DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

Manyan Malaman Tafsirin Alqur’ãni da yawa sunce game da wannan ãyar shi ne:
( Rãyuwa mai dãd’i a duniya shi ne wadãtar zuci ).

Sannan kuma duk mai wadãtar zuci yã rabauta bisa ga abin da Allah SWT ya bã shi, kuma ya kasance arziqinsa dai-dai buqãtunsa, wato ya kasance tsakãnin yalwar kud’i da kuma talauci.

Don kasantuwar komai tsakã-tsaki shi yafi; Nawa nawa ne mai kud’in da kud’insa ya shagaltar da shi ga barin sanin Ubangijinsa ! Kuma nawa nawa ne talaka wanda talaucinsa da neman abincinsa ya shagaltar da shi ga barin bautar Ubangijinsa !!!

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com 

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:24 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 50-55

DOCTOR
SAGEER

NA NANA DISO

http://deejarhberver.wordpress.com

© HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Doctor sageer ne gaba daya ya gigice don bai taba tunanin wayannan zafafan kalaman daga yasmin ba kallonta yayi sannan yaja motarsa sai wane babban super market Nan yadinga kwasar mata kaya har sai da tace doctor lafiya kuwa…

” kallonta yayi yace samun mace irinki sai an tona yasmin bansan me zanyi na faranta miki ba nidai nasan banda kamarki ina cikin damuwa Amma gaba daya k’in yayemin ita lokaci guda ina kaunar ki matata to be…

” wane murmushi tayi dayakara fito da kyanta tace Lallai dr ma yanzu da k’a dakko ne me zancewa su mama in nakoma?

” yasmin kenan har yanzu soyayyar tawa batayi nisa cikin zuciyar ki ba kenan?

” Bahaka bani kasan dai da kunya nagaya musu ai…

” oyaa muje kisha drinks wane bakery suka shiga suna zaune kowannen su yana kallon juna yasmin kuwa mamaki duk ya rudeta wai dr sageer ne ke sonta tabbas ta yarda wane hanin ga Allah baiwa ce babu irin kalar soyyayar da bata gani ba daga karshe suka gujeta…

” baby yasmin me kike tunani??

” Murmushi tayi tace rayuwa.. ” banson kina dogon tunani please tohm shikenan…

” Barister rabia adaidai lokacin ta shigo bakery din ba mamaki dr sageer tagani da yasmin, dariya tayi sannan tace lallai nasamu babbar hanyar kashe miki aure ramlat, zama tayi nisa dasu sannan ta kirawo barister ramlat tace ke hau whatsapp yasmin tanata murmushi ta daukesu ta tura mata…” kai rabia ai yasmin ce wannan…” To koma wacece gatanan sai soyayya suke da mijinki laahhh kinga ma yakusa kissing dinta subhanallahi.. ” kuka ramlat tasaka sannan tace wallahi sai anraba auren mu tasa kuka….” rabia tace koni ce ai saina sa yasakeni daman nace miki iskancin sa kawai yakeyi kuma aikin gani…

Mumy ce tace Yarinyar banza da wofi ni banga amfanin ilimin kiba ramlat tayaya miji bazai karo aure ba? Kinzama kazama mara ladafi ga dinbin hauka to wallahi ni bazaki zauna agida na ba adinga zagina ana nunani da baki ana kirana da asararriyar uwa sam kafin ubanki yadawo yayi miki duka kitattara ki koma danni ba irin sha sha shen iyaye bani…

” Mumy bin mata fa yakeyi yanzu ma rabia taturomin hotonsa da wata…

” koba kawaba ai sai takashe auren zata hutu sau nawa ina miki kashedin rabuwa da rabia baki jiniba ko? To wallahi nakarajin kincewa dr dan iska sai kingane kuranki ..

” Ai dama bakwa sona yana cutata amma kun goyi bayansa…

” dallah yimun shiru akwai son da yahuce nayi miki addua kikasami miji nagare wacce kowacce mace take fata nakuma aura miki shi sannan nace kizauna dakinki ki neme aljannar ki??

” Amma ai…

” yimun shiru ja’ira kawai ki dau mota kikoma gidanki…

” cousin din ramlat ce tace aikam kawai wasu neman auren ma sukeyi amma ke kinsamu sai iskanci kikeyi sai ki kaso auren ki dawo kiga ko damai kwasarki…

” brstr ramlat dataga bazata samu goyon baya agurin su ba, cikin ikon Allah sai ga dr sageer ya kirata after magrib yace tafito su tafi cikin borin kunya tafita Amma shi bai ce mata kala ba…

Tunda suka dawo babu wanda yayiwa juna magana sai ma wanka da barister tashiga tana fitowa ta tarar da miss call din rabia sauri tayi ta kirawo ta tace kee lafiya da daddaren nan….

