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

” Batare da musu ba ta rakashi sai da taga khalil yana kallonta sannan tace sai anjima yayana take care of your self please…

” ki kunna wayarki da daddare…

Khalil ne yace an asirce shi kenan asashi yaso ‘yar iska irinki…

” kai iya bakin ka babban mara mutunci kuuu da kuke kiran wasu ‘yan iska uban wa yakaiku iskanci…

” Ni kike gayawa haka hahaha ki zuba ido kiga wallahi sai na bata miki rayuwa…

” jahili kawai jahilci ke damunka banza kakoma skul please….

” Alhaji haruna ne yace ubanki ne zai koma ba khalil ba…

” Dariya tasaka tace Alhaji ai sai ku koma tare tayi shigewarta cikin gidana tana dariya…Nayi alwashin duk wanda yayimin sai nai masa tunda basuda kirki….

Assalamu alaikum

BARAKALLAHU FIYKUM BAZAN KUMA DAINA GODIYA AGAREKU BA BISA SAKONNIN KU ALLAH YABIYA BUKATU NA ALHERI.._

How was the page???

I can’t stop apologized for the spelling and grammar mistake’s

Please do vote comments and like.. And I call my silent readers please do vote and comment my story really need your comment and vote#TEAM …..DS….DS LOVER’S_

Kuma ya zo a hadisin da aka kar’bo daga Abi Sa’eed da Abi Huraira (RA) cewa Manzon Allah (SAW) yace:

Bãbu wata musiba/jarraba da zãta sãmi musulmi na daga gajiya/wahala da rashin lãfiya ko dãmuwa ko baqin ciki, ko cuta ko bacin rai…

…Har – qayar da zai tãka- fãce sai Allah ya rufe/kankare masa da ita – musibar/jarrabawar – wasu daga cikin kusa-kuransa )Bukhari & Muslim.

Wato yin haquri abu ne mai girma, don haka Malamai suka ce haquri ya kasu kaso uku:

1- Hakuri wajen biyayya ga Allah, ko da rai ba ta son hakan.

2- Hakuri wajen gujewa sã’bon Allah, ko da rai na matuqar buqãtar hakan.

3- Hakuri kan duk wasu abubuwa da ke kai-kawo, domin Allah ya rigã da ya tsãra yadda rayuwa zã ta kasance tun kafin halittar Annabi Ãdam da shekaru d’ari biyar (500)

Sa’an nan yana daga cikin addu’ar Manzon Allah SAW ya yin da farin ciki ya sãmu:( Dukkan gõdiya ta qara tabbata ga wannan da ni’imarsa ce ta ke cika dukkan kyãwawan abubuwa ).

A halin baqin ciki kuma: (( Dukkan gõdiya ta qara tabbata ga Allah a bisa ko wane hãli )

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 8:25 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 55-60

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Lokacin da dr sageer ya koma gida brstr ramlat yatarar sai kuka takeyi cike da rashin mamaki yazo ya huce ta gabanta..

   ” brstr dataga bai kulata ba sai cewa tayi ai daman namiji hankaka ne gabansa fari bayansa baki, har ka kai kudin aure amma baka sanar dani ba me nayi maka da zaka yimin kishiya menene bana yi maka??

    ” Baki da hankali ramlat kije kiyo karatun tanuzu tukunna, kuma bari in gayamiki babu ke babu yasmin wallahi naji ance kinyi mata abu sai na sassaba miki nagaya miki…

    ” Wallahi sai nayi mata ta aure mijina tagani tsabagen rashin mutunci naka wacce irin bukatar kace bana biya maka?

    ” Tsaki dr sageer yayu yace ina abinci na??

    ” ban dafaba? ” baki dafa ba? Allah yaso naci awaje da haka zaki barni da yunwa ke bari kiji duk duniya babu abunda namiji yake bukata sama da kulawar mace amma ke ko ohoo babu abunda ya dameki sannan yashiga daki…..

