DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

” fara ko baka lukutar ko siririya??
” yadan rissina yace yanzu dai ta shiga.
” To ina zuwa, daman kafin yakarasa yasmin tafito nan tace sannu ina yini? Lafiya dai ko?
” wallahi lafiya kalou daman inason mudan tattauna ne ina yawan ganin ki wallahi kuma naji kinshiga raina inason kitaimaka kibani dama in shiga sahun samarin danAllah?
” Shiru tayi batace komai sai ji sukayi Alhaji haruna yana kai yaro wannan yarinyar dakake gani cikakkiyar karuwace bin maza da mata agurinta yadda kasan dabba, dama daya daga cikin yarana kace kanaso da yafi dan sunfita tarbiya…
” kuka tasaka tace Allah shaida ne kifa mata mari yayi yace zaki yaudari yaron mutane shigiya ‘yar iska..
” matashin saurayin ne yace kaji tsoron Allah katuna tsayuwar ka da Allah sannan ya shiga cikin motarsa ya tafi..
” Ke kuma bakiga komai ba sai mun saka miki bakin jinin kare…
” Da kuka tashiga cikin gidan tagayawa mama komai Aisha tace kyalesu yar kanwata Allah shaidar ki ne Ai kuma shi zai cigaba da karemu karki damu da maganarsu.
Baffa ne yayi sallama Aisha tayi masa sannu da zuwa nan suka gaisa yace auta wayatabaki? ” Dariyar karya tayi tace babu kowa baba..” To kinji ankafe sunanki amasu zana jarabawa ran monday zaku fara sai ki shirya. ” cikin mamaki tace baffa wa yabiyamin? ” sageeru ne sai kiyi masa godiya. ” inshaa Allahu. ” Mama tace aikuwa angode.
” Aisha ce tace kasan ina koyarwa baffa kuma ina daukar kudi masu yawa gakuma business da nakeyi wallahi baffa bana taba komai acikin kudin sai dai ko idan zanyi taimako Allah yabani miji nagare komai shi yakeyi min bana siyar komai kuma nasan gar da adduar da kukeyi min duk da bana kusa daku domin ku iyaye nagari masu koyar da hakuri da yadda da kaddara.. ” yasmin ce tace hakane yaya Aisha. ” wannan jakar million 4 ce aciki da dubu dari 3 duk kudin aiki na da sana’a tace nakusan shekara 10 danake tarawa wannan gaba daya nabar maka baffa kaja jari domin tarbiyar da kake bani wallahi banda abunda zangode maka duk da bana kusa dakai komai kanwata tasa sai ka turamin duk da munyi nisa kuma mahaifiyata batasaniba, hatta kudin makarantar da kabiyawa yasmin naga kasiyamin atampa duk dan karka fifita wani acikin mu, kaja jari baffa ina fatan wanna kudin yazama dukiyar da Al’umma zasu amfana da’ita ..
” yasmin ce tasaka kuka ta rungume aisha tare da fadin tabbas nayi wani sabon karatun Anan idan kanason d’anka yatashi cikin tafarkin gaskiya to kasanar dashi ilimin addini kakuma zama babban misali nagurin koyar tarbiya,kar kuma kanuna masu bambanci , abunda zamuci miki shine Allah yayimiki Albarka yaya inasonki wallahi…
” Mama ce tasaka kuka tace tabbas mai hakuri shikeda riba, ako da yaushe baffa kana fadan Allah yana sani damu kuma zai dubimu yau gashi ranar tazo ranar da mai hakuri zai ci riba, Allah yayi muku albarka aisha Allah yasaka muku da Alheri halinki nagari yasa ‘yar uwarki tagado halinki…
” Baffa ma yayi musu addua tare da godiya sannan yace yadda kikace naja jari zan koma sana’ar mahaifina wato atampofi tunda tun ina karami na iya sana’ar daman ba lallai kayi ilimi kakuma samu sanaar da kake tunani ba wane sain sai kaga alkhairin ka yana inda baka tunani especially idan kana addua …
” Tabbas hakane..
Yau Aka kai lefen dr sageeru akwati goma sha biyu kaya masu kyau, wani satin za’a fara biki yasmin kuwa ta hada kayanta zata koma boarding tun karfe 8 baffa yasa aka kaita gida ya cika da hidimomi kalakala..
