DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

Kika kara yiwa mijinki Addu a samun sauki sau kema mun hallakaki…
” cikin kidimewa tafara karatun Alkur’ani aguje ta sakko kasa mama mama sune sune zasu kashe shi wallahi sune…
Baffa ne ya riki hannun ta ta zaunar da ita kusa dashi yana tofa mata addua kuka kawai takeyi…
” Nan aka sanar ramlat ta haihu yarinya mace amma sanadiyar wasu magunguna da ramlat ke faman sha yarinyar babu lafiya ita walau tayi rai walau ta rayuwa…
” cikin ihu yasmin takara jin muryar dazu saura ke muntaba yarinyar kishiyar ki kuma mijinki bazai arzuki ba ba zai same matsayi ba hahaha….
” ihu takara sakawa tace sune sune sune…
” mama ce ta su wanene…
“Zatayi magana aikuwa sai ta sume…
” mama ce tasaka kuka wallahi duk wanda ya illatar dasu Allah bazai barsu ba…
Ki kwantar da hankalin ki cewar baffa bari nafara samo ganyen magarya…
Ramlat dake faman kuka ance yarinya ba lafiya miji ba lafiya mumy ce tace kidaina kuka komai zaizo karshe kinji…
” Dazu fa muka rabu dashi …
Ai daman hukuncin Allah babu yadda bayayi…
Su hajiya da Aisha sai bayan magariba suka tawo tare da wani babban malamin kur’ani malamin ruqya…
Suna shiga yasmin ta zabure tafara ihu tana kafita nace ko kazo abanza bazamu fita ba…
Mama ce ta riketa bayan yasa anyi mata alwala sannan yazauna mintuna talatin yana karatun Alkur’ani yasmin tanata ihu shima a firgice ta mike dr sageer ya watsa musu wani ruwa sai maganganu zamu fita zamu fita ka daina zamu fita…
” malamin yace me kukazo yi a jikinsu?
” wallahi zamu fita turo mu akayi akace mu hanashi tafiya da magana saboda za’a bashi babban mukami a America jibi…
” Ita kuma matarsa mu muka saka tayi bari muna samun shiga jikinta idan bata sallah kuma muna shiga jikinta idan tana sauraron kida…
” wanene ya turo ku??
” munyi alkawari bazamu fada ba… ” yanzu zan konaku yafara karanta surorin azaba sai suka fara haruna ne da isa da nazifi da Abokinsa auwal sune zamu cire ajiyar mu a kafarsa daman yasmin tafi karfin mu tana azkar sai bata cikin ibada muke samun shiga amma Zamu barsu mun ma dauke ajiyar da mukayi wa jaririyar..
” Malamin sai yacigaba da karatu sai sukace muncire a ajiyar mu kuma zamu fita wallhi mutanen kirki ne kuma su dage da addua dan mutanen da suka turo mu basuda imani su dinga azkar da zama da alwala da zama da dankwali ko sunzo bazasuyi nasara ba kuma su dinga sauraron suratul bakara acikin gidan su Aljanu bazasu zo ba…..
” Wannan bayanin dakuka gama kashe ku zanyi saboda agaba zaku iya shiga jikin wasu ai kuwa yaja wasu surori minti talatin sai yasmin tace dr…
” Dr sageer kuwa baice komai ba sai salati da yayi…
Hajiyar sageer ce take kuka tana tabbas zamani yazo da yan uwanka zasu cutar da kai, sageeru inshaaAllahu sai Allah yayi maka albarka kuma zai tsareka sharrin magauta….
” Hajiya yaushe kikazo yayi wannan fara’ar tasa mai bayyana wushiryar sa….
Malamin ne yace yakamata kuji tsoron Allah ku daina wasa da ita ko dan samun tsira ballanta na yanzu makiya sunyi yawa ka dinga karatun Alkur’ani akankai da yawan salati ke kuma ki guji wasa da sallah kidinga sauraron Alkur’ani da kuma yawan zama da alwala kuma kirage jin waka kidinga zama da dankwali kinji…
” yasmin ce tace inshaaAllahu…
Baffa ne yace ku dage da az’kar na safe da yamma..
Nan akayi asubuti gurin ramlat ….
Yasmin ce tace ina zakaje mijina?
