DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

    ” Murmushi tayi tace lahhh hajiya bakomai fa kawai jinin mu yazo daya ne… ” Da bakyason sa bazakiyi wannan murmushin ba bazakuma kiyi magana a hankali ba abunda nakeso kigani shi miji nagare shine wanda zai soka koda mutane na zagin ka kuma kigane cewa ita soyayya masu hankali akan saba kuma a daidai ta, kuma ki daina tunanin sai wanda ranki yakeso aa kiyi adduar nagari mai addini wanda zai tararrayi ki, tabbas nasan sageeru yana sonki Amma kuma ya kamata ki amince bawai ina goyan bayansa bani aa kinsan yana da matsalar zuciya kuma zanso ki kasance akusa dashi…

    ” Ita dai yasmin batace komai ba har hajiya tafita palour…

    ” wayar ta ta kunna hotonan sa ta shiga dannawa kallonsa takeyi cike da kauna..

    Mama ce tace daman hajiya inaso muyi magana kafin ki tafi?

    ” Akan me fa?

” A kan sageeru ne dayace a nemar masa mata ni kinga ba harka nake da mutane ba kamar ki ko ke zaki duba masa dannaga yana bukatar karin aure…

    ” To ke banda abunki ga yasmin nan me zai hana ahadasu…

    ” Nasan halin yasmin hajiya ba lallai ta soshi ba kuma kinga shima dr sageer din ba lallai yasota taba kina ganin yadda ake sokarta cewa taki auruwa nafeson daidai da’ita ya aure ta….

    ” Mama kenan ne zanyiwa baffan magana inyaso sai abasu lokaci zakiga in suna son junan su…

    ” Mama ce tatashi tashiga daki nan takira aisha tagayamata…Aisha ce tace ai mama kece baki saniba yasmin ta dade azuciyar dr ai ke dai kawai kiyimata addua Allah yasa alkhairi ne ….” inshaa Allah sannan ta goge hawayen ta dama zanga auren yasmin Allah nagode maka…

    Alhaji haruna ne yafito yaga baffa ya chanja mota tsayawa yayi yana kallon ta can yace kace kafara sayar da kawonan mutane kazama dan fashi ko dan mafiya in ba mafiya ba uban wa zai baka kudinnan dakake samu…

    ” Baffa babu abunda yace sannan ya huce bangarensa….

     ” Nan hankalin su isa haruna har su khalil ma duk yatashi sai jafa’i suke jawo mada… matar isa inna itace tayi magana tace ai bakuga komai ba tunda zalunci kuka saka agaba…

     A lokacin dr sageer ya shigo kallon motar yayi tayi bala’in kyau sannan yace musu sannunku ya shiga part din baffa bayan sun gaisa da baffa sannan ya shiga cikin palour hajiya da mama suna zaune suna hira yayi musu sannun su sannan yace mama ina yasmin?

    ” hajiya ce tace me zakayi mata da tsohon daren nan?

    ” hajiya sak’ona zan karba

     ” Tana daki bari na kirawo ta tana fitowa yarasa me zaici mata sai kallon ta yake sai kuma yace turamin suratul bakara please…

    ” hajiya tace ina na wayarka?  ” hajiya nayi deleting dazu bansaniba….

    ” Yasmin tace bari na dakko maka memory din sai kayi copying…

    ” sauri nakeyi please ki mikomin mota..

   Tana fita ta tarar dasu carko carko suna ta gulma karasawa tayi tace ya dr gashi karba yayi yace wallahi nakasa sukuni kwatakwata so nakeyi kawai naganki shiyasa na biyo domin naganki zani gayamiki son da nake miki cikin raina zankula dake please ki kula dani…

   ” Shiru tayi tana kallonsa domin kalar tasa kaunar tana burgeta…

   ” Darajarki a zuciyata tana karuwa, Wahalar sonki nashata sam bana damuwa, wallahi banki ace yau zaa daura auren mu ….

     ” Murmushi tayintace kayi ahankali karsu mamee suji please…

    ” To yaushe zaki bani amsata??

    ” zanbaka ga wannan sannan ta juya tana zuwa gurin su mamee maryam tace iyayan asiri za’a asurce shine, khalil ne yace ai dr bazai aureta ba komai nacinta a daije akare da masu faskare….

