DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

     Yana fita tatashi tayi wanka jikinta kamar tamutu dan gajiya kwanciya tayi bacci yana kokarin surar ta taji yana kara tabata tace DanAllah yaya kar na mutu kataimaka…” Yanzu please kadan ki taimaka yasmin i really miss u… ” Da safe saboda tsabar gajiya kasakomai tayi ranar babu yadda ba’ayi dashi ba yace shi ba babu inda zaije bashida mara lafiya…

      ” ramlat ce ta hada breakfast yasmin tanayiwa muh’d wasa dr yace saura naki twins din… ” hmm tace batace komai ba ta salallaba tayi sama bacci ke damunta dama bayan tayi nisa yazo ya kunna mata ac sannan ya kwantar da ita a kirjinsa shima ahaka baccin ya koshi sa…

    Ramlat ke zaune tana kallo taji sallama muryar rabia taje..

      ” Me kikazo yimun agida??  ” ke dallah sabon boka nasamu wannan kizuba wa kishiyarki zakiga aiki da cikawa..

       ” Babbar jahila asararriyar kawa nayi danasanin saninki rabia Allah ya’isa duk abunda kike saka ni kuma wallhi kije da Allah zai isar mini…

      ” Hahaha banza jaka cewar rabia ai sai na fitar dake daga daular nan sai kin koma yawo atiti da mota kuma sai na shigo gidannan ko kinaso ko bakyaso dan haka ki tsaya ki gani…

     ” Fitar min daga gida kuma nakara ganin kafarki wallahi sai na karyata…

      ” Zan fita Amma kema kiyi ready kin kusa fita nice fa Rabia uwar munafukai…

Assalamu alaikum

   how was the page??

YAKUKAGA SOYAYYAR DOCTOR DA YASMIN??

      *ina fata kuna daukar darasi acikin wannan littafin kunga sharrin kawa da illarta da makircin ta…

Kuna tunanin Ramlat zata shiryu baki daya?? Ya rikicinta da rabia??

  Ya zancen kuma kara auren dr..??

    NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE DIN GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN NAN UBANGIJI ALLAH YASA KUNA ANFANA DA ABUNDA YAKE CIKI NA DARASI ABUNDA BANYI DAIDAI BA ALLAH YAYAFEMIN…

INA GODIYA DA SOYAYYAR DAKUKE NUNAWA WANNAN LITTAFIN ALLAH YASAKA DA ALHERI…

    Please do vote comments and like ????

????????????????GO AND SUBSCRIBE TO THAT YOUTUBE  CHANNEL GA SHI CAN NAYI POSTING A FARKON PAGE DIN…FOR THOSE WHO WANT TO LEARN  FOOD,SNACKS AND DRINKS….????????

????????????????please click the link and subscribe  ..

   Urs Nana diso

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:20 PM] ‪+234 703 475 7034‬: 97-100

  DOCTOR
           SAGEER

NA NANA DISO

https://www.youtube.com/channel/UCvopCYalw1ooSYq-rMhjm5g

   © HASKE WRITER’S ASSOCIATION

Tun lok’acin da rabia ta fita hankalin ramlat bai kwanta ba tunanin abubuwan datayi abaya takeyi tabbas tayi nadamar haduwa da rabia bata taba tunanin MUGUWAR KAWA bace tabbas duk wanda yace zai biyewa kawaye domin suji dadi a duniya kullum basa tunamasa lahira zaiyi asara ba karama ba tabbas kawa ta rudeni datuno na kashewa kai na aure Allah na gode maka Allah ka yafemin duk abunda nayiwa Dr sageer sannan tasaka kuka, Muhammad dake jin yunwa ta dauka tabashi abincin sa sannan tashiga kitchen don hada abinci….

    ” yasmin Sai gurin 4:00 saura tatashi bata nufi ko’ina ba sai toilet wanka tayi sannan tasa kaya doguwar riga ga cikinta da yadan fito, sallah tayi sannan ta matsa kusa da dr sageer tana latsa hannunsa cikin k’ankanin lokaci yafarka bude idonsa da zaiyi yaganta akusa dashi murmushi yayi yace lokacin sallah yayi ko??

    ” Eh yayi katashi kaje masallaci kada ka makara ko??

    ” Tohm yace bai tsaya ko’ina ba sai masallaci…

   Yasmin ce tasakko taga har ramlat tajera komai a dinning samun guri tayi ta zauna tace sannu maman muhd nabarki da aiki yau dinne banajin dadi…

    ” Murmushi ramlat tayi tace ni sau nawa ina barinki da aikin ai ko kaso daya banyi ba daga cikin abunda kikayi duk kin kwashe ladan..

