DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

   ” Wallahi narasa irin ramlat tarasa kawar da zaau dinga mu’amala sai rabia shiyasa in ramlat tayi wani abun nake tunanin sata akai zata kashe min yarinya….

    ” najiba ce ta kada kai tace abunda kawaye sukeyi kenan su kashe maka aure su aure mijin naka, kuma su saka ayawon duniya, ai duk mai hankali yasan kawa ba abar anemi shawarar ta bace…

   ” Wallahi kam bani wayar tata boyeta zanyi..

     ” Ai dr sageer sai son barka wallahi ba’acewa komai saboda namiji ne mai kokari…

     ” mumy tace shine ai suje mata bakin cikin su rabata dashi…

Anty barira ce taja hannun yasmin tayi cikin daki da’ita ke zo kikaebi tawa tsarabar…

     ” Turo baki tayi tace nifa tsarabobin nan sun ‘isheni gaskiya…

     ” Dariya anty barira tayi tace ke tawa ta dabance shanye wannan zallar aya da dabino ne da zuma ki shanye duka roba biyun..

   ” dakyar ta’iya shanyi wa sannan tace wash cikina fa yacika…

    ” karbi wannan kazar da nonon nan kishanye ma…” dakyar ta karasa sannan tace yau kinsa nayi over ci…

    ” Zakiji ajikin ki ai da kanki zaki nemi ne…Anty aisha ce ta shigo tana cewa haba anty barira ‘yan ubanci zaa nunamin ne ansata a dak’a ana gyara mu anshanya mu…

    ” Haba aisha jiya zuwa yau nawa kikasha…

      ” hahaha ai ni nafeson wanda zai burkice in muka hadu….

      ” Toh uwar magana kyalemu nayiwa ‘yata wa’azi ke yasmin ki saurari ni kijini shi namiji ke zaki gyarashi duk kazantar sa zaki gyara abunki, Amma fa sai kina gyarawa kema duk wani lungu da sako na jikin ki ki tabbatar kina dirjeshi da sabulo, warin baki kada ki sake kice zaki zauna dashi ki dau makilin kiwanke hakoranki, duk yadda kika kai da son jiki kada ki bare gashin hammata dana mara su tarar miki su sukesa warin jiki ki aski kina ta ammali da turari in mijinki yaji wari ajikin ki to kin kade, kishiyar ki ‘yar gayu ce kema sai ki dage da gayu, kuma kada kice zaki zauna da faso ki wanke kafarki ke kada ki zauna lebenki ya bushe dinga shafa ko basilin ne kuma girki kikara dagewa kada kisake mijinki ya dawo ki barshi da yunwa kinji…

    ” Inshaa Allahu Anty barira zan kokarta inshaa Allahu…

   ” Yauwa ‘yar gidana Allah yasa Albarka a auren naku…

    Karfe 7 da rabi nadare yasmin tafito sanyi da gown dinta red and white tayi masifar kyau ga kwalliyar zamani ta dauki fuskarta jambakin ta ma abun A kallane ga jikinta yajik’o da tsumi jitakeyi kamar tana jik’ewa, Dr ta sageer da yasha farar shaddar sa mai adon ja tayi masa kyau koya ya murmusa sai kiga hushiryar sa ta bayyana kallon ta yatsaya yi kai mashaa Allah matata ta takaina…

    ” Mota tashiga sanadiyar babu kowa aciki su yusra basu karasa fitowa ba yace yasmin cikin jin kunya takasa kallonsa…

     ” Gaskiya kinyi bala’in kyau mashaa Allah… ” da karamin bakin ta da yaaha jambaki tace nagode..

    “Jiya yi gabadaya jikin sa ya mutu yasmin please ki goge janbakin ki wallahi kina sakani cikin wani hali ga wata muguwar sha’awa, yana daga cikin abunda ke tayar min da hankali especially innaga ansa kuma ana magana kingA kada acikin mutane nayi abun kunya ko??

    ” Murmushi tayi sannan ta dakko tushu ajakarta za goge..

    ” Basai kin wahalar da kanki ba yasa bakin sa yafara kissing dinta tas sai da ya goge…wani numfashi yasmin ta sake jikinta har wani yar yar yakeyi..

