DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

    Dariya tasa ta rungumeta akayi yimusu hoto daga nan ango da abokanan sa sukazo kallonta kawai dr yakeyi ji yakeyi kamar ya rungumeta sai da suka gama hotonan su  sannan sukaje cikin gidan su mamee dakyar akayi hotunan saboda habaici idon yasmin gaba daya yakawo hawaye bayan sunfito yatsaya asoro tazo shiga gidan yace yasmin anjima da da daddare zaayi dinner tsaki taja sannan tasa kuka bazanje ba bazanje ba bai san lokacin da yafara kissing dinta ba gashi ta kasa tureshi sai bayan mintuna ya saketa idonta sai hawaye yake fitar sau nawa ina baka hakuri baka damu dani ba…

    ” kissing din bakin ta yakarayi kin tabbatar ina sonki ina kaunarki matata na yarda dake ko’ina nashige ke zan nuna, ke tawace, na soki zuciya ta daya, rungumeta yayi sann kara da cewa bana nadama nasan sona ne yakamaki…

    ” Hawayen ta ta cigaba da zubar sannan tace wazai tabamin kai na barshi akanka zanyi komai, rayuwa da kai zanyi ta so zama farinciki dan yakore damuwa ta, ina kaunarka mijina, Ni dai taka ce danAllah kada ki yadani, kai kadai nabawa yarda cikin zuciya…

    ” To ki daina kuka kinji? Zanyi alfahari dake in kika zamo acikin gidana..anjima ki shirya za’ayi dinner..

    ” To ta tacemasa tare dayimasa wani rikitaccen kallo sannan ta shiga cikin gidan…

    ” yana isa mota khalifa yace yau dai burin ka yacika yakamata kaje gurin ramlat bakaji muryarta ba …

   ” Dole natafi gurinta na lallashi matata…

ASSALAMU ALAIKUM

~INa gaisuwa da jinjina gareku d’inbin masoyana, adduo’in dakuke min nagode sosai….Nayi tafiya Nakuma dawo lafiya!

    Tell me your opinion about this page!

~…Again apologized for the spelling and grammar mistake….bansamun cikkakin lokaci na kara bin labarin…ballantana nagyara…

  Rayuwa tafi take da matsala da jarabawa kalakala…hakurin ka shine kawai nasararka… Ba za ka sauka tashar nasara ba sai ka hau motar hakuri da kokari da sadaukarwa….. Yana da kayu ka yafe idan aka yi ma laifi. Abin da ya fi haka kyau shi ne ka manta da laifin da aka yi ma ka……Rayuwa komai me wucewa ce…

  Please do vote comments and like..your comment give me more courage to continue writing my story…and it helps me to write better…#TEAM…DS….DSLOVER’S

Alqur’ãni mai girma shi ne tushe na farko cikin abubuwanda suka shãfi shari’ar Musulunci, kuma zuwa gare shi musulmai ke kõmawa yãyin da wani abun ya rikitar da su cikin lamarin duniya da lãhira.

Mumini na qwarai yana  yin duba zuwa ga Alqur’ãni a matsayin abin d’auke kewa ta yarda yake karantã shi kullum, sã’ilin nan yake tin-tin-tini cikin izinar da ke cikinsa da misãlai da ya qunsa, kuma ya nemi fahimtar Alqur’ãnin da hukunce-hukunce da ya qunsa.

Sai kula da aikata duk abin da Alqur’ani yayi umurni da shi, da nesantar abin da ya hana, don shi ne kad’ai litattafin da ya dãce ga rayuwar d’an Ãdam kuma yana nan a kiyãye kamar yadda Allah SWT ya fad’a cewa:

(( Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alqur’ãni), kuma lalle Mu, haqiqa, Mãsu kiyãyewa ne gare shi )).

Bisa ga haka mumini na qwarai shi ne wanda ba ya nesantar karatun Alqur’ãni a kõda yaushe, sannan kuma yake qõqarin bibiyar ma’anar abin da yake karantãwa da neman sanin wasu darussa wad’anda suka shãfi Alqur’ãni.

