DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

” Suma dan basajin magana ne..
” Lallai yasmin kinsamu bakin magana, Naga kema jiya fad’a kukayi da bilal?
” haba mama yaza’ayi ina gani ana zagin baffa nayi shiru ni wacce irin yarinya ce?
” Ai gwara da kikayi masa magana wallahi bilal bashida kirki babu wanda yake gani da gashi agidan nan…
Kamar daga sama sukaji sallamar Aisha dagudu…
” oyoyo oyoyo yaya Aisha sannu da zuwa cewar yasmin..
” Ai bakida kirki yasmin ace kina kanwata sau biyu kika taba zuwa benin dubi yadda kikayi kyau, kuma wai mama kina ganin ta?
” ke dai shiga muji ki huta ke da kikasha hanya…
Suna shiga palour ta durkusa har kasa tace ina yini mama?? Kuna lafiya??
” wallahi lafiya kalou yasu mujibat da hamid duk suna lafiya dai??
” lafiya kalou wallahi ina baffa?
” baffa yana gurin aiki ai sai yamma ke da ganinsa…
” yasmin ce tace kinsan garin naku ne nisa shiyasa baya burgeni…
” k’injiki ai ke a kaiki mambila naga tsiya..
” ke dai dakikayi auren nisan inshaa Allahu ni bazanyi ba!..
Dr sageer ne yashigo direct kitchen ya huce dan yasan yasmin tagama ta ajiye masa…
” Mama ce tace ke yasmin ba kauri nakeji ba??
” wayyoo indomie din dr cikin sauri ta isa kitchen din ta tarar dashi atsaye yama kasa magana…
” cikin garaje ta riki tukunyar ai kuwa sai tasaki saboda zafi sauri yayi ya riki hannu subhnlhi badai ki kone ba ko??
” Kayi hakuri wallahi ina hira ne shiyasa ta kone…
” Kallonta kawai yakeyi cikin wani irin salo da sai da taji wane yanayin dabata taba jiba acikin jikinta…
” Murmushi yayi yace bakomai bari naje na siyo wani abun…
” sai tace ai mungama abinci kaje daki bari nazubo maka…
” jikin wani salo yace mijinki yahuta yasmin…
” Shiru tayi masa batare da tace masa k’alaba..
Mamee ce tace wai ke maryam menene haka tun safe kike abu daya in anyi magana kiyi shiru meke damunki??
” Gyara zamanta tayi tace cikina ke ciwo..
” bari nakirawo sageeru sai yabaki magani inaji yana cikin gida ai…
” can tace mamee nawa aka kai kudin auren dr?
” dubu dari biyu mana, ansaka wata daya bikin…
” Cikin sanyin murya tace Allah sarki …
Aisha ce tashigo part din su mamee tare da yasmin dr yana bayansu Assalamu alaikum hajiya mamee menene duniya???
” Tsaki tayi tace kin bayana kenan uwar magana lafiya dai kikazo ince ba auren naki ne ya mutu ba??
” Aisha ce cikin siyasa tace ina auren mu zai mutu naku bai mutu ba kuna soyewarku…
” Ai nayi tunanin auren ne ya mutu ai kizo kukarawa baffan ku wani hawan jinin???
” Ina ai igiyar aure Allah kadai ke rabata mutum komai shidancin sa bai isaba…
” Tsaki takaraja ciki da tsanar Aisha da yasmin can tace sageeru Maryam babu lafiya fa?
” Yasmin ce tace yaya ana magana?
” Allah yabata lafiya anjima tashirya driver sai ya kaita asubuti ai..
” To shikenan ina surukar tamu??
” tananan tana gaidaki…
yasmin ce tace yaya Aisha tashi mu tafi…
” Sum sum sum dake uwar munafukai daga zuwanta zakice tatashi ku tafi to takiya…
” yasmin dai batace kalaba, Aisha tace ohh naga ranar da zaku gani wallahi in banda zumunci mai zai shigo damu??
