DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

” To sakeshi nawa ne kudin naka?
” Dubu ashirin ne sauran…
” Kayi hakuri danAllah ga kudinka…
Wallahi kayi sa’a anbiya maka da kaga yadda ake gunduwa gunduwa da mutum banza mai bakar zuciya…
” Cikin borin kunya yashiga gida baffa ne shima ya biyo bayansa Alhaji haruna ne yace kai baffa banson munafurci kudin da ba’asan asalin su ba kada kakara kwatar mana riga ko ance maka mu fak’irai ne? Banza mai kudin yankan kai banza mai yarinya karuwa…
” Abunka da mutumin kirki baffa murmushi yayi sannan ya huce cikin gidansa…
Yasmin da ke faman shiryawa tasa wata blue atampha riga da siket gaba daya shape dinta yafito kayan ta ta’iba sannan tafito palour nan ta tarar da baffa sannu da dawowa baffa…
” Yauwa sannu auta sai ki kasance cikin shiri sai karfe 5 jirgen zai tashi…
Tohm baba kwana biyu ni zanyi fa kasan basan benin din nan nake ba…
” Tohm shikenan dan soyamin danKali da kwai…
Tashi tayi tashiga kitchen tana cikin soyawa taji sallamar dr murmushi tayi sannan tajiyo…
” kallonta kawai yakeyi saboda kyan datayi masa ga halittun ta duk sun fito ina zakije kika cancada wannan adon??
” benin zamu tafi nida hajiya…
” aikowa sai dai nima atafi dani…
” dariya tayi tace kafiya tsokana aikin naka fa??
” yasmin kenan kinki ki fahimce ni kenan??
Hajiya ce tace au hirama kika tsaya yi bazaki maza ki gama ba???
” durkusawa yayi har kasa yagaida hajiya…
” lafiya lou yajikin mai dakin naka??
” Alhamdulilahi hajiya DanAllah nima zanje benin din sau mu tawo tare da yasmin…
” haba sageeru aikin naka fa nibanason sha shanci kayi zamanka kaga zai iya yuwa akawo mara lafiya…
” Toh hajiya itama tayi zamanta yasmin din menene amfanin zuwan nata…
” Kasan Allah sageeru babu inda zakaje kazauna kaje ka duba kanin babanka ance zaayi masa aiki babu kudi…
” haba hajiya kin manta abunda sukayi min?? Irin tsanar da suka nunamin?? Shine fa…
” haba sageer kaifa ba yaro bani ai zamani yazo idan mutum yayi maka sharri sai kayi masa alheri kamanta dabaya ka fuskanci gaba Allah yayi maka albarka…
” Ameen yaa hayyu yaa qayyum sannan tafita yasmin tace yanaji kayi shiru yaya??
” Please ki hakura da zuwa banson kiyi nisa dani please…
” Dariya tasaka sai kace wata matarka?? Lallai kai dinnan zuwana babu fashe sannan ta fita gurin misalin karfe hudu suka shirya dr sageer ne ya kaisu har airport amma ko kulata baiyi ba sai hajiya da yabawa uban kudi tana ta shimasa albarka harsunyi gaba tayi sauri tadawo tace yaya lafiya kaki kulani…
” tsaki yayi tare da fadin tunda ban isa dake ba sai kije kiyi abunda kikeso in har kinaso na sai ki fasa tafiya…
” Nafasa tafiya?? Cikin mamaki tazaro idanuwanta haba doctor karkayimun wannan hukuncin…
” shiru yayi yana kallonta hajiya tace yasmin yi sauri mana…
” tafiya ta dinga yi tana kallonsa tana jiyowa har yatafi ahanya yatsa yana cin abinci sannan ya zauna tabbas yana son yasmin soyayyar da bazata fadu ba amma shi yayi rashin sa’a bata sonsa…
Lokacin da suka isa mijin ya Aisha yazo ya dauke su suna karasawa gida yasmin ta rungume aisha kai haka aka gyara gidanki??
