DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

” yasmin aranta tace ai wallahi ni bazan dau rainin nan ba sannan tace gashi inji hajiya in yadawo abashi…
” ramlat ce tace to dan mikomin wannan bazan iya tashi ba..
” ita kuma yasmin taga daidai cikint ne shine taji tsoro amma dataganta akwance sai ta taimaka mata ai kuwa tana durkusawa zata miko mata sai ga dr sageer nan ihuuu ramlat tasaka sannan tace wayoooo zata kashemin baby muguwa azzaluma….
Yasmin da gaba daya tatsorata sannan ta jiyo taga dr sageer ya shigo idonsa har wank jayayi…
” ramlat ce takara da cewa wayyoo cikina nashiga uku wallahi indai da’ana ya mutu sai nima na kashe ki kuka tasaka ramlat yasmin kuwa da ta miki sanin kanta dr yans bala’in son yara bata ankara ba sai taji mari…
” Daga aiko ki cikin gidana shine zaki gular mata ciki da hannu yasmin kashemin ita zakiyi da baby na???
” ramlat ce tace Allah yaso kagani da idon ka da sai ace sharri nayi mata…
” yasmin batace komai ba sai kuka haka tabar gidan mota ta hau sai kuka take har ta’isa gida mama da hajiya na palour tazo ta hucesu tana kuka hankalin mama yayi mugun tashi amma sai tayi ta maza ta dake…
” Hajiya tace ohh ni suwaiba me kuma yafaru?? Duk sukayi dak’in…
” yasmin tace daga nashiga gidan sai takarasa musu labarin tana kuka amma batace dr ya mareta saboda mama zata iya shiga damuwa hajiya kuwa sai tace sai ta rama mata…
” Mama ce tace Allah yasawake ke kuma da kuka bayayi miki wahala ai sai kiyita yi….
” Hajiya tace yi hakuri auta kinji aniyarta ta bita Allah ai baya zalunci…
Abida kenan cewar Amal irin wannan kyau haka kinsa rake da zuma sai sha kikeyi inci dai dawani sirrin???
Wallahi amal ban cushe cushen kayan matan nan wannan fruit din idan nadinga sha sun isheni ke bakiga oga yadda yake gigicewa ba wallahi, kuma kinsan wani abu harda rashin tsafta yakansa maza suja baya da kai ke dana gyara bakiga yadda yake mutuwa akaina ba…
” Ke wallahi gaskiyar ki wata makociyata zainabu bata rabo dasu kwakwa da aya ke har kantu kullum cikin tauna da lemo takeyi innaci mata ke bakya gajiya da cinsu sai tacemin ke gyarane ba kadan ba ai sirrin su sai mai yi…
” Wallahi kam ai indai mace ta dage da biyayya da kula da kanta ai sai sambarka wallahi…
Hakane wallahi..
Yau kusan sati guda kenan yasmin ko wayarsa bata dauka bama tabari su hadu gashi ankawo kudin aurenta dubu dare biyu ansa biki wata 4..
” mama ce takira yasmin dak’in tace lallai yasmin nalura fushi kikeyi da dr kenan?
Mama goyan bayanta fayayi kuma yasan karya takeyi…” haba yasmin mutum akan abunda yakeso ai makaho ne kin manta son yara irin na sageeru to bari kiji wata rayuwa zaki fara wacce gaba dayanta hakuri indai kinason ganin daidai kinaso kuma ki dace, dole sai kin kau da kanki kinyi kuma hakuri sosai kuma ki tsaya ki karanci mijin ki sosai, bakiga komai na makirci ba kwata kwata saboda bama kufara zama guri daya ba kissa zaki koya karki zama ballagaza, kina gani dai ni mahaifiyar ki kwata kwata banda kishiya amma kinga dai da idonki abunda facaloli sukeyi min ko kadan basa sona kina dai ganin sharri kala kala.
