DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

GOD BLESS YOU OLL….

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com
[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 10-15

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Kuk’an da barister ramlat ke famanyi yasa gidan gaba daya ya dauka, adaidai lokacin da momy take kokarin shigowa gidan sautin kukan ‘yarta tace yakara firgeta ta cikin sauri da hanzari taisa cikin gidan nan ta tarar da ramlat a shaime tana wasu irin maganganu, dotar??? What wrong with you? Ya’ilahi…..

    ” Rungume mumy tayi sannan tace baya sona mumy yace mun rabu wallhi zaki’iya rasani akan dr sageer,mumy please kibashi hakuri kuskure nane…

  ” Ya’ilahi me kikayi masa? Always ina gayamiki kina iya magaba kina barister amma u need to change your words namiji bazai dauka ba….

  ” Wallahi Rabia ce tace yaudarata yakeyi if yazo naci masa mutunci zai daina kuma zai tsorata….

    ” are u mad ramlat? Sau nawa ina cewa kirabu da rabia ba mutuniyar kirki bace ba, kuma ke ina ilimin ki? Mtseww ke kika jawowa kanki dan haka sai kiyitayi….

   ” mumy please karkice haka haba mum please ki bashi hakuri please mum!!

   ” Har cikin zuciyarta ta tausaya mata especially tafita hayyacin ta hakan yasa tace ke zaki shawo hankalinsa not me tashiga daki…

   ” cikin wani yanayi da fargaba ta dauki wayarta tafara kiransa ta kirasa yafi sau 10 amma bai dauka ba…..

   Yasmin ke faman karatun Al kurani malamin math ya shigo nan yayi musu sannan yabafa class work duk wanda bai iyaba bulala biyar ce, yusra kawar yasmin kwata kwata bata iya ba gashi tarasa yadda zatayi yasmin data lura da hakan sai ta bawa yusra littafinta ta karbe nata tana gama solving a tsoroce ta mika mata nata…

  ” Duk class din da yafara marking mutum uku ne kawai sukaci nan ya dinga duk’an kamar an aiko shi…

   Yusra ce tace godiya nakeyi kawata kin taimaki ne sosai…

   ” yasmin ce tace bakomai kawata malamin math din nan mugune wallahi taso muje na koyamiki yadda ake solving din..

    ” Nan suka tafi suna ‘yar hirar su can irs teacher yace yasmin?

   ” jiyowa sukayi suka gaishe shi cikin murmushi yace kina dai lafiya ko?

   ” cikin rashin fahimta tace eh sai anjima sukayi gaba, yadade yana kallonsu har Allah yasa suka huce wasu senior dinsu wata daga cikin su tace kee yarinyar nan zo?
 
   Tohm gani inji yasmin..

       ” ga kayana kije ki wanke min kinji…

    ” Tohm shikenan, zata karba tace au ashe kinada hankali barshi nafison yarinyar da zatace bazatayi ba…..

  ” Tohm nagode suka karasa hucewa,yusra ce tayi tsaki gaskiya kinada over hakuri yasmin ke komai babu ruwanki ???

Maryam ce ke cikin motar saurayin ta sai rangwada takeyi tana wani narkar da murya abun sai wanda yagani, Adaidai lokacin ne dr sageer ya danno kan motar shirun da yaji anki amatsa daga gurin gate yasa shi sakko wa daga motar cikin bacin rai,maganar da zaiyi yaga maryam zaune saurayin ta yana kokarin taba hannun ta sai dr sageer yayi maza ya bude motar cikin zafin rai ya k’ifa mata mari menene haka dan ubanki…

   ” Cikin bacin rai tace haba yaya wannan wani irin abu ne??

    ” uban wanene wannan ‘yar iska wannan samarin banzan kike bi??? Dan ubanki shige gida sannan ya juya k’an saurayin ta cikin zafin rai yace idan nakara ganin ka kofar gidannan sai na ballaka wallahi dan iskan banza da wofi….

   ” simsim ya shige motarsa ya gudu…

    ” Wallahi mamee watarana sai na karya maryam kina ganin iskancin da tayi amma bazaki hanata ba???

   Mamee ce tajiyo tace banson takura banson shishigi kai uban matan dakake hulda dasu waya sani??? To kafita harkar yarana ko sokakeyi su zama kamar yusra babu mai shinshinasu??

