DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

Sai karfe hudu yasmin ta shirya zata fita tacewa ramlat ni nafita ynzu zandawo..
” Toh kawai tace mata batare da ta bata doguwar amsaba tunanin rabia kawai takeyi domin shaidancin rabia yafi karfin tunanin ta…
Yasmin batayi wata doguwar tafiya ba ta’isa gidansu fadila..anty hauwa ce tace sai yau?? Ai nayi fushi…
” gaisheta tayi sannan taga wasu matan guda biyu ta gaishesu, anty kenan mijin nawa ne bayason fita shiyasa…
” Fadila tace yasmin ya gida ya kishiyarki?? ” yasmin tayi dariya tace tana gaisheki..” ina amsawa…
” Wata ta kusa da fadila ce tace kinsan Allah anty hauwa duk zafin ran namiji da yawan fushinsa yana gani kinci kananan kaya ko’ina ajikinki ya matsu ga turare nan danan zakiga ya sakko…
” tace tabbas especially idan kikayi shigar sannan kika bashi hakuri dai kiji labari ya canza daga fada zuwa tarairaya…
” yasmin tace ai rayuwar ce komai zakayi sai dai da hakuri… ” fadila tace hakane yasmin bikina saura 3weeks fa…
” A’a Allah yakaimu bari natafi kunga har 6 takusa sukayi sallama fadila ta rakota suna tafi suna hira sai gani sukayi ansha gabansu da mota…
” Fadila ce tace haba malam da hankalin ka daka bugemu fa…
” Allah ya huce zuciyar ku yasmin nakeson yiwa magana please..
” Cikin sauri ta dago uncle jabir?? Ko cikin bacci bazata taba manta muryar nan ba…
” yasmin nine ashe kinyi aure wallahi nadadi ina nemanki nabaki hakuri wallahi ba yaudararki nayi ba ummata ce ta matsamin sai na aure fatima gatanan ku gaisa kiyi hakuri…
” Murmushi tayi mai cike da takaici dr sageer da yashigo layin yaganta tare da jabir cikin zazAfan kishi yakara jan motar yashiga cikin gida…
” yasmin tana ganin haka tace nagode bakomai sai anjima fadila nagode duk ta rudi takarasa cikin gida tana shiga palour taganshi sai jujjuya key yake tana shigowa cikin tsawa yace da uban wa kika tsaya kina yimasa dariya wanene…
” yasmin da kuka ke kokarin kwace mata tace uncle jabir ne ….
” Taina yazama uncle dinki ko muharramin ki ne yama zaayi ku gaisa for what reason??
” Wallahi bakomai yace min ba ha..
” is okay daman nasan u don’t love me she kikeso ko harda yimasa fara kina kallonsa ohh my god my wife yaza’ayi yatsaya dake for what reason baisan hukuncin aure ba??
Shiru tayi Sannan tace Allah yabaka hakuri wallahi batsaya dashi don komai ba kayi hakuri inshaa Allahu bazan kuma ba nayi kuskure sannan ta durkusa har kasa…ramlat ce duk jikinta yayi sanyi tace kayi hakuri baban muh’d…
” Wallahi yasmin bazan iya jure ganin ki da wani ba inasonki ina kaunarki too much Amma na hakura danAllah karki ki kara kinji???
Yadda yafada har cikin ranta tace too inshaa Allahu bari naje nayi sallah sannan ta hau sama kuka tasaka sai tayi mai isarta sannan ta ta saka kayan bacci tare da addua ta kwanta…
Ramlat ce tace tun dazu yasmin fa bata sakko ba ni bari naje na kwanta sai da safe…
” Allah yakaimu samn ya hau yaje yayi wanka shafa’i da witr yayi sanna ya nufi dakin yasmin gani yayi har ta kwanta bude bargon yayi shima yashiga cikin sauti kasakasa yace yasmin dita…
Naam yayasanna tasa kuka ai kaine baka yarda dani ba kawai hakuri bani wallahi babu abunda yacemin…
Dr sageer ne ya rungumeta sannan yace akanki zan shiga kowanne yanayi ke dayace na kira ki sarauniya , Nashiga yanayi lokacin da naganki dashi kiyimin uzuri kiyi hakuri,Ni nadamu dake kema ki damu dani DanAllah…
” murmushi tayi tace ina alfahari dakai mijina sannan ta sumbace sa ahaka ya rungumeta har sukayi bacci…
Da sassafe mamee tafito tana ihu tana nashiga uku na lallace kuraje kuraje innalillahi yau nashiga uku na lallace??
Alhaji haruna ne yafito da sauri yace kutmar wallahi sai dai ki barmin gida kije nasakeki saki uku….
Amma kacika shege mara mutunci azzalumi zan barmaka gida amma ban yafe maka ba…
” zatashiga daki yace Wallahi bazaki dauki komai ba bazaki shafa mana ba kitashi kitafi ya hankadata…
” Tana ihu tana kuka takama hanya..
Assalamu alaikum
BARAKALLAHU FIYKUM BAZAN KUMA DAINA GODIYA AGAREKU BA BISA SAKONNIN KU ALLAH YABIYA BUKATU NA ALHERI.._
How was the page???
I can’t stop apologized for the spelling and grammar mistake’s
Please do vote comments and like.. And I call my silent readers please do vote and comment my story really need your comment and vote#TEAM …..DS….DS LOVER’S_
Please do vote comments and like ????
????????????????GO AND SUBSCRIBE TO THAT YOUTUBE CHANNEL GA SHI CAN NAYI POSTING A FARKON PAGE DIN…FOR THOSE WHO WANT TO LEARN FOOD,SNACKS AND DRINKS….????????
????????????????please click the link and subscribe ..
Ya zo a Hadisin da aka karɓo daga Abi Huraira RA yace: Manzon Allah SAW yace: (( Mai yin zina bã zai yi zinar ba alhãli yana mumini, kuma mai yin sãta bã zai yi sãtar ba alhãli yana mumini, haka mai shan giya bã zai shã giyar ba alhãli yana mumini…))
Bukhary & Muslim
Wato duk lõkacin da bãyi za suyi waɗancan ɓarna to sai a cire imãni daga zuciyarsu a sanda suke yin ɓarnar.
Allah SWT ya haramta zina sannan kuma aka sanya uƙuba mai tsanani ga mãsu aikata zinar, kai har ma kusantar zina sai da Allah SWT ya hama kamar inda yake cewa:
(( Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã munãna ga zama hanya )).
Bisa ga haka duk wani abu da ke ita kai wa kusa da zina to haram ne kamar sumbanta da shigar banza/nuna tsaraici da bayyanar da kwalliya a fili don tãyar da sha’awa da yãɗa hoton banza da faɗar maganar da ta shãfi tãyar da sha’awa.
Wani mai hikima yana cewa: “Abu shida shi ke haifar da zina: Kallo, murmushi, sallama, zance/magana, wajen haɗuwa sai kuma yin ɓarnar”. Shi ya sanya addini ya hane tushen zina wato kalle-kalle !
Allah Ya dãtar da mu
Urs Nana diso
Email:kabba43@yahoo. com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO