DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

” Haba hajiyata wallahi zanyi ke dai kicigaba da yimin addua nasamu mata tagari?
” Addu’a?? Wallhi babu ranar da zanyi sujjada face na kira sunan ka sageeru ina jimaka tsoron zamanin nan mutum yayi auren ya yacika ballantana ku yaran zamani…
” Hajiyata ki kwantar da hankalin ki wayata tagaba dake inshaa Allahu ak’an aure nace…
” Yauwa ko kaifa Allah yayi maka Albarka yakuma tsaremin ku sharrin mutum da Aljan..
” Ameen hajiyata Allah yakara lafiya agaida su hammad da nazifi inanan tafe inshaa Allahu…
” Yauwa dan kirki zasuji kahuta lafiya kace ina gaida baffa da yasmin..
” Tohm inshaa Allahu..
Yusra ce tace oh tasmin akwana atashi babu wuya kinga saura shekara daya mugama, muna dawowa kuma sai waec da neco ko?
” Shiru tayi tana tunanin baffa tasan bashida kudin biya mata tayi jarabawa hawayenta ta goge tace eh hakane…
” Wallahi yasmin akwai abunda ke damunki sosai ke mutuniyar kirki ce Dan Allah ki taimaka kigayamin bakisani ba ko nakawo miki mafita kinga daga yau bazamu kara haduwa ba sai bayan hutu…
” Cikin murmushi mai kama da damuwa tace yusra bazan dawo makaranta ba…
” saboda me yasmin??
” saboda baffa na baida kudin biyan jarabawa idan yasamu nan gaba sai nazana dan bazan matsa masa ba wallhi….
” haba yar’uwata kada ki damu kamar kin zana jarabawa menene amfanin k’awancen mu idan bazamu taimaki juna ba…
” Allah sarki yusra nagode to Allah yabiyaki ke da iyayenki da irin dawainiyar da kukayi dani,wanda mukazo tare ma basa kulani ballantana kuma ita yayartawa…
” Bakomai ai daman naka yaki ka wane ya soka!..
” Tabbas hakane zomuje muyi alwala sai mu huce masallaci ko?..
” Ehhh..
” Ameen yace..
Barister wai yau lafiya kuwa ba walwala gashi kamar baki da lafiya??
” Wallhi munyi fada da dr na shiyasa nakasa sukuni yak’i daukar wayata yau kusan 5 mouth ko ta kaina bai bi nayi masa text akallah sunyi 50 wallahi “no reply i really love my dr i don’t think zan rayu babu shi wallhi I so much lurv him kinsan dai kauna to itace a raina kuma ta dr ce wallahi”..
” Ayyah ni zan kokarta naga na shiryaku inshaa Allahu bani number dinsa na kirasa naji…
” cikin rawar jiki tabata sannan tace amana Amal karki yaudareni kiji tsoron Allah…
” Ramlat kenan nifa saura 1mouth biki na kuma dan Allah zanyi miki wallhi…
” Nagode nagode sosai…
Daidai misalin karfe 3 yasmin ta sauka a mota bismillah tayi sannan ta bude gate din gidan su cikin annashuwa da kuma farin ciki, maganganun da suka dak’i kunnuwanta yasa ranta ya bace cikin sauri tafara tafiya…
” Alhaji isa ne kefaman cewa wallhi yau sai kabani dubu 50 d’ita idan bahaka ba wallahi kotu zata rabamu banza asararre mai jinin tsiya wanda dubu daya take gagarar sa…
” cikin hawaye baffa yace haba dan uwana kayi hakuri dan Allah wallhi ina samu zanbaka…
” bilal ne yace kaji tsohon banza hhahaha…
Yasmin ce ta ajiye akwatin tacikin zafin nama (Daman bahaushe yace mai hakuri bai iya fushi ba) kai bilal iya bakin ka kasan wazaka zaga idan zasuyi kabarsu suyi su biyu…
” Gaba daya suka jiyo suna kallonta takara ktau ga wata kiba datayi ga halittu ko’ina sun ciko abun dai bazaka ce yasmin bace sai ka kara kallonta sosai…
” ke yasmin ni kike gayawa haka…
” nunashi tayi da hannu tace kai bilal idan kanacin kasa to ka kiyayi ta shuri ubana ba sa’anka bani kuma kakara zagensa sai ranka ya baci wallahi…
” Alhaji isa ne yace shigeya ‘yar iska yimun shiru dangin talakawa idan kin cika kinason uban naki to sai kibiya masa kudin. …
” Jakarta ta zuge tabashi dubu hamsin sannan tace tozarci badai akan mu ba kuma ni inada tarbiya bazan ci maka kala ba Amma ina fata Watarana ku gani abunda kukeyi…
” kallonta yayi yace shigeya karuwa inba karuwanci kike ba a’ina kika samu kudin nan…
” tsaki tayi tace nanawa kenan ance da bunsuru dan akuya?
