DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

Wani salati yasaka tare da ambaton sunan Allah baisan lokacin da bacci ya kwashe shi ba…

” yasmin tana palour dinta tana dariya tace yanzu muka fara wasan da kai har ita sai kunji abunda naji…

Ramlat dake zagaye tace lallai yasmin wani asirin tayo tayaya zan bullo mata ko nakira rabia??

Yasmin ce tace ramlatu ramlatu…

” wannan wani iskanci ne yasmin.

” yasmin ce tace iskanciin dakika iya ne..

” lallai bakida kunya yarinyar nan wallahi sai na wanke ki da mari…

” ai ke naganki da kunyar inji yasmin kuma inkin isa mari ni wallahi sai nayi miki biyar banza katuwar wofi uwargida ko uwar hauka kuma muzuma mugani abunda kikayimin yanzu zaki kwasa…

” jikin ramlat ne yayi sanyi ta dake tace ai gwarane yanasona wata ma yasota…

” yasmin tasa dariya tare da fadin see u..wai so to kizuba ido kiga kauna sai na haukatashi da sona…

Wani irin zama ramlat tayi tare da ajiyar zuciya…

Ai yanzu kikafara ajiyar zuciya…

Assalamu alaikum

how was the page??

*_Sak’onin ku suna isa garine wannan shafin sadaukar GAREKU MUTANEN GIRKI..

Please do vote comments and like ????

Urs Nana diso

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:19 PM] ‪+234 703 475 7034‬: 90-95

  DOCTOR
           SAGEER

NA NANA DISO

https://www.youtube.com/channel/UCvopCYalw1ooSYq-rMhjm5g

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

    Ai yanzu kikafara ajiyar zuciya, cewar yasmin..

     Dakin kasa tashiga nan tayi kallo sai gurin 9 taji bacci yana kokarin dauketa babu shiri ta mik’e zata hau sama ramlat tace wai har yanzu   bai tashi ba??

     ” Wata harara yasmin tayi mata tace auke jiransa kikeyi??

      ” eh mana naga mijina ne kuma adakina yake kwana yaronsa ma bazai iya bacci ba sai dashi…

     ” mtseww sai kiyita zama aiki ne ya sameki sai da safe yasmin tana shiga dakinta tayi mamaki dataga har yanzu bacci yakeyi wanka tashiga bayan tafito tana goge jikinta da towel sai kawai taga ya farka…

    ” Dr sageer yana bude idonsa yayi karo da yasmin tafito daga bandaki cikin yanayin damuwa ya tashi yana kokarin zama…

     ” cikin kissa ta karaso gurinsa tace sannu da tashi honey, ko nahada maka ruwan wanka??

     ” Cikin murmushin sa da ya bayyana wushiryar sa yace da k’in kyauta kuwa…

    ” Tashi tayi tahada masa, kallonta kawai yakeyi sai da ta busa masa ido sannan yafahimci tana magana, cikin kashe ido tace wannan kallo haka yaya sai kace baka saba ganina ba…

    ” Dariya yayi yace ai naga kinkara kyau ne..

     ” Murmushi tayi mai cike da shagwaba tace nagode mijina nakaina oya ta riki hannunsa katashi kayi wanka to…

     ” Nifa inkinaso nayi wanka sai dai kiyimin…

     ” To tashi muje yana shiga tace to bari nazo sai ta rufe kofa…

     ” Cikin dariya tace idan na rabu dakai yaya bansan yaya zanyi rayuwa ba, kayan bacci tasaka ta kunna turaren wuta….

    “Dr sageer ne ya fito yana fitowa yace matata, dariya yasmin tayi tace mijina..

     ” bari nasaka kaya sai mu kwanta ko??

    ” Sai dai da safe…” Shiru yayi yafita yana saka wasu riga marasa nauyi yafito yana shiga yaga ta rufe kofar mukulli yasaka ya bude yace yasmin wai me nayi miki ne kike guduna…

     ” Shiru tayi sannan ta kara lulluba yana kokarin jan bargon yaji wayarsa tafara ringing hello yasmin?

    ” yasmin kuma haba sageer wannan wani irin abune wallahi baka adalci ni bazan iya kwana baka nan ba Allah kuwa…

     ” To yanzu mekikeso nayi miki naga kunyi vacci??

     ” muhammad sai kuka yakeyi missing din dad dinsa kawai yakeyi…

     ” Toh ganinan, yana kashe wayar sai yafara kokarin mikewa..

