DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

K’wance take kan gado tana faman danna waya cikin zafin nama ya k’wace wayar ramlat wai ni banida lokacin ki ne??

     Haba ya zaka kwacen waya wai sokake na goyaka?? Kokuma sokakeyi na daukeka naga kwance nake akusa dakai..

     ” Amma kinsan ina bukatar hankalij ki ko ina bukatar ki yanzu…

     ” Tsaki tayi tace to gani ai kabani please nakarasa chat dina…

     ” Shiru yayi mata sannan yace kiyi ahankali ramlat banjin dadi sosai fa, rungumeshi tayi sannan ta sumbace shi cike da son mijinta tace sannu husby Allah yasawake yakara sauki…

     ” Rungumeta yayi cikin yanayin soyayya yafara kissing dinta cikin soyayya tafara mayar masa da martani daga nan suka wada wata sabuwar duniyar…

   Da asuba dakyar yasamu yaje masallaci saboda zazzabin da yarufeshi bayan karfe 6 ramlat tatashi tana kokarin hada tea sai kuwa cewa tayi jikin nakane??

   ” Daga mata kai yayi tace bari ta kira dr yace aa basai ta kiraba nan ta shiga kitchen takirawo rabia tace kwalliya yaufa bazan zoba jikin dr yayi tsanani…

    ” ke brstr bakida hankalin namiji zaki tsaya kina kulawa dashi ki wacce irin shasha sha ce??

    ” Kina nufin natsallake shi nafito?..

  ” kwarai ma kuwa ai namiji ba dangoyo bani inda kece bakida lafiya fitarsa zaiyi kifito muje gurin bikinnan kinji?

    ” hahha angama aminiya yanzu zan shirya sai natawo…

    ” tea din data dora takashe sannan ta shiga wanka tana shirayawa dr yace ina zakije?

     ” Office mana akwai abu mai mahimmanci da zanyi but kafin 3 ma zandawo sannan tadauki jakarta cikin zafin ciwo ya lalubo wayar mama bugu daya ta dauka tace lafiya sageeru???

    ” Mama danAllah ki dafamin abinci akawomin kinji…

     ” Tohm shikenan ta kashe wayar ta kalli yasmin tace dora couscous da miyar hanta sai ki hada salad da lemon kankana…

    ” cikin biyayya tace baffa me kace nahada maka ma??

     ” auta kiyi duka iri daya sai azubamin…

      ” baffa ne yace lafiya naga wayar sageeru??

    ” to dai lafiya ba lafiya ba tabbas yaronnan yanada wata matsalar wallhi dan bakaji muryarsa ba,abinci yace adafa musu…

     ” To in zanfita sai yasmin tabini sai takaimasa, yanzu bari naje nayi wanka dan hajiya suwaiba tana hanya amma gidan dr zata sauka…

    ” Tohm shikenan

Alhaji isa ne yace kai bilal ina kudin daka dauka?? Banson iskanci fa yanzu alhaji mudi ya dauke motata abashin da yake bini.

    ” Bilsl ne yace haba baba ai kudinnan munriga mun kashe tuntuni…

    ” mamee ce tace oho muku dai nidai abani kudin ankon dana fada…

      ” Abida datazo tace gaskiya baba da kaida Alhaji kubawa baffa hakuri ko kwasamu wani rangwamen…

    ” Alhaji ne yace zakici ubanki mahaukaciya sai mun wuhulakanta shi kuma kitsaya kigani…

    ” Shi dai alhaki kwikwiyoni duk abunda kayi babu makawa sai anyi maka kuma wallahi babu ta inda azzalumi zaiyi gaba gashinan nayi auren amma kullum ina gida abunda kuka shuka sai bibiyarmu yakeyi…

    ” Mamee ce ta rufeta da duk’a tana zazzagenta har tashiga dak’i..

  Dr sageer daya jingina ajikin gado sallamar hajiyarsa yaji cikin rashin karfi yataso da daddafawa yakarasa..

