DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

     ” Eh nima din tare zamu tafi sai kitsaya su baffan su fito ko?

    “Au ai nayi tunanin ke zaki zauna dashi tare da ramlat?

     ” aa mamanki zata zauna dashi ramlat gida zata koma…

  Suna tsaye sai ga baffa sunfito bayan sunyi sallama suka shiga mota sannan suka tafi suna isa suka bude gidan bilal ne yazo hucewa yace yasmin dama magana zamuyi?

     ” tsaki tayi tashige gida can sai yayi ihu yace daman rufamiki asiri zanyi tunda babu mijin aure sai kizo a taimake ki in aure ki shine zakiyi min iskanci to indai muna gidannan maga masu kwasar ki….

   ” Hajiya suwaiba ce ta rufe kofar tare da fadin ohhh su dai sun tsotso tsiya marasa kunya da tarbiya Haka zaku kare dai….

    ” brstr ramlat tunda tabar asubutin ta tafi gida sai take ganin kamar mumy zasu kashe mata aure can sai ta kirawo rabia awaya cikin yanayin bacci tace lafiya??

    ” ke ina lafiya ana cikin wannan hali miji ba lafiya iyaye sunyi fushi dani sosai fa…

    ” To aikece doluwa aikin banza sai me in anyi fushi dake wayasani ma ko matar da zai aura ce tayi masa wani asirin? Kinga ki watsar dasu kitawo aiki gobe in bahaka ba ina tabbatar miki sai sun haifa miki ciwon zuciya waye kula da namiji yanzu? Sai sokuwar mace?

    ” Haba rabia mijina shine rayuwata fa banda kamarsa shida iyayena kina nufin na bujere musu?

    ” kaji banza tsaya su hada miki damuwa kema ace ciwon hauka ya kamaki kifito mu shakata yarinya….

    ” kumafa hakane kawata shawarar ki ta karbu kinga kinfine iya case fa??

    ” hahaha..sannan rabia ta kashe wayar cike da dariya acikin fuskarta can tayi wani tafe tare da fadin ai wallahi sai na kashe miki aure sai kingane kawance ba da kowa akeyi ba…

   Cikin ikon Allah jikin dr sageer yayi dadi dan har sallar asuba yayi suna ‘yar hira da mama yace mama aure nakeson karawa Amma kuma ina tsoron matan…

    ” Murmushi tayi tace sageeru kenan yaushe kasamu lafiyar ma? Kabar zancen nan sai an kwana biyu..

   ” Tohm na amince amma ke nakeso kisamo min yarinya mai tarbiya mai ilimin addini DanAllah kinji??

    ” To Ni yaya zanyi sageeru dama hajiya kagayawa tafini hulda da mutane ai…

    ” Ai duk maccen dake jure akwai da babu itace mace..

    ” sageeru kenan yanzu sai zuwa kwana biyu sai a sallameka kenan??

    ” Ai na warke anjima karfe 4 akwai wacce zanyiwa cs…

     ” Haba sageeru yaushe ka warke din ka hadata da wani likitan sai ya yimata….

     ” Mama banga amfanin aikina ba idan bana taimakon talakawa domin wannan matar danake gayamiki satinta daya a asubuti batasan wake kanta ba sai shekaran ko abincin da zataci batada shi ko kudin ganin likita tana cikin halin taimako sosai…

     ” Tohm shikenan sageeru Allah yakara budi da takawa da imani …

     ” Ameen mama….

Yasmin ce ke zaune tanacin abinci sai kuwa hajiya cewa tayi kinga har an sallamesu har ya huce asubutin sa…

     ” kai amma anya ya warke kuwa??

     ” ina wata warkewa? Kawai dai kinsan mutum ne mai taimako…

     ” Allah sarki Allah to yakara lafiya..

    ” Ameen … Nikuwa yasmin har yanzu babu tsayayye??

      ” Murmushi tayi zuciyarta cike da kunci tace Allah bai tsayar ba,Amma munata addu’a..

   “Hajiya tace ai dama abun na Allah …Allah yabada nagari ..ameen tace sannan tatashi tayi cikin dakinta da wayarta ke faman ringing…

    ” Hello yasmin ykke yusra ce …..
  