” zama sukayi suka ci abinci hajiya gidanta ta huce tana isa tatarar dasu dukkanin su agida kudin da dr yabata ta kasa musu sannan tace ku daure ku samu sana’a DanAllah kuduba kuga fa yaranku duk sungirma amma kullum sai dai abaku…
” Murmushi sukayi duk’an su…
Yau aka kawo lefen yasmin akwati 10 gashi biki har yarage saura sati daya a bikin yasmin doctor bakaramin fushi yayi daita ba har takai baya daukar wayarta tana zaune akan kujera tace ya Aisha nifa gaskiya tafiya zanyi dr yaki daukar wayata…
” Haba yasmin please kibari sai gobe ke akwai abunda nakeso kisani namiji kamar jariri ne sai kina tararrayar sa kuma idan kuka samu matsala babu ke bagayawa wasu mutane hakuri zaki kishiyarki tsakanin ku sallama kuma ki cire kunya ki farantawa mijinki kinasa fitinannun kaya kikuma dinga sarrafa masa girkuna kinji…
” Ita dai hankalin ta ba akwance yake ba kawai binta takeyi da to…
” Mama ce takira waya tace aisha wai menene hakane mazamaza yasmin tatawo banson shirme…
” Toh mama nan suka shirya gaba dayan su sukabi jirgin rana suna isa yasmin wanka tayi kawai tayi sallah sannan takira doctor da wayar mama Kuka tasaka masa lokaci daya jikinsa ya mutu cikin zafin nama yace wacece??
” Kuka tasaka bazan iya jure fushin ka ba, bazan iya boye soyayyar ka ba ina sonka dr sageer, nasan nayi laifi please kayi hakuri, …
” Kashe wayar yayi sannan yayi ajiyar zuciya wata sabuwar soyayyar tace take harbawa a kirjinsa…
Tun daga ranar baizo ba mama tabata kayan da zata kai dinki washe gari aka shirya ayimata jire kannin mama dasu baffa duk sun cika nan yasmin ta dan mikawa kawayenta kati wayanda bata samu zuwa ba tayi musu text a
Wayarta yusra ce tayi sallama suna zaune apalour rungume juna sukayi sannan anty barira kanwar mama da sakina sukace irin wannan kiba yasmin ko zaki ‘yan mun…
Nifa namanta daku ace kuna dangin mu amma ko kuzo inda muke sai yanzu dayake biki ne zaku kwaso kafa…
” mama ce tace banson fitsara ne goggo babar su mama tace haba jikalle kiyi musu afuwa mana kema babar taki ai bazuwa takeyi ba…
” Dariya suka saka sannan akatafi jira kayan dak’in ta mashaa Allah part din yasmin yayi bala’in kyau dan baffa yayi mata orders din kaya masu bala’in kyau kowa sai yabon kayan yakeyi da gidan…
Tun safe su yasmin suke gidan kunshi basu gama ba sai yamma sannan suka nufi saloon ta karbo dinkinta kuma wayar yusra takarba takira dr bugu daya ya dauka sannan ya katse cikin rashin jindadi aka gyara mata jikinta…
Abida dake faman fadin ai wallahi indai baku cire mugunta ba to nasara ma yanzu kuka fara gani ku dubi mutane da suka cika gidan sai kace bikin yarinyar shugaban kasa..
Mamee ce cikin kuka tace wato sai an daura auren nan wayoo ….
Abida ce tace ai daman idan kun kita wasu zasu sota…
Barister ramlat gida taje ta yini mumy sai tausar ta takeyi gashi har andaura aure yau jumma’a akan sadaki dubu dari da hamsin, hankalin ta bai tashi ba sai dataga part din yaamin yafi nata kaya nan dady yace anjima zaa zuba mata sabbi karta damu Amma kina ganin barstr kin san bata cikin hankalin ta sai kuka….
Bayan ansakko daga sallar jumma’a yasmin tasaka wani hadaddan les dinta tasaka head pink sannan tasa sarka pink jakarta da takalmin ta kuma farari kasancewa yusra ta iya kwalliya nan ta rangada mata mashaa Allah maganar kyau ma ba’ayi mamace tace auta kece??