DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

     Matsowa tayi ta karbi boy tace yarona sannan ta sumbace shi..

    Juyawa tayi tace ina kwana yaya??

      ” sai da yadan jima sannan yace lafiya lou..

     ” yadda ya amsa mata ita kanta bataji dadi ba ramlat kuwa sai faraa takeyi…

     ” yasmin kuwa tahada komai na breakfast sannan ta zauna..

    ” ramlat tace yaushe zakije gidan su mama ne??

       ” Yau zanje inshaa Allahu..

     ” Ki gaishe su in kinje please..” dr sageer dake danna waya yajiyo yace babu inda zakije fa..

     ” wani malolo ne yatsaya mata a wuya cikin takaici tace Tohm…

       Tashi tayi zata hau sama..” dr ne yayi saurin kiran sunanta sai tajiyo zo ki zauna ina zakije??

     ” Bacci nakeji idonta cike da hawaye zo to kikwanta kusa dani..

     ” Shiru tayi bataci komai ba..” ramlat tace karfe nawa jirgin zai tashi ne??

   ” karfe biyu yanzu karfe 12 ai…

     ” To bari naje nayi wanka nima…

       ” Yasmin da takasa magana tashi tayi itama dak’inta tashiga wayar ta ta dauka ta kirawo hajiya tana kuka…

    ” Lafiya yasmin lafiya??

  ” Hajiya yaya sageer yahanani zuwa inga su baffa tunda suka tare banje ba babu magiyar da banyi masa ba yaki, kuma ni banason nabishi kasar wajen nan danAllah kiyi masa magana sannan tasaka kuka…

    ” Daina kuka tagurina inshaaAllahu zan kirasa kuma kwana 2 ma zakiyi agidan…” goge hawayenta yasmin tayi tace hajiya nagode sosai…

Yasmin na zaune akan gado taje dr sageer yaturo kofa yace mata au baki shirya ba??

    ” Tace ina zanje?? ” Au Tambayata kikeyi? Wato yasmin ban isa nasaka ki abu ba ki bazanji dadinki ba kenan? Da ramlat ce nace tashirya datuni tashirya ko so kikeyi indinga neman mata?? Kinsan yanayi na…

    ” kuka tasaka ta fara ciro kayanta sai kuma wayar hajiya ta shigo cikin murna ta kallisa dataji yana gaidata…

     ” Ko amsawa batayi ba takamashi da fada kuma kabarta taje ta gaida iyayenta taje tayi kwana biyu in zakadawo sai ta dawo… ” doctor bashir da ransa ya bace yace hajiya amm… ” Umarni na baka ta kashe wayar…

    ” Kallon yasmin yayi idonsa duk yayi jaa yace kishirya kije kiga su umma..

     ” Cikin fara’a tace kwana nawa zanyi???

     ” Duk yadda yayi miki… “har da dantsallen ta nagode my habiby…

     ” Tsako yajaaa sannan yafita shiryawa yayi sannan ya rungume ramlat yace inasonki uwargida na kiyimin addu’a kinji…

     ” Ramlat cikin mamaki tace ina yasmin din?? ” No ni kadai zantafi sai nadawo 3days kawai zanyi tunda babaa tananan to sai ku zauna ita yasmin zataje gurin baffah..

   ” Ramlat ce take kokarin yin kuka ni kadai?? … ” DanAllah Ramlat kada kisani cikib tunani pls..” tohm Allah yatsaremin kai yadawo dakai lafiya…

    ” Yasmin kuwa sai ibar kaya takeyi ta dauki kusan kala 7 sannan ta rufe koina ta sakko bata tarar da kowa a palour din ba abunda yabata haushi ko sallama dr sageer baiyi mata ba tana isa gida ta rungume mama lallai baba ya zuba dukiya agidan nan mashaaAllah..

    ” Yasmin yanaganki da akwati??

     ” sati daya zanyi mama …” haba auta sati daya yayi yawa kwana biyu dai…

    ” Toh mama nan tashiga dakunan..