   ” Banza sai yau kikaga damar kulani to kinkyauta…..

    ” wayata aka sacemin shiyasa ankawo kudina ansa wata 5 fa..

     Haba danAllah congrat Allah yasa damu za’ayi…

   ” Ameen yasmin DanAllah ki amince da dr sageer ba lallai sai mara mata ba kowa fa da zabinsa da Allah yayi masa ke dai kiyita Addua Allah ya tabbatar muku da Alherinsa…

     ” bazaki gani ba yusra bafa wani sona yakeyi ba kawai yaudarata yakeyi…

   ” kada ki yanke wannan hukuncin kibashi dama yasmin…kuma kisani wayake auren soyayya yanzu? Malama anayin aureni dan kauna in akwai kauna ai babu wulakanci da tozarci kuma dan a rufawa juna asiri ne, dukiya ba itace aure mai wadatar zuci mai tsoron Allah wanda zai kula dake wannan shine mai sonki…

    ” Yasmin ce tace tabbas hakane dan bazan manta maganan malamin mu ba da yace idan kuntashi adduar miji kuce in talakane Allah yabaku mai addini mai kuma sanaa in kuma mai kudine Allah yabaku mai addini mai kuma aiki dashi…

Hakane kawata nagode sai kinjini, sannan suka kashe wayar…

   Dr sageer dake zaune akan kujerar sa yana cin abinci wayarsa ce tafara ringing salama yayi sannan yace wake magana…

     ” yasmin cikin rashin kulawa tace nice dama mama tace mekakeso adafa maka??

     ” cikin murmushi kamar tana kallon sa yace duk abunda kika dafa ai zanci…

    ” yajin naka?

” Naji sauki ai..” Allah yakara lafiya..

    ” Ameen nagode my queen Allah ya mallaka min ke a matsayin matata yadda nake sonki Allah kadai zai shaida…

    ” Batare da tace komai ba ta kashe wayar cike da murmushi tana fadin kai kasani…

    Hajiya suwaiba ce tashiga cikin part din su mamee ko sallama batayi ba tace tabbas kun nunamin ku makiya nane kunsaka hassada da bakin ciki acikin ranku tayaya zakuyi gaba to sageeru dai bai mutu ba, haruna kuma sharrin ka kai da isa akanku sai kare marasa mutunci kawai…

    ” Dukkan su babu wanda yayi magana dan  suna shayenta sosai da sosai…

   
   Abida dake faman kuka tana kaci amanata garba baka kula dani baka sona har yaushe mukai auren zakaci kishiya hatta kusa dabi baka zuwa …

    ” Garba ne yace ai ko jaki yanason kulawa da hutu ballantana ne mutum, menene bana yimiki acikin gidan nan menene bana baki tundaga kan ruwa har reza?  Bakya tsafta kwata kwata dubi dakinki sai kace na mahaukaciya naga har tsintsiya sai na siyo?? Bakya kitso akan kari bakya dan kunshin nan da mata sukeyi ke harma irin style dinkinnan bakyayi wanda zan kalleki naji sha’awar ki komai ina baki har kudi kaya abinci komai akwai ayimin naji dadi ne baza’ayi ba ba? Dan haka aure babu fashi, karatun Alkur’ani tunda muke agidannan banga kinayi ba to uban me kikeso nayi miki??

    ” Kuka tasaka tace inshaa Allahu zangyara har sallah ma zantsayar inshaa Allahu kayi hakuri sannan ta durkasa…

    ” bakomai abida ni ina kaunarki shiyasa natsaya ina gayamiki gaskiya…

   ” zangyara inshaa Allahu mijina…

    Ramlat ce ta fito daga wanka tana amsa waya nan dr sageer ya shigo jakarsa kawai ya ajiye sannan ya rungumeta my brstr kullum kyau kiketa karati sannan ya sumbaci bakinta…

    ” shiru tayi sannan tace wane irin so kakeyimin dr?

   ” kara rungumeta yayi sannan yace wanda bazai fadu ba…

    ” Nan tafara sakashi fita hayyacin sa tabbas mijinta daya tamkar dubu ne samun mai hakuri irinsa sai an tona…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button