DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

     ” kanta tasaka kan cinyarsa sannan tace karka tafi kabarni tsoro nakeji…

     ” karki damu anan zan kwanna kusa dake…

     ” Murmushi tayi sannan tace to karufe kofar kazo ka kwanta…

     ” tohm yace mata sannan yayi yadda takeso cikin jin zafin hannun ta tace banzan nayi ba…

    ” Haba my sweety kwanta kiyi baccib ki kinji ni nakine har abada….

      ” Murmushin mugunta tayi sannan tace acikin zuciyar ta ai yasmin bakiga komai ba ma…

     Yasmin dake faman zubda hawaye da kyar bacci ya kwashe ta…

Assalamu alaikum

   Gaisuwa gareku masoya ina godiya da addu’oi Allah yabar kauna…

Ya kukaji shafin nan??

    Menene ra’ayin ku dangane da shafin nan??

Anya zaman yasmin da ramlat zaiyi dadi kuwa zaman doya da manja??

    
  Please do vote comments and like..your comment give me more courage to continue writing my story…and it helps me to write better…#TEAM…DS….DSLOVER’S

Nana Aisha RA tace: Na tambayi Manzon Allah SAW -game da wannan ãyar-:
(( Da wad’anda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu )).

Shin shi ne wanda yake sãta yake zina yake shan giya? Sai yace:
(( A’a, Mutumin da yake azumi yake sallah kuma yake sadaka, amma yana jin tsoro kada – Allah SWT- yaqi kar’bar aikin da yayi )).

Sã’ilin nan bãwa yaji tsoron tãlãlar da Allah SWT ke yi masa, a duk lõkacin da bãwa yaga alãmun dãcewa da nutsuwar zuciya, to, kada ya rud’i kansa da hakan, A’a abin da ake so ya qãra dãgewa wajen biyayyar Allah SWT.

Domin shi shaid’an yana iya ‘batar da bãwa ta kõwace hanya, idan muna aikin alheri sai ya zo mana ta ‘bangaren da nuna mana cewa ai mu wasu na musamman ne a gurin Allah SWT.

Abin da ya wajaba ga mumini shi ne jin tsoron zunuban da ke aikatãwa, komai qanqantarsu, in kuma shaid’an ya rinjãye shi sai ayi saurin tuba zuwa ga Allah SWT.

Kada bãwa ya rud’u da yawan aikin alherinsa; don wani laifin guda d’aya zai iya sanya rushewar ayyukan bãwa a tsawon shekarunsa har ya kai kansa cikin wad’anda Allah SWT yake cewa:

(( Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra ! ))….

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com   

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:25 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 65-67

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

   Yasmin tun karfe 6 na safe ta farka jitayi gabadaya jikinta yana ciwo ga wani ciwon mara dake da wainiya da ita cikin salati da zikiri tatashi wanka tashiga tana fitowa ta saka wani material dinta da akayi mata riga da siket rigarta irin mai buda d’an saman nan wato rabin kafada awaje, kayan sunyi carasras ajikinta kwanciya tayi tana karewa da’kin kallo yayi bala’in kyau can kuma tafara lalubar wayar ta tanata kiran mama bata dauka ba sai takira yusra tace ta kaiwa mama wayar..

    ” salamu alaiki auta kuntashi lafiya?  ” lafiya lou mama wallahi nayi missing dinki… ” mamace tayi dariya tace nima haka yasmin yauwa alhaji madu yabaki atampha shabiyar da mayafai baffa kuma ya siyo miki dogayen riguna guda 5 na dauke daya…

     ” A’a mama kikara daya, su anty barira sukuma sai abasu atamphar kowa daya mayafin kuma abawa su mamee…

    ” To yusra fa?  ” Akwai takalmi da jaka acikin akwatin ki da sarka da wani less sai abata dauran kawayen nawa kuma akwai turare da man shafawa suma sai ki rarraba musu…

    ” Tohm shikenan Allah yayimiki albarka yabaku zaman lafiya, yasmin banason fitina da tsokana kinji ko kizauna kiyiwa mijinki biyayya…

     ” Inshaa Allahu mamata zanyi yadda kikace…

   Sunayin sallama sai ga muryar su anty barira,sumayya,yusra,da abida da saurin ta tatashi tafito palour tana sai yanzu kukazo haba karfe fa 9?