  
  Mamee ce tace yanzu Alhaji babu wani boka dakasani ma aiki kamar yankan wuka???

     ” Alhaji isa ne yace to inma akwai bokan ina kudin aikin…

       ” Khalil ne yace DanAllah mutuba mudaina abunda mukeyi tun ina yaro kuke illatar da baffa Amma kullum gaba yakeyi…Dr sageer kunyi masa asiri kan kar yasamu karin girma gashinan asirin ya karye kukallah ya kunna musu wayarsa yadda turawan America suka girmamashi tare da kyaututuka…

     ” Basu gigice ba sai dasukaji uban kudin da suka bashi tare da motoci..

   Alhaji haruna ne yayi cilli da wayar tare dacewa wallahi sai munga bayansa bazaiyi kudi ba…

    ” inna ce tace kudi na nawa kuma ku dai da zuciyar ku ta mutu kai kuma isa Allah ya’isa tsakanina da kai khalil katashi mutafi ka koma makaranta kayi noma agarenmu idan kasamu mata sai kayi auren ka Ai yanzu kaji jiki kakuma gane sharri dan aike ne ko karufe kofa sai ka bude masa…

   ” Khalil ne yace tabbas hakane inna zan biki kukuma Allah yaganar daku…

    ” Mamee tace to waya rikiko?? “Ku tafi mana kunga Alhaji isa asaida gidan dasuka tashi sai akaiwa boka ko???

    ” Alhaji isa yace gaskiya kin kawo shawara mai kyau sai Haruna ya samo dillalai…

  
    Bayan Angama karrama Dr sageer da karamasa girma wani hotel suka kaishi yana kokarin cire safa wata baturiya tashigo tasaka wasu shaidanun kaya bakinta dauke da red lipstick tana bude kofa tace…excuse me please Dr sageer…

    Dagowa yayi da kansa yace …hope fine??
      ” she smile and say am happy for your success…

    ” he reply to her by saying thanking…

       ” am juliet am here to help you sleep well..

      ” I don’t understand…

” she just smile and started to remove his shoes…

     ” cikin gigicewa yace thank you please i appreciate…

   ” she smile again and say okay let me bath you please….

     ” Dr sageer shout and said i don’t need any it please u can work out…

     ” she reply to him by saying do u need some kiss???

     ” cikin zafin nama yace getout…

     ” cikin tsoro tafita innalilahi kawai yake ambata da’irin shigar datayi…

   Wayansa ya dakko yafara neman lambar yasmin har zai buga yakatse..yakirawo ramlat sukafara video call…

    ” Mashaa Allah dr na yazama tauraron taurari Alhamdulilahi naji dadi..

      ” nagode matata kinyi wankan tsarki??

     ” No kofa sati baayi da haihuwar ba banyi ba meke damunka??

    ” Hawaye ne ke zuba a idonsa tare da fadin kinsan matsalata kinsani ai…

     ” Cikin rashin jindadi tace shiyasa nace ka tafi da yasmin ai…  ” yasmin batasona bata kaunata ba nine agabanta ba…

     ” Shiru tayi tace ai jibi zaka tawo dear kayi azumi mana…

    ” Tohm nagode kikularmin da kanki da muhammad kinji…

    ” Tohm tace tare da fadin ilove u so much… sannan ta kashe..

    ” Hoton yasmin yafara kallo yana hucewa cikin jindadi yace Allah ne yasamin sonki… wasu magunguna ya hadiya sannan yayi sallah yayi bacci…

  Fadila ce tashigo gurin mama ta zauna tanata dariya mama yau baki nemi ne ba…

    ” yasmin ce tace sannu..

   ” mama tace fadila ga yarinyar tawa laa itace yasmin din kice kinzo mana..

   ” mama ce tace yasmin wannan yarinyar kanwata ce hadiza kinganeta kusa damu take kullum tana tayani aiki da zama…

    ” Murmushi yasmin tayi hankalin ta duk yana kan dr sageer bai kirata ba har ynzu…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button