    ” Turo baki tayi tace to ai duk ka kwashe….” kibarshi haka yafi kyau daga nan suka huce gurin dinner kai ramlat ma tayi bala’in kyau har inda suke taje ta rungumesu aka dau hoto ya’ilahi tace saboda kawai kokartawa takeyi amma zuciyarta kamar ta buga intaga yana yiwa yasmin magana, baau tashi ba sai 12 dinner tayi kyau sosai….

   Washe gari tun karfi biyu akayi kamu da yamma baffa yayi mata waazi bayan karfi 6 mutocin kai amarya sunzo mama tace yasmin kije kuyi sallama da mamee mana dasu maryam ….” tohm mama tana shiga mamee ta dinga jawo mata bala’i kala kala amma bata kulasu ba nan tayi wanka sannan tashirya daga nan aka dau motoci sai gidan yasmin….

   Barister ramlat ke zaune duk abun duniya ya isheta sai jitayi ance ke kin isa nakiraki kiyi blocking dina…

    ” Ramlat ce tace banza wayake ta waya ina cikin bala’in nan narasa inda zansa kaina…

    ” Karki damu aminiyas shiyasa na tako nabaki shawara wacce zaki hanasa kusantar ta koma suyi soyayyar yau ki ruguza musu farin cikin su yadda kema yayi miki…

   ” Ramlat ce tace barister rabi’a wacce shawara ce wannan???

    ” Hmmm bayan kowa yatafi ki fito tsakiyar palour kisa kara sannan ki fasa kwalba ki caka ahannun ki yadda jikin zaita zuba…

    ” Yauwa rabia wannan ce kam mafita dannasan inyaga jinin hankalin sa zai tashi sosai…

    ” eh mana bari ni natafi sauri nakeyi…tohm sai kinjini…

   ” Dariya brstr rabia tasaka ahanya tace ni ai ban taba ganin jakar mace irin ramlat ba komai dauka takeyi hahaha ai sai nakashe auren nan kuma na aure doctor namijin mazaje…

    Bangaren yasmin badai kyau ba duk irin gudar da akeyi duk ramlat tanaji sai karfe 1 sannan doctor ya shigo yana shigowa ya fara shiga dakin ramlat nan sukayi sallah har da tuntuben sauri…

      ” Amarya yasmin mata ga doctoe sageer yau Allah yayarda…

      ” Murmushi tayi cike da sonsa…

    Sai kitashi muje muyi sallah ko? Sai da sukayi alwala sukayi sallah yana tayi mata addu’oi tace nifa bacci nakeji…

     ” to ai yanzu sai kijirani ko ya watsa ruwa ita kuma ta riga ta kwanta bacci har yana kokarin surarta can taji mutum abakin ta dakyar yakarasa adduar ma cikin kidemewa yafara shafata yana kokarin rabata da riga sai kuwa wani mahaukacin ihu sukaji….

      ” da sauro ya fito yasmin kuma mayafi kawai tasaka…

    ” ramlat da ‘idonta yayi faman ja tafasa kwalbar sai caccakawa takeyi ahannun ta….da gudu dr sageer yazo ina yana kokarin kwacewa har ta suma….

     ” Yasmin kuwa cikin gigicewa tace anya lafiyar ta kalou da daddaren nan zata…

    ” dakko min jakun kunana yasmi i sauri ramlat ramlat daki yayi da’ita sai da ya gyara gurin sannan ya saka mata robar ruwa ya kwantar da’ita ya lullubeta ….

     ” yasmin da macce ki ibarta doctor yace jiki kwanta yasmin…

     ” Tunda ta samu bacci ai sai ka taso kaima…

    ” Sai kace mara imani kina ganin ta suma taza’ayi natafi na barta ko farfadowa batayi ba?

      ” Tsaya wa tayi tana kallonsa can tace ince ita tajawowa kanta ai naga…

     ” to kitafi ni anan zan kwana kije ki kwanta ke daya, danyan ciki ne fa da’ita…

    ” Yasmin ce tace Allah yabata lafiya sannan ta huce dak’inta tabbas ramlat ba karamar makira bace ba..  Amma indai akan mijina ne muzuba mugani…

    ” Ramlat dake kokarin bude idonta tace mijina mijina ina sonka please…

     ” Gani akusa dake ramlat me isa zakiyiwa kanki haka nifa nakine har abada …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button