DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

      ” Karfa ka makara… ” Toh muje ki rakani sakkowa sukayi abun sha’awa Su yusra suka gaishe shi yana amsawa yashiga part din ramlat kwance take ko wanka batayi ba wani urin bugawa zuciyar ramlat tayi dataga yadda yasmin take tayi kyau sosai ga diri ga kuma kyau yasmin ce tace yajikin naki??

    ” Dakyar tace da sauki.. ” zama yayi kusa da ramlat yace ni zanfita kina bukatar wani abun??..
   
    ” cikin kissa tace ni kai nake bukata..” murmushi yayi yace in badole ba ai bazan fita na barku ba…

    ” Toh bari nima narakaka… ” yasmin cikin tata kissar tace haba ke da baki da lafiya kiyi hutawarki na rakasa…

    ” Dr sageer ne yace aikuwa kinga kina bukatar hutawa sannan ya sunbaci goshinta ya tashi…

    ” yasmin ce ta riki masa hannu zuciyar ramlat kamar ta buga amma takasa cewa komai har zuka fita sai da yasmin ta rakashi har kofar motarsa sannan tace Allah yatsaremin kai yabaka nasara a abunda zakayi…

     ” Dariya yayi yace kyakyawa Allah ya mallaka mini ke, ki daina kunyata please! Ki kular min da kanki…

    ” Karka manta da adduar fita daga gida karkuma kamanta da bismillah a kowanne abu zaka fara…bye bye…

    Tohm inshaa Allahu yashiga cikin mota mai gadi ya bude mata gate..

Tana komawa cikin gida yusra tace sannu dadi miji kin barmu anan?

   ” Anty barira ce tace ina kishiyar taki mugaisa?

    ” hmm ai jiya da daddare ta caccakawa hannunta kwalba tana daki tana fama da zazzabi…

    ” abida ce tace mata wasu ai mahaukata ne wallahi basu da cikakkin hankali yanzu ai kanta tayi wa, kutashi muje sai mu dubata…

    ” yasmin ce tace Allah dai yasawake sumayya ku tafar mata da taliyar nan da miyar…

    ” Basu minti biyar ba suka dawo anty barira tace ohh ahaka kyace mutuniyar kirki ce suka sa dariya haka suka dinga hira basu tafi ba sai 6 na yamma yasmin tagama sallah kenan ta dauki ledar dasuka kawo mata nan taga mama har da always ta hado mata ga dubu 5 acikin leda cikin murmushi ta dauka daga nan fa marar ta tadan dinga juyawa har sai da jinin yafara zuba wanka taje tayi sannan tasaka pad din tana fitowa ta shirya cikin kananan kaya riga da siketa tayi kyau sannan tajira masa abincin a dinning table ba’afi minti biyu da zamanta ba sai gashi ya shigo zama yayi yana mai da idonsa kanta cikin gigita yace sweetheart zo muga kwalliya tashi tayi taje kusa dashi tace sannu da dawowa ya akai??

    ” Lafiya lou yaron ne balafiya gashi dr nafiu yace sai gobe zai shigo garin… ” wayyo Allah yabashi lafiya to katashi kaci abinci sai kayi wanka ko??

    ” dining din yazauna sannan ta zuba masa kallon ta yayi yace nagaji sosai da sosai..” bari nabaka to sai dasuka gama sannan yayi wanka yana kallon mudubi gaba daya jikinsa ya mutu dayaga always can yace yasmin bakyajin dadi ne?

    ” eh wallahi amma ai na warware mara tace dama, Shiru yayi baice komai ba irin feeling din dayaji baisan yaya zaiyi dashi ba fita yayi dakin ramlat..

    ” Yasmin tayi saurin dauke ragowar always din tasaka a durowa sai bayan karfi goma yashigo yana ta mata wasu dan wasanni sai wayarsa ta fara ringing yana dauka ramlat tace itafa tsoro takeji ga kuma ciwon kai…

    ” yasmin bari naje nadawo…

    ” yana zuwa ramlat tasa kuka ita bazata iya kwana ita kadai ba sai dai su kwana tare yarasa yarda zaiyi da’ita yakira yasmin awaya yace jikin ramlat ne ba lafiya ki kwanta sai da safe…

    ” Maganar tayi mata takaici aranta Amma tace toh Allah yakara sauki…

    ” Ramlat kuma tafara zancen zuci ai sai kinsan kin aure mijina sai na rabaki dashi ta karfi dayaji…

Assalamu alaikum BARAKALLAHU FIYKUM!!!
    
