DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

Mama ai kallo natsaya yi ingayamiki wani matashin mutum america ta karrama kinga yadda kawaye na suketa ihu dama zai aure su gaskiya yayi bawan Allah kinsan ya sunansa??
Mama tayi dariya tace dr sageer ko??? ” fadila ce tasaka dariya tace ashe kema kinkala..
” D’a nane ai , shine mijin yasmin…
” yasmin wani kishinsa taji , ” fadila tace wallahi ki rikeshi hannu bibbiyu don baki yadda yanmmata ke sonsa ba…
” shiru tayi tashiga daki duk sai taji ta tsane gidan ma tabbas miji wani niima ne daga Allah wayanta dauka ta dinga kiranshi amma bai dauka ba message babu wanda bata turaba bai kulata ba..
Washegari ana karyawa baffa yace gobe mijinki zai dawo misalin 6 na yamma sai ki tafe gida da wuri koh?
” sauri tayi tace inshaa Allahu baffa…
” baffa yace kunyi waya ko??
” Cikin sauri tace eh munyi azuciyar ta kuma kuka take kokarin yi…wayan mama ta dauka ta shiga wani room takirawo shi bugu daya ya dauka yace mamata ina yini??
” kuka tasaka tace yaya nicefa danAllah kayi hakuri wallhi nayi kuskure.. ” sauri yayi yakatse wayar sannan yace yasmin bazaki illatamin rayuwata ba sannan yafita…
Washegari da safe tasa fadila ta nemo mata mai kunshi da kitso sannan tasa aka siyo mata kwakwa tayi lemo dayawa sannan tayi white rice da farfesu tayi hadin salad duk tasa aka kaimata gida ita gurin 5 ta shirya tsaf mama tace kiji tsoron Allah yasmin kije tsoron Allah kikula da dr kiyimasa biyayya danAllah…
Tohm mama inshaaAllahu…” Allah yayimiki albarka..” Ameen!!!
Yasmin nakarasawa cikin gidan taga ramlat tanata video call da dr harda su kiss cikin kishi tace sallamata nakeyi…
” ramlat tace ina nan muna soyewa da mijina banjiki ba sannunki da zuwa…
Tsaki tayi tahau sama ta bude dak’inta turaren wuta tasaka sannan ta gyara dakinsa tayi waka wata riga da siket tasaka duk saman kirjinta abude siket din duk yadameta dankwali ta daura tanajin shigowarsa ta rungumesa tureta yayi ahankali sannan yace ina muhammad gobe suna inshaa Allahu…
Ramlat ya sumbata ta mika masa yaron yasmin kuwa duk jikinta yayi sanyi dakyar tace sannu da zuwa ya hanya??
Banza yayi mata ya kalle ramlat sunata hira..
Yasmin da batasan lok’acin da kuka yacita ba tatashi ta hau sama kallonta kawai yakeyi dr duk jikinsa ya mutu, kuka tayi sosai sannan tayi sallar isha’i tafesa turare ta nufi dak’insa tana shiga taga yana kwanci cikinsa nata ciyo sa juye yakeyi a tsoraci tace lafiya yaya tasaka kuka…
Maganin da yake nunawa ta dakko tabashi…kuka tasaka tace DANALLAH kayi hakuri wallhi nayi kuskure DanAllah kada kayi fushi dani zanshiga wani hali…
Bakyasona ko? zan iya shiga mugun hali yasmin bakya kaunata? Zan sakike sai ki aure wanda kikeso… sai ya sume..
” A furgice ta mike tana A’a A’a A’a yaya ina sonka ina sonka Tasa wani mahaukacin ihu ai kuwa sai tawadi aguje ramlat tashigo….
Assalamu alaikum
Kuyi hakuri da rashin rubutuwa akan lokaci..!!!
*_Sak’onin ku suna isa garine wannan shafin sadaukar GAREKU MUTANEN GIRKI..
Please do vote comments and like ????
Urs Nana diso
Email:kabba43@yahoo. com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:19 PM] +234 703 475 7034: 85-90
DOCTOR
SAGEER
NA NANA DISO
http://deejarhberver.wordpress.com
© HASKE WRITER’S ASSOCIATION
A furgice ta mike tana A’a A’a A’a yaya ina sonka ina sonka Tasa wani mahaukacin ihu ai kuwa sai tawadi aguje ramlat tashigo….
