DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

NA NANA DISO

http://deejarhberver.wordpress.com

© HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Alhaji Rabiu ba fulatanin mutum da yazo daga garin bande zuwa garin Adbas ya k’anzo garin domin k’awo dabbobi cikin hukuncin Allah tun yana zuwa sau biyu a wata har kasuwancin sa ya habaka ubangidan sa yace zai dinga yimasa zaman kanti anan ne yabar kiwon da yakeyi..

Cikin shekaru shima Allah ya buda masa sai yasamu daukaka takai baya bada kaya sai dila dila, sanadiyar matansa biyu a lokacin hajjo da asabe kowaccen su tanada yara bibbiyu acikin yaran hajjo akwai kawu maikal da suwaiba, ita kuma asabe tanada haruna da isa kowannen su yafi shekara 20 a lokacin mahaifin su rabiu yana bala’in jidasu har takai mutane suna musu kirari da ‘ya’yan gata. sanadiyar garin sakoto dayaje daurin aure sai Allah yasa yaga hajiya sadiya har Allah yasa suka dai daita akayi aure yakawota cikin gidansa, Nan ne fa mata biyu suka addabeta har abun yafara isar ta.

Lokacin da ta samu cikin baffa tundaga lokacin Alhaji rabiu yake mata hidima abun yana bawa maikal da haruna haushi har takai suka bayyana bayan lokuta ta haihu bata kuma dade ba Allah yayimata rasuwa tabar baffa a hannun su asabe babu irin azabar da baisha ba mahaifinsu kuma yana sansu bayan wasu shekaru kowannen su akayi masa aure, bayan shekaru sai aka shirya tafiya zuwa wata kasar inda maikal da iyayen nasu gaba daya suka rasu… tunda lokacin haruna da isa suka kwashe gadon suka barwa baffa dan wani part ita kuma suwaiba suka bata dubu 50…

Hajiya suwaiba itace babbar ‘ya agidan tayi auren fari sai Allah yayiwa mijin rasuwa daga nan sai tadawo gidansu tare da d’anta sageer yasha fama kalakala amma haruna ya daukeshi lokacin da tayi aure,ta kan cewa baffa kadaina damuwa da lamarin yan’uwan domin su sunyi asara…

Haruna bayan sageer dayake roko akwai yarsa mace abida da maryam sukenan Allah yabashi amma sai mugunta da zalunci atattare dasu ga kuma borin kudi yadda kasan babansu ke bugawa…

Isa kuma yanada yara 3 akwai bilal akwai jafar sai kuma kubra,duk cikin yaransa yana sangarta bilal shine sanadiyar lallacewar shi baya ganin kowa da mutunci sai bin mata da kashe kudi…

Baffa kuwa yanada yara biyu Aisha itace tafarko tun tana karama hajiya suwaiba ta dauketa ta tafi daita benin acan ma ta aurar da’ita, sai yasmin daga nan matarsa bata kara haihuwa ba…

Baffa yasha wahala kala kala arayuwarsa bama lokacin dayace sai yayi karatu dan kudin da yake samu a makaranta da hidimar iyalai yake tafiya, yan uwansa haruna da isa ko kallon arzuki basa yimasa kuma Allah daya bashi yasmin babu ruwanta ba kamar yaransu ba abun yakan basu haushi wataran ko kudin zuwa wajen gadi bashi dashi, watarana suna zaune da mama yake cewa wai ace ni mai kwalin masters amma gadi nakeyi sai yasa kuka…
Yasmin sau ta kalleshi tace baffa Ai lamarin na Allah ne inshaa Allahu wataran sai kazama wani kamar yadda yan uwanka suka zama wasu…