  Please do vote comments and like..your comment give me more courage to continue writing my story…and it helps me to write better…#TEAM…DS….DSLOVER’S

Ya zo a hadisin da Abdullahi d’an Abbas RA yace: Wata rana Manzon Allah SAW yã gõya/d’auke ne -a bãyan abar hawa- sai yace:…

(( Yã kai wannan yãron ! Tabbas zan sanar da kai wasu kalmõmi, ka kiyãye/biyayya ga Ubangiji, sai Ubangiji ya kikyãye/kãre ka, ka kiyãye/biyayya ga Ubangiji za ka sãme Shi daura da kai…

…Idan za kayi rõqo/tambaya/neman abu; to, ka rõqi Ubangiji, idan kuma za ka nemi taimako; to, ka nemi taimakon Ubangiji…

…Kuma ka sani, dã ace dukkan al’umma za ta had’u bisa ga su amfãnar da kai; ba za su amfã ne ka ba, sai da abin da Allah SWT ya rigã da ya rubuta/qaddara a gare ka…

…Kuma da za su had’u bisa su cutar da kai; ba za su iya cutar da kai ba, fãce da abin da Allah SWT ya rigã da ya qaddara a kanka…

…An rigã da an d’auke alqaluma -na Malã’iku- kuma takardun sun bushe )).
Imãm Ahmad & At-trimizy.

Wato ana son bãwa ya kula da duk wani abu da Allah SWT ya umurce shi da aikatãwa, da kuma nesantar duk abin da ya hana, idan bãwa yayi hakan; to, Allah SWT zai kãre bãwansa ya shiryar da shi ya ninka masa lãdan ayyukan da yayi, sa’an nan ya sauwaqqe masa al’amura.

Urs Nana diso

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com   

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 8:25 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 67-70

DOCTOR
        SAGEER

NA NANA DISO

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

   Yasmin cike da bakin ciki da damuwa tatashi wanka tayi sannan ta saka wasu fitinannun doguwar rigar ya kama jikinta sosai da sosai wayar ta ta dauka tana karanta azkar…

   ” Dr sageer ne yashigo fuskar sa cike da murmushi sweetheart har kin tashi??

    ” Tsugunnawa tayi har kasa tace ina kwana.. ” wani dadi yaji tare da janta zuwa k’an gado kinyi bala’in kyau my wifey nagode wa Allah da ya mallaka min ke…

    ” Murmushi tayi wanda bai ji ranta ba tace yajikin ramlat??

    ” Dr sageer ne yace kinsan abunki da mai ciki yau laulayi gobe lafiya jikin nata dai da sauki kam…

   ” To tahada breakfast din? ” No ke zaki hada ai bazata iya ita tace dole sai ana tausaya mata ana kuma tararrayar ta..

   ” Cikin mamaki ta kalleshi sannan tace toh mikewar da zatayi yabita da kallo ko’ina ajikin kadawa yakeyi atake yaji wata muguwar sha’awar ta ta kamashi cikin ransa yace Allah kataimaki ne yasmin yau tagama period dinta, yanzu ramlat bata gamsar dani yadda yakamata…

   Sai karfe 9 sannan yasmin tagama komai tajira a dinning din babban palour shiga tayi part din ramlat tana kwance kan kujira tace kifito muyi breakfast…

    ” Nifa banason munafurci haba shigeyar yarinya sai nacin tsiya kin wani mannewa doctor haba to bari kiji sai nasa kin karbi takardar sakinki da hannun ki kuma munafurci da bakin ciki bakima fara gani ba sai kiyi ready….

   ” Murmushi yasmin tayi tace ai mai abin fada baya fada sai tabar gurin tana fita ta tarar dashi azaune kamar ita yaje jira ita wannan kallon da yake mata shine bata so…

   ” dr sageer ne yace yanaji ku shiru ramlat dake karasowa tana turo ciki…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button