” Da daddare dr sageer yaje gurin ramlat taci kwalliya bakace ita bace ba daman irin siraran matannan ne ga ido amma batada hanci sosai kuma ita chocolate colour ce sai dai iyayi acikin ta kamar me tana zuwa tace ya muradin zuciyata.. ” Cikin kayataccen murmushin sa wanda ya bayyana hushiryar sa da hakorin makka yace Amincin Allah ya tabbata agareki ya ruhin zuciyata amaryata kuma muradi
na…
” yauwa mummy tace in gayamaka kayafa sunyi sai sai Allah yabiyaka kuma gobe zasuje jiran kayan dak’i ..
” Dariys yayi yace tohm shikenan na riga nacika saman ku kwacika kasan kitchen dinki katoto kinsanni da son abinci…
” Haha lallai kam..
To ni inada aiki yanzu sai zuw gobe in Allah yakaimu..
” kagaida gida sannan tashiga cikin gida..
Baffa ya bar aikinsa yasamu babban shago ya zuba kaya aciki, da magriba yana dawowa yayi sallah, Dr sageer yana shigowa yace baffa naga yanzu kana yin yamma??
” Eh da yake yanzu nakoma shago nazuba kaya.. ” shago baffa? Ina kasamu kudi?? ” Wanda ya yarda da Allah ai shi zaisha kallo, ga dubu dari tukwuicin bikin ka Allah yasaka albarka a auren ku kuma kaji tsoron Allah kariketa dakyau..
” To baffa nagode Allah yakara budi sannan yatafi, ” mama tace gaskiya nayi dacen miji wallhi mai boye sirrin gidan sa akwai da babu..
” Murmushi yayi baice mata komai ba…
Yau jumma’a yau aka fara biki sunyi kamu da dinner sai dauren aure abun ba a magana sai wanda yaje biki dai yayi kyau sosai kuma manyan mutane sun halacci bikin su abida da maryam da bilal basu haukace ba sai da sukaga gida kowa baisan yana ginin ba kallon kolo sukeyiwa dr sageer nan suka dawo gida suma zagin. ” mumy da dady sunyiwa ramlat fada abisa gaskiya da amana sannan aka tafi da ita hajiya suwaiba itama tayi mata sannan akayi gidanta..
Lokacin da aka kaita bayan kowa ya watse tayi kwanciyar ta sai bacci lokacin da dr sageer ya shigo yaganta ta kifa cikinta sai bacci takeyi yana kokarin tashinta sai kuwa tace please darling bacci sai da safe shima haka yayi shafa’i da wutir sannan ya kwanta da asuba kuwa bayan yafita tayi sallah rabia ta kirawota tace kada fa kisake kice zaki zauna kiyi tawowarki office kinga munada case mai zafi…” eh daman zanzo sannan ta kashe wayar…
” Hajiya suwaiba tare da aisha suka koma benin , yasmin kuwa batasan abunda ake ba tana can tanata karatun ta..
Su abida kuwa yanzu aka kara samun kofar yawo, mamee tace kowannen su yaje ya dangwalo mata babban arzuki dan bazata aurawa talaka ba..
Ina zakije ramlat??
” wacce irin tambaya ce dr inada aiki mai mahimmanci a office i neef to live kafin na makara..
” Ai ban baki izini ba ko ni na dauke hotu a office..” sai ka koma kaga matarka tafita itama..
” Ramlat ban baki izini ba nagaya miki…
” hmm kaga sai nadawo…
” zama yayi kan kujera tare da takumi…
Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment…
Let me know what you think about this page…Ku gayan ra’ayoyin ku…
i request you to avoid spelling and grammar error….#TEAM DS
WANNAN SHAFIN SADAUKAR WANE GAREKU FACEBOOK READER’S ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI SAK’ON NINKU SUNA ISA TA, INA KUMA GODIYA SOSAI…
GOD BLESS YOU OLL….
Ya zo a hadisin Mu’ãz d’an Jabal (RA) yace: Manzon Allah (SAW) yace:
(( Ka ji tsõron Allah a duk inda kake, sannan ka bibiyar da kyakkyãwan aiki a kan mummuna; sai ta shãfe/guge ta -ita mummunar-, kuma ka yi mu’ãlama da mutãne da kyãwawan d’abi’u )).
Imãm At-tirmizy, kuma yace: “Hadisin Hasan ne”.