     ” Sageeru lafiya dai subhnlhi ina ramlatun??

    ” Dakyar yazauna akan kujera sannan yajingina yace sannu da zuwa hajiya..

    ” Ai kai zanyiwa sannu sageeru yaushe jikin yayi haka???

    ” dazu ne..” toh ina ramlatun??

    ” Ta tafi gurin aiki..

” yanzu dan rashin imani da tausayi ahaka tafita tabarka subhanallahi anya kayi sa’ar mata kuwa??

     ” Sallamar yasmin sukaji tasaka doguwar riga blue da farin mayafinta sai k’wandu na a hannun ta ahhh hajiyarmu yaushe kika karaso??

    ” Ja’ira bayan kinki zuwa garin namu?

   ” hajiya kenan bazaki gani ba garin nan fa banason sa kwata kwata yanzu dai yagida ya hanya??

    ” Lpyalou ….ina samarin naki??

     ” Murmushin karya tayi tace samari sunanan sannan ta kalli dr cikin dakewa tace ina kwana ya sageer…

    ” dakyar yace lafiya sannan yayi shiru abunka da mai haske duk fuskarsa tayi ja gakuma idonsa dayayi jajir sai dan karamin nishi dayakeyi…

    ” hajiya ta kalla tace bashida lafiya ne??

    ” Yanzu nazo naganshi ahaka tunda kinzo taimaka wa yayan naki kibashi abinci wannan wawiyar matar tasa tafita…

    ” Dan shiru tayi sai jitayi yace DanAllah..

    ” Ni bari nashiga gidan hajiya hansatu mugaisa…

    ” yasmin ce ta zuba masa abincin sannan ta ajiye masa akusa dashi amma sam yakasa motsawa sai dakyar yadau cokalin yana dauka ya wadi saboda rawar da hannun yakeyi…

     ” Yasmin dake satar kallonsa ta tausaya masa sosai aranta tace wannan wacce irin matace mijinta na wannan halin zatafita?

     ” zai dakko cokalin yasmin ta tashi ta dau abinci cikin sunkuyar da kai ta bashi sai da yagama ci tabashi lemon riki hannunta yayi da hannunsa dake dauke da zafi yace yasmin DanAllah kisoni danAllah..

    ” Shiru tayi tana tausaya masa tace yaya so fa kace?? Kaima yaudarata zakayi kenan?

     ” yasmin ke dai ki aminci min kigani inhar da yaudara nazo…

      ” hmm tatashi zata tafi sannan tace kanemi wata ba dai niba kagani..

     ” haka tatafi tabarshi yana wani irin tare mai gigicewa…

     ” mumy din ramlat ce  tana sallama taganshi acikin jini caba caba aguje takarasa tana innalillahi wainna illahirrajiun dr sageer??

    Assalamu Alaikum

Tabbas kun cancanci yabo da kuma godiya masoyana nagode da irin kaunar da kukeyiwa wannan littafin ina kuma fatan kuna amfana da abunda ke cikinsa? Kuma ina neman afuwarku abisa jimawa danayi banyi rubutuba wani uzuri ne ya rikine…lurv u oll

Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment…
  
  Let me know what you think about this page…Ku gayan ra’ayoyin ku…

    i request you to avoid spelling and grammar error….#TEAM DS

   Mumini na qwarai shi ne wanda yake yarda/amincewa da duk abin da Allah SWT ya tsãra kuma ya zartar, abin da yafi alheri shi ne duk abin da Allah SWT ya zã’barwa bãwansa mumini; bã abin da shi muminin ya yake so ba ko ya zã’barwa kansa..

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:24 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 35-40

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Yasmin dake faman kokarin  samun mota sai ga hajiya suwaiba nan ta karaso cikin karamci da dadtaku irin na manyan mutane tace yasmin har kin fito??

    ” Eh hajiya naga dare yanayi kuma zan shiga makaranta da safe kinga na kwanta da wuri ko??

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button