DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

Alhaji haruna ne ke cikin dokar daji yanata wasu abubuwa har ya’isa bayan wani dutse yana zuwa boka yace nasani nasani ka ajiye dubu hamsin zamu gama maka dasu..
” Murmushi alhaji haruna yayi yace ga dubu hamsin nan muna godiya boka..
” tashi katafi zamuyi hahahaha…
” yana tafiya boka yace ai ku matsalar ku kenan kada wani yafiku bansan komai ba yasa dariya yau dilu zataci kaji inba da harkar karyarba babu mai bani dubu hamsin haha yashige gida…
Alhaji haruna tunda yakarasa gida yake fadin ai kawai sai dai kuji labarin mutuwar baffa da sageeru…
” mamee ce tayi guda tace damun zama masu arzuki…
” Alhaji isa dake faman washe baki yace ai bokan yafa’iya aiki sosai karku damu..
Yau kwana 5 kenan tsakanin yasmin da dr sai kallo tun tana sakkowa taci abincin har ta daina takama azumi tabbas mai samun kulawar miji dan gatane don ranar suna ma sai da momy tace tazo ayi hoto da ita sannan ta dan sakko…
” Hankalin dr sageer baitashi akan yasmin ba sai dayaga bata bude ko kofarta tabbas yasan bai kyauta ba amma kuma haka shine daidai kodan ya hukuntata kuma irin kalaman da ramlat take gaya masa yasmin tace abun nabasa tsoro…
“Bayan sallar isha’i yasmin na zaune akan sallaya takara kiran wayar mama dakyar ta dauka tace lafiya kiketa kirana mara kunya???
” Mama kitsaya ki saurari ne wallahi banyi komai ba Allah inason yaya Allah mama inasonsa shine…
” dakata shine me kice kullum cikin kuntata masa har dacewa ramlat wai tace abaki takardar sake to baffa zangayawa wallahi wallahi kika kaso aurenki sai dai wata uwar bani ba haka kika inayi eh…
” Nashiga uku nashiga uku wallahi mama ban fada ba yaza’ayi nace haka wallahi…
” ki cigaba da duk abunda kikaga shine daidai kuma kika kashe sageer kema kashiki zaayi…
” ummata ke kike fadin haka ke dakikafi kowa sanin halina tasa kuka…
” yasmin ta da nasani ba yasmin ta yanzu ba mara jin magana takashe wayar…
” Wani abune ya tokari mata awuya sai hawaye dake zuba a idonta ahankali ta kwanta soyayyar su da dr sageer kawai take tunawa to ita kuwa me tayi masa haka yatsaneta bakomai ji tayi tana son cin indomie…
” Doctor sageer ke faman kallon hotunan yasmin can yace ramlat yasmin ta sakko yau???
” Ta sakko tabani sako ingayamaka wai in kanada zuciya ka saketa tunda ku ba dangin mayu bani…
” Kallonta yayi da mamaki ita tagayamiki haka…
” hmmm ai yafi haka kadan nagayamaka…
” Baice komai ba yacigaba da aikinsa a system..
” Cikin hijjabi har kasa yasmin ta sakko bataci komai ba ta huce kitchen indomie tayi da shayi tahadu indomie din taji vegetable palour ta zauna tabbas duk dr sageer ya rami ta lura kallon plate dinta kawai yakeyi ramlat tace bari na dakko muhammad…
” Dr sageer yace kidaina barinsa shi kadai…
Tashi yasmin tayi zata tafi sama ramlat tace ina zakije?? Ai baki ci ba…
” in kinaso ke kicinye bana sha’awar su yanzu..
” Dr sageer ne ya cinye har da tea din cikin ransa sai son yasmin kara bugar ransa yakeyi ba shiri yaja mota yaje yasiyo mata gashashiyar kaza da yogurt da yadawo duk sun kwanta sama yayi direct dakin yasmin yana shiga yaga ta rufe kofar da mukulli babban mukulli ya dakko ya bude yashiga ta cikin bargo ta dugungune kallonta kawai yake yana me nayi miki bakyasona yasmin? Idan na rabu dake zanshiga mugun hali hannunta ya riki alokacin duk tanajin abunda yake cewa amma tayi luf sai hawaye…
” cikin kakkausar murya yace yasmin yasmin yasmin tayi masa banza…
Hannunsa yasa abargon yana kokarin shafata tayi saurin tashi tana kuka banaso kabari..
” To tashi kici kaza gashi nasiyo miki…
” banaci banaci tasaka kuka..