” Ai kun tsosa agurin uwarku dole kuyi fitsara…
” tashi sukayi suka fita suna fita sukaga Alhaji haruna nan Aisha ta gaidasa..
” dangin tsiya kice kin bayyana bakar kadara haihuwar asara…
” Ko sauraran sa basuyi ba haka suka huce suka huce part dinsu sannan suka fashi da kuka…
” Mama ce tace ke aisha daga zuwanki sai kuka??
” Mama wannan wacce irin rayuwace ta kunci haba mama wannan cin mutuncin ace shi iyayena suke ji…
” Yasmin ce tace ai kadan kikagani yaya wallahi inkinga yadda suka tozarta baffa jiya sai kinyi kuka kuma wai ace bazamuyi magana ba???
” Mama itama taji haushin abun amma sai ta dake tace ai sai hakuri watarana zai zama labari …
” Aisha ce tace ni ko atatsuniya ban taba ganin irin tsanar nan ba?
Hakuri dai zakuyi Allah yana sane damu…
Mummy ce tace Allah yanunamin ranar auren nan naki barister yau dai ankawo kudi…
” Murmushi tayi tace mumy kinga gidan dayakeyi kuwa anjima zai turomin dan haka kisanar da dady asakamin hadaddun kayan daki please…
” Oh wannan wacce irin Amarya ce lallai zamani…
” mumy kenan Wayar tace tafara ringing cikin sanyin murya ta dauka darling dafatan kana lafiya?
” ke zan tambaya dafatan kina lafiya? Tun dazu tunanin ki kawai nakeyi acikin office , Ramlat ina tsananin sonki DanAllah ki kula dani?
” Har cikin ranta taji tace mijina bakada matsala ba, nima ina kaunarka dr zan iya komai akanka kuma zanyi maka hidima,zuciyata bazan bude wani yashigo ba ko kadan bazan so naga kayi fushi ba…
” Ramlat banason wannan aikin naki please ki rage saboda ina bukatar kulawar ki…
” DanAllah Mubar maganar aikina darling..
” Shiru yayi yace to sai anjima..” cikin juyi ta rungume wayar tare da murmushi, cikin mintuna taja motarta sai office tana iss tace kawata kinsan me??
Sai kinfada ince dai mutumin zai sakar mana kudi??
” ke ba wannan ba kinsan yace wai na jiye aiki!!!
” mtseww bashida hankali ke doluwar inace dazaki ajiye aikin ki ke yana zura kafarsa kema ki zura duniya fa sai da wuta bakiga yadda manyan mata ke shakstawarsu ba???
” Dadina dake kinaso ayi dani wallahi kam daman yaudarar sa zanyi nace zanbari sai nashiga daga ciki nacigaba…
” Yauwa ko kefa, barister lawal yana kiranki kije yana office…
” Tohm ina zuwa kawata bari naje nadawo nadan maganar case dinnan ce.
” Rabia ce tayi dariya mugunta tace ai sai najawo kinsa yasake ki da kanki banza tazata sonta nakeyi? Duk duniya na tsaneta yadda kika samu miji bansamu ba kema bazan barki kiji dadi ba.
” Barister ramlat ce tadawo tace kawata me muke cewa ma?
” Uhm daman zancen kudine million uku yakamata yabaki nagyaran jiki karki yarda ko million daya yabaki mugune fa dr yana samun kudi sosai….
” kinaso kiga nafito kawata kinaso kiga ina harka ban mutafa sannan suka tafa.
Yasmin ce ta dawo daga gidansu fatima tun akan titi wani saurayi ke binta amota har tayi sauri tashiga gida, A dai dai lokacin Alhaji haruna yaganshi sannan ya karaso yace lafiya kuwa??
” har kasa matashin ya durkusa yace ina yini baba? Daman wata yarinya nagani tun dazu shine nazo gurinta yanzu tashiga ciki..