    ” Yasmin ce tace Allah ko ke ai zai soki sai kije ki aure shi tunda ansaba bin dutse…can tace ko bahaka ba Alhaji….

    ” Nace ubanki ne yake bin kan dutsen banza masu yankan kai….

    ” ubana yafi karfin ku wallahi nangani nan bari nagaba yayi gaba sannan nan tashige….

    ” Hajiya tace ke dawa yasmin nida wayannan ‘yan rainin hankalin…

   ” Mama tace banson tsokana salan suzo su zazzageki…

   Dr yana shiga brstr ramlat tace munafiki tsinanne mai bin mata kagama kazantar taka shine kashigo???

   ” Cikin zafin rai yakifa mata mari mara mutunci naga take taken ki wallahi sai kingane kuranki mara mutunci duk hakurin danakeyi dake??

    ” hakurin me to wallahi sai dai kazaba ko kafasa kara aure kokuma nabar gidan ….

   ” Waya hanaki bari tafi yanzu ma sai kindawo kuma aure nan da 2month sannan yashiga daki kuka takara saka gashi tajawo sunyi fada gashi tana bukatar mijinta dakin ta shiga ta kwanta akan gado kusan awanta 2 tanata juye ahaka har dr ya fahimce ta nan yafara sarrafata har hankalin ta yatashi daga nan tafara kissing dinsa cikin kidemewa har sai da suka shiga wata sabuwar duniya….

    Da asuba rabia ta kirata tace lallai kibar gidan kitafi gida yazaba ko ke ko aure…aikuwa ta biyewa rabia da safe tatafi….

   ” ya shirya zai tafi aiki ya kirata ta gaggaya masa magana cikin zafin rai dakyar yake tukin har ya’isa kofar gidan ya kira yasmin yace please tafito zata ga black mota…

   ” Mayafin ta ta yafa sannan tafito ta bude motar tashiga cikin damuwa da idanun sa sukayi jajir yace zaki aure ne yasmin please kada namutu…

   ” Yasmin ce tace so ai baya kisa…

   ” Amma kema kwanakin baya aikin san zafin soyayya da masoyin ki ya gujeki ko??

    ” Shiru tayi tana kallonsa…

    Dani dake akwai alak’ar mu ta ‘yan uwa, zuciya tawa ke ta kama, komai wahala dake zani kasance, Alkawari ki rik’e komai wuya kar mu rabu kinji… rashin yarda dani zaisa nafada halaka ki taimakawa ruhina kisoni danAllah ni ke nake so yasmin…

   ” Cikin hawaye tace kai daya na yarda muyi soyayya acikin ruhina, banyi zaton zan kamu da soyayya a nan kusa ba, Na baka dama kasan kaunar ka, tabbas nagani bani da tamka kaine kadai zabina, kai kagwadamini son da kakemin dan na shaqu da da kai, sannan ta rike hannun sa tace na baka amanar kai na…

  Assalamu alaikum

Kuyi hakuri masoyan wannan littafin tabbas ina cikin busy ne shiyasa banayin post akai akai Kuyi min afuwa masoyana ina tare daku….

   Ko yakuke ganin wannan soyayya???

   Yasmin da dr sageer sun dace??

  Barister ramlat wane hali zata shiga in taji labarin yasmin zai aura???

   Wacce irin k’awace rabi’a??

   Ko yaya auren su dr zai kasance???

WANNAN SHAFIN  SADAUKAR WACE GAREKI MATAR KIRKI MATAR K’WARAI UWA GA ‘YAN BIYU WATO ANTY MAI JIDDA ALLAH YASAKA MIKI DA ALKHAIRI YAKARA SOYAYYA DA MAIGIDA

   I can’t stop apologized for the  spelling and grammar mistake’s

     How was the page???

    _Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM….DS

Wadãtar zuci {Qanã’a}

Duk wanda ya wadãtu da abin da Allah SWT ya bã shi; to, zai sãmu nutsuwar zuciya da kuma dãcewa a rãyuwar duniya da qiyãma.

Allah SWT yana fad’a cikin suratun Nahl ãya ta (97) cewa:
(( Wanda ya aikata aiki na qwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mumini, to, haqiqa, Muna rãyar da shi, rãyuwa mai dãd’i. Kuma haqiqa, Muna sãkã musu lãdarsu da mafi kyawun abin da suka kasance sunã aikatãwa )).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button