    ” yasmin ce tayi sauri ta rungumesa Sai tasa kuka…

    ” Kara rungumeta yayi daman abunda yakeso kenan sannan yace my wifey ya akayi menene na kuka??

     ” Tafiya fa zakayi ka barni kuma kasan nafi kowa bukatarka..

     ” Ai kinsan kema bazan iya tafiya ba…

    ” Turo baki tayi tace har fa..kafin takarasa yasa bakinsa a nata kusan 3mint duk ya rudi yace please yasmin nayi sau daya please my lovely wife please DanAllah…

      ” Aa gaskiya wallahi ni babu abunda zakayi zazzabi nakeyi tayi murmushin mugunta inkuma gurin ramlat zaka tafi sai katashi katafi…

    ” Rungumeta yakarayi yace ai ko hug din dakika van zanji sa’ida…

   Ramlat data gaji da jiranshi Lallai yasmin wallahi sai naci uban ta…

    Tun safiyar yau mamee ke sintiri tana jiran Alhaji haruna shigowa yayi yace ga turaren da boka yabayar yace musaka acikin gidan su ita yasmin zaasaketa dan haka sai ku shirya har maryam mutafi…

     ” Hahaha mamee tasaka dariya yauwa bari na shirya gaskiya idan yasmin bata fito daga gidan mijinta ba zan iya hauka yarinya sai jindadi takeyi ba mamaki ma kuga tayi ciki…

    Ai wallahi da sai an zubar wallahi inji Alhaji haruna..

    Yasmin tana palour sai dariya takeyi suna waya da yusrah, ramlat ce tace ke asalin matsiyata dangin talauci…

    ” yasmin ce cikin masifa tace ubanki ne talakan banza jahila ke naga kina tutiya da wannan gidan to ni mai gidan nakeso ba wannan dukiyar tashi ba ki zauna kiyi biyayya bawai hada masifa da munafurci ba…

    ” kutmar ni kike gayawa wannan wallahi sai kinsan kingayamin karaman dabba kawai…

    ” yasmin ce wayarta tafara ringing cikin sauri ta dauka sannan ta zauna kiss tafara aika masa darling ya office nayi missing dika wallahi….

   ” Murmushi yayi yace nima da kyar nakeyin aikin tunaninki duk ya addabeni wallahi in banda kin matsamin nafita zama zanyi ina kallon ki…

    ” mijina kenan baka rabo da barkwanci…

    ” yauwa anjima su mamee zasuzo kishirya musu wani abun..

    ” Tohm in kaga gwanda kasiyomin please…

      ” Anya banyi ajiya ba kuwa??

    ” hahaha adakin wa?

” Acikin ki mana…? ” cikin kunya ta kashe wayar ta kalli ramlat tace lafiya kika tsayamin aka??

” Tsaki tayi ta shiga palour dinta nan da nan yasmin tashiga kitchen tunani tayi menene abu mai sauki dazata sarrafa musu?

   Can tace bari nayi musu CP DRINK’S , abarba ta dakko ta yankata sai ta dakko cocumber ita ta yanka guda biyu sai ta zuba su acikin blender tasa ruwa ta markada ta tace sannan ta juyeshi acikin jug tasa sugar directly fridge ta sakashi..

    Bari to Na hada musu da cake alokacin ramlat tashigo wai me kikeyi ne??

    ” Abunda kika sakani atake ta dakko kwai guda huda ta zubo flour cokalin cin abinci goma, ta dakko flavour dinta vanillah essences ta ta ebo sugar cokalin cin abinci 6 sai butter dinta simas ta zuba cokali 4 sai baking powder dinta ta gwangwani…

     ” Ramlat dake ta saki saki acikin ranta tabbas yasmin indai gurin girki ne ta’iya yadda na dade inasom koyan cake bari nayi shiru na koya…

    ” Atake yasmin ta dauki karamar muciya ta zuba butter da sugar a dan bowl kusan minti 5 tanata juyasu har suka fara canjawa sai tafasa kwai ta jujjuya sannan tasaka flour da flavour 1table spoon da baking powder 1tea spoon ta jujjuyasu har sai da suka hade jikin su sannan ta dakko papers na cupcake ta zuzzuba aciki ta kunna abun gashinta ta kunna wutar sama da kasa ta jajjirasu…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button