Yakanyi dariya yace Yarinyar kirki Allah yasa, mama tace ameen…

Yasmin yarinya ce fara amma irin siraran nan, ga kuma hanci kina ganinta kinga jik’ar ba fulatani, Babu ruwanta tun tana karama kawayen ke ce mata ‘yar aljanna saboda hakurinta, lokacin da take aji biyu a islamiyya kwata kwata bata gane karatu hakan ya kansata kullun cikin kuka har mama ta gane sai tafara tambayar lafiya?? Ta sanar daita halin da take ciku daga nan tace ba kuka zakiyi ba addua zaki dingayi nima zan tayaki inshaa Allahu zaki fara fahimta, “Allah to yasa kamar wasa tana zuwa makaranta tana addua cikin shekaru 2 sai gashi tafara karbar kyauttuka, su abida maryam kuwa da kubra sai ma tsanarta da suka karayi haka ta dinga rayuwa cikin kuncin rayuwa. A kwai lokacin da bata da ikon zaman gate anayi mata karatu sai kiga bilal yazo ya zaneta ita kuma aduniya ta tsani bilal saboda zaluncin sa,Dr sageer kuwa irin hidimar da yakeyi masu takanyi masa Addua sosai duk da karancin shekarunta amma bata sakewa da kowa, tana kallon yaran gidan za’aja su amota amma ita sai dai akafa,tana makatantar gamnati amma su sunayin ta rabin million kullum burin su su zageta dalilin haka mahaifinta yace zai kaita boarding ko tasamu ta huta, Mahaifiyarta taso ya barta ta cigaba Amma ina yaki hakan nasa zuciyarta k’una…

Cigaban labari…

Dr sageer ke faman juyi akan kujerar sa ta office babu abunda ke damunsa irin tafiyar yasmin kai yanzu ba zanga kyakyawar fuskarta ba kullum ga lafazunta mai sanyaya zuciya, har khalifa ya zauna akusa da mashi amma bai kulaba…

” Haba doctor wannan tunani ince dai lafiya???

” Jiyowa yayi yace ina kuwa lafiya? Baffa ya kai yasmin makaranta…

” To a gaskiya dr zangaya maka gaskiya ka ajiye maganar yasmin a agefe kafara zancen bikin ka…

” Hmmm daman ai na lura kafi son ramlat, to bari ingaya maka yasmin tsoka tace babu ta inda zamu rabu ni inaso ka binciko min boarding din da suka tafi…

” ai nasanta ko yabzu sai na rakaka sai dai nisanta…

” yanzu kayi magana mutumi na ina godiya ran sunday maje…

Yasmin dake aji azaune tana karatu kamar daga sama taji anyi mata sallama tana daga kanta taga wata yarinya ce da bata huce suyi shekaru daya ba cikin murmushu ta amsa mata sallamar…

” sunana yusra nima last week nazo skull dinnan kuma naga babu ruwanki ga son karatu ko zamu zama kawaye?

Murmushi tayi tace ni yasmin sunana, ina kuma fata zamuyi kawanci nagari??

” inshaaAllah daga nan suka kullah kawance…

Mumy ce tafito zata tafi office tace dota?

” Tace yes mum har kinshirya?..

” Eh ramlat idan dr yazo kya gaishe shi..

” ohh mum bakyason dr sageer dina wallahi….

” haba my barister ni kuwa nake son sa…

” rungume mumy tayi tace har naji dadi lurv u momma…

Yau sunday kowa acikin makarantar ana kawo musu visiting kowacce tana shigowa da abubuwa amma yasmin tana gefe bata cewa komai, alokacin dr yazo yana zuwa yace yar aljanna kamar daga sama ta ruga ta rungumesa tace yaya??

” Dr sageer ne yaji dadi yadda tayi murna da zuwansa cikin murna yace yakike kanwata?kina dai karatun ko??

” inayi sosai wallhi ga mama da baffa?

” Suna gaida ke! Yasmin yasmin?

‘Naam ?? ” kinsan ina sonki ko?

” eh tace..” to kada ki kula kowa kinji da niyar soyayya kinga yanzu karatu kikeyi…

” Tohm bazan kulaba, nagode da zuwanka lokaci yayi..

” sawa yayi aka shigo masa da abubuwa da yakawo masu yawa sannan yace duk nakine..

” Nagode Allah yabiyaka sai anjima..

” har tayi nisa yace yasmin??.

“Naam..

Kikula da kanki kinji?

” Tohm tace sannan aka shigar mata da kayan..

Tundaga nan ya huce gidansu barister ramlat cikin fara’arsa yashiga palour tana zaune tayi bala’in kyau, yanayin saĺlama ta miki…

” to bakin munafuki bakin dan iska yaudarata dakakeyi to Allah ya rufamin asiri murabu tu daga yau…

” haba ramlat me yayi zafi haka??

” dan iska mai bin mata fitar min agida…

” kifa mata mari yayi see this stupid kika kara jifana da zafaffan kalaman ki wallhi sai na hukunta ki, kuma daga yau babu ni abu ke sannan yafita rai abaci……

Cikin kuru ruwan kuka ta nunashi daga nan kuma tafara nashiga uku inason ka sagee….

Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment…

Let me know what you think about this page…Ku gayan ra’ayoyin ku…

i request you to avoid spelling and grammar error….#TEAM DS

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button