    ” Dariya suka sa au karfe shida kikeso muzo…” eh mana yagajiyar ku?

     ” Ai tabi lafiya…Toh mashaa Allah nan suka dinga hira can yasmin tace ya abida ina maryam?

      ” hmm wannan sarakan bakin cikin ai bazata iya zuwa ba…” kai anty abida bakin cikin lafiya ke dai kawai dan bakwa shirine…

    ” Yasmin kenan sai dai ki boye gaskiya Amma kinsan dai halinsu…

    Sumayya ce tace ga abinci nan da taliya da macroni da pepper chicken da fried rice sai lemo zobo dana kankana…

    ” sannunku Amma kun kyauta wallahi sosai wayar tace tayi ringing tana dauka dr sageer yace zo…

    ” tashi tayi tace ina zuwa kukunna kallo sama ta hau tana hawa taga wasu kujeru masu kyau ga wani daki da bandaki ga setroom da toilet sai kuma wani dak’in daban wanda ya tabbatar mata acikin dak’in yake sallama tayi sannan ta durkusa har kasa ta gaishe shi…

     ” kallom ta kawai yakeyi kayan sun kama ko’ina najikinta gaskiya Allah yayiwa yasmin halitta zama tayi bakin gado tace yajikin nata??

     ” Ai taji dadi yanzu dakko min kaya mara nauyi…  ” Tohm tace sannan tace fita zakayi ne??  ” Eh inada aikin da zanyiwa wasu mata har su biyu karfe 11…

     ” Allah yabasu lafiya…” Ameen yace sannan ta taimaka masa yasaka rigarta tasa masa takalmi sannan ta samasa hula…

    ” gaskiya kayi kyau my dr karfa wata ta kyasamin kai…” Dariya yayi yace ai ni nakine nahar abada kinyi kyau yasmin kayan nan sun karbi jikinki…

     ” Kara juyawa tayi tana wani fari tace danAllah fa… ” Allah kuwa bari na tashi natafi…

   ” katsaya nazuba maka abinci mama takawo…

     ” aa basai ma naci ba nasha shayi a office…

     ” Haba my dr ya za’ayi kafita baka ci komai ba ni wallahi bazan yarda ba salan adingayi da mijina…

    ” Toh naji Amma banason abu mai nayi..

    ” Tohm ina zuwa palour tafito ta biya kitchen ta dakko plate da spoon da cup taliyar ta zuba masa sannan ta zuba lemon…

    ” yusra tace lallai dadi miji anmanta damu ma… ” Yasmin ce taci ai dole abawa mai gida hakkinsa…” dariya suka saka…

    ” zama tayi agefensa ga taliya da salad ai su basuda nauyi…” yanzu cinma ai aiki ne yasmin da kinbarni natafi…

    ” Abincin ta dauka tafara bashi abaku yanata kallonta sai data gama tace menene amfanin mu in bamu kula da kaiba???

      ” murmushi yayi tare da wani mayantaccen kallo can yace mata to mikomin lemon…. ” cikin wata irin shagwaba tace to A’a bude bakinka bashi tayi tace bari itama nazuba mata sannan nakai mata…

     ” Yauwa my sweetheart gaskiya kayannan sunyi kyau this your jambaki i love it yakai bakinga kusan 1mint yana kissing dinta sannan ya saketa wani iri taji ajikinta ta sunkuyar da kanta…” rungumeta yayi yana dariya sannan yaja hancin ta yace inasonki yasmin, zuciya da raina duk kin sace…

   Wata kunyarsa taji tatashi zata fita yariko ta jiyowa tayi yana kallonta itama kallonsa takeyi..” kece muradina in babu ke ba lafiya bazan rabu dake ba, farin ciki zan samarki sannan kara sumbatar bakinta ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button