Hank’alin Ramlat bai tashi ba sai dataga doctor sageer baya motse kwata kwata batasan lokacin da ta ajiye muhammad ba tana kuka takirawo dr khalifa dakyar ya dauka yace matar dr ya’akayi??
” kuka tasaka tace mijina ya mutu, wallahi yasmin ce wayoo ka taimakeni danAllah…
” Kashe wayar yayi yajuya kan motarsa sai gidan dr sageer yana shiga ya hau sama hankalin sa bai tashi ba sai dayaga yasmin akwance bai bi takan dr sageer ba yafara dubata…
” Dr khalifa yazaka biyewa wannan mahaukaciyar yarinyar batason shi bata kaunar shi, itace sanadin komai tasa kuka…
” dakata ramlat karya kikeyi wallahu yasmin bazatayi haka ba da dai kece kowa yasan zaki aikata haka, bazaki fadi kyakyawar kalma ba haba sai kace ba musulma ba…
” Ai daman nasan haka zakace yayi mata banza ya dudduba yasmin nan yasa ramlat ta kwantar da’ita wata allura yayi mata sannan yayi hanyar fita..
” Dr mijina fa dr kataimaka, mijinki nan da minti biyar ma zai watsake matsalar sa mai sauki ce wallahi kuji tsoron hakkin yasmin kuji tsoron hakkin ta yarinya karama ace jininta yana hawa…
” Ramlat ce tajaa tsaki ta mutu mana sai me sai me kuma ai nasanar dasu mama duk abunda takeyi..
” Bai saurareta ba yatafi…
Mama ke faman sintiri apalour tana innalillahi..
” fadila tace haba mama wallahi yasmin bazatayi haka ba sharrin kishiya ce wallahi bazatayi ba, to kinkirawo ta kinji ta bakinta???
” Mama cikin fada tace ai tasan tayi laifi bazata dauka ba…
” DanAllah mama kidaina fadin haka please…
” Wani numfashi mama tajaa sannan ta goge hawayenta so kikeyi ace ninake zugata idan ta kashe musu yaro fa…
” Makiyi ai duk abunda bayaso babu sharrin da bazaiyi ba kiyi hakuri danAllah…
Tunda doctor sageer ya tashi idonsa yayi jajir wanka yayi ramlat sai sannu takeyi masa…
” Kallon yasmin dake kwance yayu yace wannan fa??
” ina tunanin bacci takeyi, tsaki yajaa sannan yace yunwa nakeji sosai cikin murmushi tace katashi muje kaci abinci..
” murmushi yayi yace ina babyna??
” yana gurin iya bari nakarbo shi suna hira yace abinci sannan ya zauna kallo nan ramlat da matsa kusa dashi tana ta bashi labarin budirin da za’ayi gobe yanata dariya…
” wasa yake tayi da muhammad yace ita bazata tashi ba kenan???
” ramlat ce tace uhm kaikama damu da wanda bai damu dakai ba..
” Shiru yayi baice komai ba..
Yasmin dake kokarin bude idonta hawaye ne yabiyo bayan budewa tashi tayi zaune tace tabbas da namiji hankaka ne gabansa fari bayansa baki, yaya baya sona baya kaunata gashi yace zai sakeni yanzu in yasakeni ina zanje mama bazara barni na zauna gurinta ba hajiya kuma yaronta ne tasaka kuka mai cikin da kuna, A hankali tace inshaa Allahu bazan sake cewa komai ba daga gaisuwa sai kuma in yace nayi wani abun… hannun ta tazata daga taji alamar alura zafi taji nan taje dakinta tayi wanka sannan ta zauna ga yunwa da takeji…
Hijjabi tasaka har kasa sannan ta sakko daga benen tana kallon su sunta hira ramlat rungume da muhammad dining ta duba taga shinkafa jallop haka ta zuba ta zauna taci, wata kasala taji sannan tace sai da safenku…
” Ramlat tasa dariya tace yauwa…
” yasmin tana shiga dakinta tace tabbas dr baya kaunata baya sona har yaushe mukayi auren yafara wulakanta ni wayoo Allah na tasaka kuka mai cike da kunci tare da fadin tabbas wannan shine KUNCIN RAYUW ramlat bata kyauta ba tunda tasaka SON ZUCIYA acikin aikinta wayarta tadakko number mama tagani kusan kira 20 cikin tashin hankali ta bi kiran to ko ya sakeni naga bai kalleni ba shikenan nashiga uku takara saka kuka ….