Shi Alqur’ãni igiyar Allah SWT ne wanda yake miqaqqe, duk wanda ke son Allah SWT da gaske, to, zai so littafin Allah ya kuma girmamã shi da ma’abõtansa.

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com  

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:25 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 60-65

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Anty najiba ce kanwar mumy tace haba barister menene abun damu ak’an kishiya common sai kace jahila kinfi yarinyar nan komai da komai fa akasari ba ke ba’ajin ta bace ba ki manta da’ita tashi muje kiyi wanka ki shirya kema kinji my barister…

    ” Har cikin ranta ramlat ta d’anji dadin kalaman ta goge hawayen fuskar ta tayi sannan ta shiga wanka…

     Dr sageer ne yakaraso cikin gidan su ramlat mumy yafara tarar wa sannan suka gaisa cikin farin ciki tace Allah yasanya Alheri doctor ya hada maka kansu…

    ” Har cikin ransa yarasa irin mumy tabbas wata suruka ce da babu ruwanta gata dai ‘yar boko Amma tafi masu ilimin dayawa aiki dashi cikin murmushi yace Ameen mumy….

     ” Ramlat din tana cikin daki kaga ko abinci tun safe ta kasaci narasa irinta wallahi sai kana hakuri da’ita dr kana kuma yimata wa’azi…

     ” Murmushi yayi yace inshaa Allahu mumy sannan yashiga dak’in da take nan yaganta zaune ko kaya bata saka ba tayi tagumi rufe kofar yayi yazauna kusa da’ita cikin bacin rai yajanye hannun sannan yace haba matata haba sirrin zuciyata, ke tawa ce iyalina sannan ya rungumeta wane kuka tasaka mai cike da tausayi dagota yayi ya goge hawayen sannan ya kalleta haba ramlat so kikeyi ki illata kanki da baby din cikin ki???

     ” Shiru tayi batai magana ba sai da yagama goge hawayen fuskar ta sannan tace ai duk kai kajawomin da kakoyamin soyayyar ka kasaka min dafi acikin raina, yanzu itama haka zaka tararrayi ta kenan??

    ” Haba my wife haba ramlat ba dan bana sonki yasa nayi miki kishiya ba badan in muzanta miki ba wallahi ina mutukar son mata biyu wannan kaddarace daga Allah kici abincin sai kisha maganin ki kinji?

    ” Wane murmushi tayi da yakaraso da hawayen fuskarta tace ni sai dai k’abani bazan iya ci ba…

      ” Uwargida rangida duk yadda kikace haka za’ayi ai karbi to kici…

     ” Kallon sa kawai takeyi tabbas sageer dole mace ta sosa cikin maza dare kadan ne irinsu yadda yake tararrayar matarsa sai da tagama ci sannan yabata ruwa..

     ” kwanciya tayi kan kafadarsa sannan tace yau zakuyi dinner ko?

     ” Eh yau za’ayi ga kayanki can apalour zakije ko??

      ” cikin murmushi mai cike da boye damuwa tace kanaso naje?

        ” Ai abunda kikeso shi nakeso in hakan zai haifar miki da damuwa ai bai kamata kije ba…

     ” kumatun sa tashafa tace farin cikin ka shine nawa inasonka da yawa mijina…

     ” Bakinta ya sumbata yace nima haka matata uwar ‘yayana ina bala’in sonki…

      ” yana shafata yana danyi mata hira har bacci ya kwashe shi sallar azahar yayi sannan yanufi asubuti dan yanada aiki…

     Anty najiba ce tashigo taga yadda ya kwantar da’ita ga kuma kayanta da rafar ‘yan dari bibbiyu akusa da’ita murmushi tayi tace dama mijin mu muma zai dinga yimana adalci kamar yadda dr yake yiwa su ramlat tana cikin tunanin nan taji wayar ta text ya shigo tana budewa taga rabia tana cewa wai ke meke damunki da baki kashe auren ba tabbijan kina gani yana rawar jiki akan yarinyar kina zaune su hada miki hawan jini bikin ma kiyi zaman ku agidan ku karki je… najiba bata tsaya ko’ina ba sai dak’in mumy nan tabata takaranta mumy ce tafara blocking dinta kafin nan tace…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button