    ” Hmmm yasmin kawai tace bata kara cewa komai ba ramlat ce ta kunna tv shirin tambaya mabudin ilimi na aminu daurawa…

    ” Dr sageer yana dawowa daga masallaci ya zauna sunayi masa sannu da zuwa muhd ya dauka yana my boy sai wayo kakeyi Allah yayi maka albarka…

    ” yasmin ce tace Ga abinci a dinning kutashi muje muci…

    ” Suna cikin ci sai sukaji anci malam tambayata itace kullum idan na nemi matata sai tak’i sai nayi mata magiya wani zubin kuma idan na bata mata rai sai tadinga ramawa da hanani hakk’ina..
    Malam yace kamar yadda yazo a hadisi cewa duk maccen da mijinta yanemeta taki amincewa batare da tana cikin larurar da aka haramta kusantar juna wata ko  tsanin cuta ba to mala’iku zasu kwana suna tsine mata, mata kusan wannan tabbas babban kuskure ne dakuma asara dumin aljannar mijinku tana tafin kafarsa akwai hanyoyi da yawa na ramuwa amma banda wannan tunda zatajawo wa kanta tsinewar mala’iku kuma babbar asara ce wannan, tabbas rayuwar Aure sai hakuri dole in zaa zauna sai wani ya cuce wani ko wani ya kware wani ko wani ya batawa wani danhaka hakuri shine babbar ribar wannan zama dan duk wanda kuka sundade to su kadai suka san hakurin da sukayi,kuma Allah da kansa yace kuma kuyi bushara ga masu hakuri,kuma kusani Allah baya zalunci koma duk wanda aka zalunta zai saka masa kuma Allah baya yafe hakk’in wani..

   ” Yasmin dake cin abinci tayi saurin kwarewa, cikin sauri dr sageer ya mikomata ruwa sannu sannu…

    ” ramlat ma shiru tayi batace komai ba domin ada ta wahalar da dr sageer tabbas lokaci yayi dazata bashi hakuri..

      Dr sageer yafi kowa jindadin wa’azin nan don halin da yake ciki kenan cikin fara’a yace yakamata mufara tulawar al kurani ko zuwa gobe da daddare ne..

     ” Sukace toh Allah ya kaimu..

 
Alhaji haruna ne yace to wallahi kusani boka yasanar dani cewa indai basuyi amfani da turaren nan ba duk mu ukun cutar baras ko kuraje masu wari zasu samemu ina fatan kun tabbatar sunyi amfani dashi…

   ” mamee ce tace amfani na nawa ai yanzu babu mamaki yasmin tana gidanta dr kuwa balafiya…

    ” Alhaji isa yace kwarai kuwa don jiya a gabana kika kirasu awaya kuma sunji sunyi amfani dashi…

     ” Toh shikenan kar mushiga matsala shiya bamu da mai bamu magani…

    ” mamee tace matsala ai sun dade da shigar ta amma mu bazata samemu ba…

     Da safe dr ya shirya zai fita yanata sauri yasmin tace honey yace yes menene sakkowa tayi ta sumbaci bakinsa tace please zan dan lika gidan anty hauwa kanwar mama anjima kaji?

    ” Banson fita yasmin innadawo maje, Nan da nan din haba yayana please nikadai fa agida…

    ” okay tohm sai kin dawo dear ki gaisheta ki kula da kanki ..

     ” rike hannun sa tayi tace thank you ban yarda kowacce mace ta kallarmin kai ba kaji please ka kula da kanka i love u so much..

      ” murmushi yayi yafita yaja mota yasmin ta samu guri ta zauna kogin tunani tashiga abu na farko da tafara tunawa shine irin rayuwar talauci da sukayi da irin tsanar da yayan baffa suka nuna musu ashe dama baffana zai samu sana’a tayi murmushi tare da fadin tabbas mai hakuri yana tare da nasara, wani kukane ya kwace mata cikin ranta tace bantaba tunanin zanyi aure ba nasha wulakancin samari su zo su gudu ashe lokaci na ne baiyiba Allah nagode maka kaicon wanda baiyi hakuri ba, duk samarina akorar min ayimin sharri nazo nagam jamia ashe inada rabo daga karshe nazo na aure wanda ko amafarki ban taba tunanin zai soni ba Allah mai girma kayi mana afuwa Allah ka yafemana kakara mana hakuri ta shafa cikinta tana murmushi gashi baby na yakusa zuwa Allah kayi masa albarka sannan ta hau sama…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button