” baffa ne yace shige muje shige muji yasmin…
Bilal kuwa ranshi ya baci shida mahaifinsa suka fita basu so hakan ba…
” mama ce tace daman malam nagaya maka kasamo musu kudinsu gashi kaga yadda takaya…
” yasmin ina kika samu kudin nan har dubu hamsin???
” Nan tabashi labarin yusra da kudin da mahaifinta yabata yace tabawa babanta abiya mata kudin jarabawar ta..
Allah sarki mutanen kirki mungode nan baffa yace banson fitsara yasmin ko gaba kada kikara tanka musu kinji? Duk abunda sukeyi zasu kwashi kashin su a hannun su…
” Tohm baffa bazan karaba inshaa Allahu..
Bayan sallah magriba yasmin da mama suna bangaran su a soro a zaune dr yana dai dai kofar zai shigo sai yaji yasmin tana fadin..
” Ni nahakura da jarabawar mama zamana zanyi bazan koma ba kudin dasuka bani naje nabiyawa baffa bashi domin kare mutuncin sa…
” karki damu yamin Allah zai hore kinji murmushi tayi tace kems ga chanjin kudin kya siya wani abun…
” yasmin kenan Allah yayimiki Albarka…
Doctor tunda yaji kalaman yasmin hankalinsa ya tashi nan ya sanar da principle din yaturo masa da Account number yatura kudin jarabawar kamar daga sama yaji wayar ramlat cikin yanayi yace hello?
” kuka tasaka masa kayi hakuri dan Allah hubby please nasan nayi maka laifi wallhi u are my life..
” Ya huce ramlat Nima ina sonk’i sannan ya katse wayar…
” Yasmin tana zaune a k’an k’ujera sallama taji sannan ta daga k’anta yaya ina yini???
” ah kanwata k’inzama ‘yar dumama ke da boarding ke ramarwa ke kinyi kyau…
” Murmushi tayi tace Allah yaya?
” Wallahi kam nayi missing dinki sosai…
” Shiru tayi sannan tace yaushe ne bikin naku ne da barister?
” Gobe za’akai k’udina nida barister inshaa Allahu…
” kai mashaa Allahu, Allah yasanya alheri zamusha biki ashe?
” inshaa Allah please ki dafamin indomie zandawo anjima kinji??
” Tohm shikenan..
Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment…
Let me know what you think about this page…Ku gayan ra’ayoyin ku…
i request you to avoid spelling and grammar error….#TEAM DS
GOD BLESS YOU OLL….
Urs Nana diso
Deejarh berver
http//:deejarhberver.wordpress.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 8:22 AM] +234 703 475 7034: 15-20
DOCTOR
SAGEER
NA NANA DISO
http://deejarhberver.wordpress.com
© HASKE WRITER’S ASSOCIATION
Yasmin kin dora abincin dai ko?
” Eh mama,har nagama ma dr ne yace na dora masa indomie yanzu zai dawo…
” Ke dai jininku ya hadu da sageeru bakamar su abida ba?