” gurin baby na mana…
” To katsaya kaci abinci kayi sallah sai muje tare…
” Tohm yace yayi wanka ta dakko masa shadda tasaka masa turare sannan tace oya kaci abinci sai kayi sallah mu tafi binta yake da kallo kawai Allah yabashi mace tagari sai 9 sannan suka tafi asubuti dr sageer ne ya dauki yarinyar sannan yayi mata kiran sallah yayi mata huduba yace ai da ke take kama…
” yasmin ce tace aikam dai Allah yaraya mana ita..
” mumy ce tace to ni zan tafi su hajiya har sun tafi fa…
” ramlat ce tace nidai dr zanbi mutafi gida sai abu tazauna agurina…
” Mumy ce tace tunda Allah yabata lafiya kuma sun sallameku ai Alhmdlh sai ayi gida ko…
Yau kwana biyar da haihu dr sai nan nan yake dasu duk wasu aikin gida yasmin keyi ita da baki har abinci ma yau da anty aisha tazo ta kawo mata wani maganin mata tunda tasha duk wata kasala da Sha’awa ta rufeta bayan tayi sallar isha’i tasaka wata bodyhug ta kamata ko ina na jikinta ya bayyana cikin siyasa ta nufi dak’insa…
” cikin kissa tace au aiki kakeyi ko kace nazo na tayaka zama tayi kusa dashi sannan ta sumbaci bakinsa…
Cikin kankanin lokaci idonsa yayi ja kallonta yayi yace ina mutukar ji dake yau dinnan sai nasamar da baby inshaa Allahu..kara narke masa tayi ajiki tace nidai kayimin a hankali…
” yasmin idan ina tare dake ina shiga halin sha’awa da kauna hankali yakan gushe danAllah kisoni ni yadda nake sonki…
” cikin murmushi tace bari kaga tafara kissing dinsa daga nan suka fada birnin soyayya….
Bayan sunyi wanka suka sauka gurin mai jego dr sageer yana kusa da’ita ke ‘yan bakwai zaki haifa min…
” ramlat tace dan daya ma ina mutum yacika ramlat tace daman ke ba lallai kiyi juriya ba…
” yasmin tace ai naga lokacin juriyar ki kina ta ihu suka saka dariya…
” Dr sageer ne yace jibi zanje karin matsayi dawa zamu tafi…
” yasmin tayi saurin cewa da ramlat zaka itace uwar gida..
” Ramlat tayi shiru to ai aini jego nakeyi kuje dai…
” kunga sai da safe da ke zai tafi ni banson zuwa fa..
” binta yayi har daki yace au dama bakyason a yasmin su kike nadinga sha’awar wasu matan?
” murmushi tayi tace kafata kafar mijina…
Assalamu alaikum
Kuyi hakuri da rashin rubutuwa akan lokaci..!!!
*_Sak’onin ku suna isa garine wannan shafin sadaukar GAREKU MUTANEN GIRKI..
Please do vote comments and like ????
Urs Nana diso
Email:kabba43@yahoo. com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:19 PM] +234 703 475 7034: 80-85
DOCTOR
SAGEER
NA NANA DISO
http://nanadisoo.blogspot.com
© HASKE WRITER’S ASSOCIATION
Murmushi tayi tace kafata kafar mijina…
Kallon ta yayi yace sai da safe sai kifara shiri ko??
My dear inason zuwa gidan mama kaga babu nisa damu..
No! Kibari idan mundawo sai kije ina tunanin zaifi…
DanAllah mijina kataimaka wallahi nayi missing ummata please..
Kinga babu inda zakije yafita tare da rufe kofar bai tsaya ko’ina ba sai dak’in ramlat tana zaune tana ta kallon boy dinsu…
” cikin mamaki tace ya naganka anan??
“Nifa bazan iya nisa da baby naba nagayamiki bani shi…
” murmushin mugunta tayi tabbas tasamu wani makaman kuntatawa yasmin…
” Sunan sa muhammad, bayan mundawo daga tafiyar tun 3 days zamuyi sai ayi sunan zanmiki transfer duk abunda kike bukata sai ayi ko??
” kwanciya ramlat tayi ak’an kafadarsa inbanda murna babu abunda takeyi ina alfahari dakai mijina ina mutukar sonka wallahi akanka zan iya komai..
” Ramlat kenan nima ina mutukar sonki sosai..
Yasmin da takaici ya isheta kuka tasaka sai gurin 2 sannan bacci ya dauketa da safe bayan ta hada breakfast tashirya cikin wani material goduwar riga ya kamata tayi rolling sannan tasa janbaki…
” ramlat ce tafara cewa irin wannan kwalliya ina zakije??