Cikin murya mai sanyi yace haba kanwata danAllah kici ko kadanni banson kina kwana da yunwa wallahi dazu baki koshi da indomie ba kinyi hakan ne don kinsan banci abinci ba yasmin ni fa ina sonki wallahi wallahi amma kuma kalaman dakike gayawa ramlat kullum tagayamin suna batamin rai jiya harda ce mata ni asalin mu mayu ne?
” hawaye takeyi kawai tabbas me ramlat take shirya mata dole wasan yazo karshe…
” karbi kici danAllah..” karba tayi tanaci tana hawaye idonta duk sun kunbura…
” yasmin dita ba haka take ba mai son mijin tace ga kula dashi ga jin maganarsa Amma bansan wa yacanja minke ba dubi yadda kika saka kanki kuka…
” tana gamaci ta sha ruwa ta koma zata kwanta yace aa yanzu fa kikaci abinci haba my sweetheart..
” kuka tasaka ni kakyaleni, kwanciya yayi ya rungumota tashi tayi tace kaje ka rungume wacce kakeso baniba…
” to ai ke nakeso kenake kauna…
” Kaje ka hadani da mama ta daina kulani kullum sai fada takemin batasona tasaka kuka..
” haba yasmin yaya zanyi nahadaki da mama haba yasmin kema kinsani bazan taba ba…
” To waya gayamata inba kaiba tasa kuka.. wayarsa ya dakko yasa handsfree mamata ina yini…
” Sageeru lafiya lou danAllah kayi hakuri da halin yasmin ramlat kullum sai tagayamin abunda tayi kuma yanzu tafara fuskantar fushina..
” mama ba dai yasmin ditaba wallahi batayi min komai inbanda kuka ni bana batamin kuma bata taba gayamin maganganu na bacin rai ba…
” mamace tayi diriss tabbass fadila tayi gaskiya datace sharrin wanda bayason ne…Mama ce tace to harnaji dadi duk dahaka zanmata fada…
” DanAllah mama kudaina biyewa maganar mutane ni yasmin batayimin komai sai soyayya da kulawa ina son matata har abada…
Toh agabana sai anjima…
” kinji dai da bakinki ko kinji abunda tace yaya zaayi inkai karar ki?? Kinsan kuwa yadda nake sonki? Zan gwada miki son danake miki kinsan duk sirrina ina mutukar sonki nasan nayi kuskure sosai da sosai Amma danAllah kiyi hakuri yana kokarin durkusawa tajuya kanta yasmin bataci komai ba tashi yayi yakashe fitila alwala tayi tayi sallah tare da adduar Allah yabarta da mijinta kuma sai ta nunawa ramlat ita karamar makirace…
” Da safe wayarta tayi ringing bataga suna ajikin number ba ta dauka tare da yin sallama…
” fadila ce yasmin nasan kina cikin damuwa wallahi bakowace silaba face kishiyar ki ita ke hadamiki wannan gwaramar tasha kiran mama tace kinci Wallahi kitashi ki kwaci mijinki kada ta kashe miki aure nasan ke ba yarinya bace…
” Murmushi tayi tace inshaa Allahu nagode fadila…
Bayan ta sauka ta hada breakfast kwalliya tace wasu mini skirt tasa tare da wata riga mai kamar vest gaba daya kirjinta awaje dankwali tasaka sannan ta sakko ramlat nazaune tana karyawa tunda taganta tasaki baki dr yana shigowa yasmin taje ta rungumeshi tana wata irin shagwaba cikin wani salo tace nayi missing din kissing dinka..
” Kallonta kawai yakeyi tare da wani narkakken sonta ga wata kasala tafara kissing dinsa…
” Ramlat ce cikin takaici tace kinada hankali kuwa…
” yasmin ce tasa kuka ta nuna masa sanan kirjinta tace kaekayi yaya kasosamin ” cikin rawar murya yace to yafara sosawa nan da nan yashiga wani yaniyi sannan taja hannunsa tace kaxo muje ka karya…
Binta kawai yake da kallo ramlat dake faman zagin yasmin ko takanta batayi ba…
” ramlat tace dr ga muhammad cikin wata kasallaliyar murya yace yasmin nake bukata…
” Ahankali yasmin ta kara sumbatar bakin shi sannan tace ga tea nan ni nayi sama tana hawa ya biyo ta yana shigowa tare da magiya tace dakata yaya dakata kada kasake ka tabani …
” kuka yake kokarin yi yasmin please please ..tsaki taja ta bar dakin…