    ” Abida ce tace mtseeww mamee kyale wannan yayan bashida waweyyen kai ahaka dan boko sai kauyen ce???

    ” Tashi yayi zai daketa ta ruga daki, lallai mamee nagode da kalaman ki kuma kisani uwa na daukeki duk rintse idan naga k’annina sun shiga sun kauce hanya zan musu nasiya in gaya masu gaskiya sannan yafita daga dak’in….

    ” tsaki tayi tace too muzuba nidakai muga wanda bai fasaba mara kunya ke kuma ki shige dak’i saura naji kinkara futa…

    ” Tana shiga ta k’ifa k’anta ak’an gado tafara kuka…

   ” Abida ce tace lafiya maryam ko dai ya dak’i kine??

    ” wallahi sister ina bala’in son ya sageer wallhi inasonsa narasa yaushe soyayyarsa ta shige ni sannan ta goge hawayenta tace please karki sanar da mamee…

   ” yusra kenan ke dai mutafi…

Tabbijan lallai kina cikin wahala hahaha wannan k’olon gardin kikeso ga alhajin birni nan!

    ” banson iskanci abida banson haka ki iya bakin ki nagaya miki…

   ” Allah ya baki hakuri son koko daukar rai…

  Bilal ne ya K’alli  mahaifinsa Alhaji isa yace dad wancan baffa ya biyaka kudin ka kuwa??
 
  Ina ai zuciyarsa ta mutu dubu 20 ake basa kudin gadi ina yaga kudin biyan dubu hamsin??

   ” Yasamu kudi ai tunda yakai ‘yarsa boarding yakamata gobe ka kunna mada wuta yabiyaka…

    ” Angama my son kai dai kanason kaga sun wulakanta kamar yadda mukeso kenan??

    ” Kwarai kuwa ko kadan banaso sufimu…

Baffa ke lazumi ak’an dadduma,mama ce tafito tace sannu da hutu maigida…

    ” k’allonta yayi yace yauwa uwargida lafiya dai??

    ” wallahi kaga nakasa baccin tunanin kada ‘yan uwanka su cimaka mutunci akan kudin nan nasu dubu hamsin…

    ” To yazanyi? Wallahi banida hanyar samu albashina ma dubu ashirin ne kuma kinsan duk naci bashi banga ta ‘inda zanbiya ba…

    ” Ya kamata ka kokarta dan Allah wallahi banason naga suna hayagaga…

    ” kinfi kowa sanin ni bana maula ballantana nace abani kuma bana rok’o ballanta nakarba,kuma kinsan sun batamin suna babu mai bani bashi,Amma ki kwantar da hankalinki Allah zai bayar da yadda za’ayi…

   ” To Allah yasa,bari nagyarawa yasmin dak’inta naga gobe zata dawo…

    ” yauwa goben in Allah ya kaimu kiyimata tuwo danAllah tunda tanason tuwo kuma gobe Aisha ma zatazo sai ayi mata d’an wani abun…

    ” cikin jindadi tace Allah yakawo mana su lafiya…

Dr sageer ke k’allon ‘mbc 2 yana kallon wani vampire hankalin sa rabi akan tunanin ramlat yake tabbas yana son ramlat amma abun yafara bashi tsoro har tafara zargin sa, shiru yayi yana wani tunani har wayar sa tafar ringing cikin murmushi ya dauki wayar ayayin da yaga mahaifiyar sa ce…

” Assalamu alaikum Sageeru???

    ” Cikin girmamawa yace Allah yakara lafiya hajiyata yakuke ya benin??

    ” yanzu abunda kakeyi ka kyauta sageeru yanzu bazaka fito da mata kayi aure ba ehhh???

    ” Haba hajiyata wanene ya tabomin ke, kuma hajiya har nawa nake?? Gaba daya fa kwanan nan nafara aiki???

   ” kayimin shiru kafin raina yakara baci shekara 30 da daya fa zakayi shine yaro…tun kana karatu nace kayi aure sai kacemin wai ai bakada lokaci sai kagama yanzu ka gama har kazama tsohon ma’aikaci amma katsaya wasa haba sageeru bakaga kanninka na uku yayi aure ba, ko sokakeyi ayimin dariya???

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button