” Dallah kinyi masa zancen yasmin din danagan su tare? To karkiyi kizama mara yanci gwara ki sanar dashi yasan kinsani…

” Ai daman zangaya masa hauka nakeyi nayi shiru aikinsan abunda bazai yihuba kenan…

” bayam ta katse wayar sai tasa kayan baccin ta nan ta kalli cikin ta har yafara fitowa murmushi tayi takara turoshi sannan ta nufi dak’insa, tunda tashiga yake faman kallonta saboda tsabagen kyan datayi masa shi daman doctor yana bala’in son yaga matarsa da sleeping dress…

Zama tayi tace wannan yarinyar ta nuna hoton yasmin awayarta tace menene Alakar ku?

” kallonta yayi yace budurwa tace kuma itace wacce zan aura…

” Ashe kuwa baka siyawa kanka farin ciki ba indai kayi auren nan zaga yadda ake hauka wallahi…

” Murmushi yayi yace au kinfasa tafiya ne? ” kuka tasaka masa daman ni baka sona baka kaunata ai shiyasa kakemin abunda kakeso…

” Tasowa yayi ya zauna kusa da’ita ne ina sonki ina kaunarki matata sai dai kuma narasa wa’yanda suke zugamin ke, shafa cikinta yafara yana this my baby endless lurv for you…

” Rungumesa tayi daga nan kuma yafara kissing dinta batasan lokacin datace inasonka dr i can’t live without you nan ya shiga sarrafata sai gurin 10 yasaketa yayi wanka….

Mama ce tace Baffa kaga siyayar da sageeru yayiwa yasmin kuwa nidai lamarin nan yana bani tsoro…

” hajiya suwaiba tayimin bayanin zan tambayi yasmin din ko tana sonsa tukunna…

” Allah mai iko kaga sai yanzu Allah yakawo mijin anata abu ashe shi mijin nata yana kusa da’ita ma…

” Ai daman haka sha’anin Allah yake sai dai in mutum baiyi hakuri ba, sai ki kirawomin yasmin din ..

Tana shiga ta tarar da ita azaune tace yasmin..

” Naam mama? ” kizo inji baffa yana kiranki…

Tana fita ta zauna akusa dashi tace gani baffa…

” Yauwa auta maganar sageeru ce yazo akan cewa zasu turo sati mai zuwa kuma nayi miki alkawarin bazan yi miki auren dole ba sai ki sanar dani ko kina sonsa?? Banson bata kunya ke ‘yatace kina ban shawarwari ballantana kuma maganar rayuwarki ki bude baki kigayamin da kanki banson na zalinci ki…

” Shiru tayi nadan lokaci har sai da yakara maimaita magana sannan tace eh baba sannan tamiki tabar gurin tana shiga ta rufe kofar dakinta tare da murna daman zanyi aure nan ta kwanta cike da murna…

Yau ramlat da zazzabi tatashi sosai har sai da yasaka mata karin ruwa sai shagwaba take masa saboda sha’awa datake tada masa yasa yabar gidan…

Hajiya ce tace yasmin taimaka mini danAllah kije min gidan sageeru ga atampopin matarsa sai kuma kiyi mata sannu…

Gaskiya hajiya matarsa bada kirki kinga kartayi min sharri wallahi…

Mama ce tace au bazaki je ba kike nufi tashi kitafi kafin ranki ya baci, ai babba baya aikin ka kace aa..

” Hajiya ce tace ai yasmin da gaskiyarta ramlat bata da ta ido kwatakwata daman sageerun yace bazai fito ba yau ramlat din ba lafiya shiyasa…

” yasmin dai ba’ason ranta ba ta yafa mayafi daman wata duguwar rigace ajikinta tana fitowa ta dau kayan…

” Hajiya tace kiyi shatar abun hawa kina kaimata sai ki dawo…

” Tohm hajiya…

Lokacin da yasmin tafita ta tarar da ahmadu mai adaidaita ko zaka kaine sabuwar unguwa??

” Muje mana yasmin sunatafi suna hira har suka isa dataje gidan shiru tayi sallama yayi sau 10 apalour din amma ramlat batace uffan ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button