Akwai lokacin da mamee tacewa mahaifin ki wai nasatar mata kudi yadauka yabiya Yazo yanata bala’i ko uffan banci ba sai ma hakuri dana bashi lokacin da yazo cin abinci muna hirar mu mai dadi sai ce masa nayi tunda muke da kai ai bantaba yimaka sata ba kuma duk halin da muke ciki ai bangayawa kowa, kinsan me yace?? Sai cewa yayi sai daga baya naga bankyauta miki ba Amma kiyimin afuwa wani sa’in in aka gayamaka wanda kafiso yayi maka laifi burin ka kayimasa hukunci adaidai lokacin…
To kinga ita rayuwa tagaji haka hakuri zakiyita yi kuma ki tararrayi mijinki kinji…
” inshaa Allahu mamata inasonki tunda natashi baki taba yimin hudubar tsiya ba ba ki taba cewa in zagi wani ba baki taba cewa muyi wane mugun abu ba tabbas kincika uwa tagari Allah yasaka miki da Alheri…
” Ameen auta
Yasmin na zaune tasaka wata blue rigarta irin sun matseta mikewa tayi ta dau wayarta suna magana da wata ‘yar ajin alokacin dr sageer yayi sallah dawowar sa daga asubuti kenan babu kowa adak’in sai ita daya…
Tashi tayi ta cigaba da wayarta batare da tace masa uffan ba tashiga daki…
Dr sageer gaba daya hankalin sa ya tashi wai yasmin dinsa itace take bada dashi yau through out yakasa cin abinci yasan yayi kuskure but yasmin time ne da zatayi masa uzuri…
” Aa dr kaine agidan namu? ” eh wallahi mama daga office na biyo yinwa nakeji please kunyi abinci… ” Tausayin sa mama taji sannan tace munyi bari nakira yasmin ta zuba maka ni zan lika makota anyi rasuwa… ” yasmin fito ki zubawa yayanki abinci ni nafita… ” Toh kawai yasmin tace sannan tayi banza da zancen yafi 30minute azaune dakin ya shiga yaganta akwance tana chatting dayayi sallama a hankali ta amsa ko daga kai batayi ba ballantana ta kallesa…
” zama yayi gefenta sannan yace yasmin DanAllah kiyi hakuri wallahi nayi kuskure kaidin ramlat ce kuma itama tagane kuranta, wallahi tunanin ki yana kokarin nakasa ne please my yasmin sannan ya durkusa please yasmin ki saurari ne…
” Kaga is better ka rabu dani daman ai naga so iriri na shafama, kanunamin gidanka yafi karfin ka ko kiyashi akace maka nakashi bada dalili ba ai ka tuhomeni ballantana dan zalunci na dak’ar mata ciki goge hawayen dake fuskarta tayi sannan tace ahaka kuma ka mari ne, Ni ba marin ne matsalata ba aa yadda dakayi zanyi mata wannan muguntar…
” yasmin am your husband to be, yakamata ki fahimce ni please wallahi inasonki ina kaunarki but nasan nayi kuskure ga fuskata rama marin to…
” tashi tayi zata fita sai ya rik’ota jiyo tayi sai idanuwan su sukayi arba da juna kusan minti uku kenan a hankali yariki hannunta sannan yadaga shi to rama marinki…
” cikin shagwaba tace ni kacika ni bazan rama ba kakyaleni sai tasa kuka…
” To kice kin yafemin cikin wani yanayi yayi maganar aikuwa sai ta fuzge hannunta yakara dankota wallahi in bakiyi dariya ba sai nayi kissing din wannam hot lips dinki…
” cikin tsoro tace sai kace…
Kafin takarasa yakai bakinsa sauri tayi ta turesa Allah ba ruwana sai Allah yasaka min ni ba’yar iska bace ba sannan takara saka kuka….
” au bazakiyi shiru ba sokike ki nakara???
” Cikin wani yanayi da ita kanta batasan irinsa ba tayi dariya sannan tafita zama tayi kan kujera yafito ya zauna kusa da’ita ni nasan kanwata bazatayi fushi dani ba….
A daidai lokacin maryam tashigo yasmin ita kuma tana cewa aikaini baka…
” dr sageer ne yasa dariya kinsan Allah wannan shagwabar taki tana rikirkita ni sosai kyau kuma kikeyi in kikayi fushi… amma fa kin azabtar dani sosai 9days please karki karayimin irin wannan….
” Da yasmin ta lura maryam tana tsaye sai ta kashe ido tace tabbas inasonka amma narasa ta’inda zan fayyace maka soyayyar danake maka….
” Murmushi yayi yace nifa dazasu taimaki ne 4 month yayi nisa abarshi 2 please…
” mik’ewa tayi tace nidama 1year akasaka…. ” Ai sai ajawo na zuzuce…” bari nazubo maka abinci…
” Tana fita maryam ta gudu takoma bangaren su kuka tasakawa mamee wallahi mamee soyayya sukeyi kuma kinsan ina bala’in son yaya mamee zaku iya rasani wallahi…
” ki kyale marasa mutunci zanyi maganin su aure kuma basu isa ba…
Yasmin na zaune tana chatting dr sageer yace tashi muje ki rakani mota…