     ” kuka tasaka sannan takira rabia awaya sannan tace wallahi rabia auren yaki yafasa narasa yadda zanyi zuciyata sai bugawa takeyi please i need some advice please…

    ” dariyar mugunta rabia tayi sannan tace kije kikara yimasa masifa zama zakiyi kina kallonsa idan kika bude masa huta zakiga yafasa….  ” cikin kuka tace toh sannan ta kashe wayar dak’in tabisa cikin masifa tace wallahi tallahi kai dai ba d’an halak baniba kuma baka haifu ba, ko haihu banyi ba zaka karamin kishiya sannan tasa kuka…

    ” k’allon ta kawai yakeyi sannan yace tabbas inason ki rike hannun ta yayi kafin yayi magana ta fizge sannan tace wallahi zakaga tashin hankali indai kayi auren nan don wallahi sai na takura mata…

    ” Murmushi yayi yace ai ba jahila zan auro ba nutsetsiyar yarinya wacce tai ilimi kuma tana aiki dashi wacce zata kula dani da ita…

    ” Kuka tasaka wanda har sai da ya tausaya mata amma ina brstr ramlat jitakeyi kamar zuciyarta zata buga saboda kishi…

Yasmin tana kwance bacci yana kokarin kwashe ta sai kuwa jitayi an kirata dauka tayi tare da sallama…

    ” wallahi bakida kirki yasmin wato ankawo kudin auren ki ko kisanar dani to nagode sosai…

    ” DanAllah kiyi hakuri yusra wallahi nakira wayar mamanku bansamu ba kuma inata kokarin kiran daya layin naki amma wayar ki akashe kiyimin afuwa please aminiyata…

    ” dariya tasa tace Matar doctor bada kanki asare amarya gidan sageeru Allah yasa kina shiga ki haifi twins…

    ” Dariya tasaka sannan suka cigaba da hira bayan wasu mintuna sukayi salama…

     Yasmin yasmin kiranki kifa naketayi…

    ” mama ina waya banji ba wallahi bari nafito tana sanyi da kayan bacci sannan tafito takarbi wayar…

    ” ke yasmin ki biyo hajiya kutawo kizo muyi miki irin gyaran jikin mu kuma akwai abubuwan da zamu tattauna dake…

    ” Au yaya aisha ygida? Gaskiya ni garin nan naku bana sonsa ayimin anan…

     ” Nifa dadi na dake shirme please kibiyota kinji ‘yar kanwata wallahi ina missing dinki gasu umar nan sai kuka suke kinki zuwa…

     ” Karki damu ‘yar uwa zan biyota inshaa Allahu…

    Tana kashe wayar sannan ta nufi dakin da hajiya take bayan tayi mata sannu sannan tace hajiya gobe zaki tafi ko?

    ” eh wallahi bansan halin da yayanki suke ciki ba gashi anyi rasuwa sai gab da bikin ku zandawo…

    ” DanAllah hajiya zanbiki zanje gidan yaya Aisha kinji…

     ” Hajiya ce tayi murmushi tace ko kefa?? Sai ki shirya jirgin 12 zamu bi nagaya babanki anjima…

   ” yauwa hajiya tamu nagode sosai…

     Mamee ke faman sintiri a palour can tace wai Alhaji babu wani boka akasa ne?? Da za’asa ya hana auren nan…

    ” Alhaji haruna ne yace ina wani boka ina kudin ai boka sai da kudi ki duba yadda kullum yarinyar nan take cigaba gashi sageeru sai kantuna yake budewa…

    ” Na shiga uku na lallace to yanzu ga dankune na kasiyar DanAllah ahana auren nan…

     ” To yace sannan ya karba yana fita waje alhaji mukhtar yace ku dai anyi asararru kabiya ni kudina dubu sittin dita wallahi sai kabiya ni…

     ” Wallahi banda ko sisi…

     ” Dallah yimun shiru ku ba abun atausaya bani malam bani kudina kokuma yanzu nasa atara maka gajiya…

     ” Ga dank’une dubu hamsin ne kudinsa zan ciko maka dubu ashirin…

    ” kai baka isaba malam bani cikon kudin bai ankaraba yaji ankifa masa mari gaba daya mutane sun tsaya kallonsa baffa ne ya karaso gurin da mota yana zuwa yace haba bawan Allah me yayi zafi haka …..

    ”  Alhaji mukhtar ne yace kudina yakarbar min sama da shekara daya amma yaki biya na wannan mutumin ba abin tausayi bani wallahi…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button