DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

    ” To munafika ke wannan mutumin kike sanarwa me zai baki kudin sata kokuma kudin yankan kai??

    ” baffa ne yabata kudin yace gashinan Allah yataimaka abida…

     ” Kuka tasaka tace tabbas nagani wallahi mutumin kirki daban yake tabbas kai mutum kirkine baffa har ka’iya biyamin kudin makaranta Amma lokacin da baka dashi babu wanda ya taimakawa yarinyar ka???

    ” ba dan kowa nayi ba nayi dan Alkah ne sannan yashiga cikin gida yana zaune suna tattaunawa sukaji sallamar yasmin tare da akwatinta…

    ” baffa kuna lafita??

” mama ce tace sannu da hanya yasmin Allah yasa kici jarabawar sai kuma jami’a…

    ” baffa ne yace jami’ar lafiya sai dai aure miji yana fitowa zatayi aurenta…

   ” ita dai dariya tayi tace Allah ubangiji yayimana zabi nagari..

    ” Ameen auta..

Shekaru sai wakana sukeyi yasmin kullum cikin kuka domin baffa har yagaji tafara makaranta tunda babu maganar miji da sunzo sai aji shiru ga abida tayi aurenta sai maryam kadai ga barazar da kullum khalil yake mata na yana sonta yauma kamar kullum uncle nafeeu yazo tashirya kenan sai ta zauna k’an kujera…

    ” mama ce tace wai yasmin ba baki kikayi ba??

    ” kuka tasaka tace mama kullum ace saurayi in yazo bazai dawo ba mama basa sona ace yayan mahaifinka su dinga korar maka samari gashi har ina kokarin gama jami’a kullum zagin da akemin naki aure sai mai kudi…

     ” Nima mahaifiyar ki sai danayi tunanin haka yasmin sai daga baya nagani akwai wani abun akasa yasmin karki damu jinkirin ki inshaa Allahu zai zama Alkhairi ki tashi kije bansanki da wulakanci ba kinji?

    ” Tohm tace sannan tafita tanayin sallama yace yasmin lafiya bakida wayane???

    ” eh wallahi banda ita baffa ne bai siyamin ba shiyasa…

    ” A daidai lokacin dr sageer yayi parking yana fitowa yatsaya amsa waya…
 
     ” yasmin daman nazo nasanar dake sai nadawo daga sudan za’a kawo kudin mu inason naje nakara karatu…

      ” kallonsa kawai takeyi hawaye na bin fuskarta tabbas tasan zatayi rashin masoyi nai kaunarta mai sonta shikenan tasan kuma balallai ta auru ba tunda shi kadaine yane idan alhaji haruna ko isa sunyi mata sharri sai yace bakomai yana son abarsa…

     ” Yasmin menene na kuka kinsan dai ina sonki kuma 5month kawai zanyi nadawo kima kafin lokacin kin karasa makarantar ki dan haka kada ki damu ina tare dake kinji?

     ” idonta daya riga yayi jajir tace to Allah yabaka saa tayi shigewar ta tana karasa gate Alhaji isa yace k’arya mai bakin jini yauma yazo ya gudu kenan ke da aure sai dai kiga anayi , aguje ta takarasa gida tana shiga ta kifa kai sai kuka…

    ” wai ciwo kikeso kisawa kanki ne so kike nima nakamu da ciwon?? Yasmin ina hakurin naki…

    ” kuka takara fashewa dashi sannan tace mama kinji me baban bilal yace min wai bazantaba auruwa ba kullum sai ya zageni kullum kuma samarina basa zama, yanzuma uncle yatafi bansaniba ko shima guduwa zaiyi sannan takara saka kuka tace mama shi kadai nakeso inason uncle nafee’u tayaya zuciyata zata rabu dashi…

   ” Dr sageer ne yayu sallama ya shigo amma basuji ba sai tsorata da yayi da irin kukan da yasmin takeyi…

    ” mama ce tace to kibar kukan…

    ” kukan takara fashewa dashi tare da fadin kibarni nayi ko naji dadi inason uncle nafee’u yaya zanyi yanzu mama??

    ” mama ce kwallah suka cikomata idonta tare da barin gurin ta shiga daki…

    ” Dr sageer ne ya tuna da irin rayuwar da yayi abaya sannan yazo yazauna akusa da yasmin hannunta ya riki yace haba kanwata me isa kike damun kanki haka???

    ” bakinta ta cije tace dr so shakuwa su ba’a boyesu ina mutukar sonsa kamar yadda yake sona shi ya koyamin sonsa in yatafi yabarni yaya zanyi ina zan saka kaina???

     ” Yasmin kenan bakisan akwai wanda yakeson ki ba fiye da kanki fiye da masoyanki??

     ” shine uncle nafee’u yaya har yanzu bakasan zafin soyayya ba tunda kana tare da wacce kakeso dan haka ka kyaleni kada…sannan tasaka kuka mai cike da tausayi ta shiga dak’inta…

    ” yanayin da yashiga yasa shi barin gidab gabadaya yana isa yaga ramlat bata dawo ba tana dawowa ya kifa mata mari ke wai bazakiji maganata ba to menene amfaninki ban isa na baki umarni ba kullum kina titi tunda nayi auren nan gaba daya na rame wai ahaka ina da mace meke damunki wai aikin ince sai da izinin miji???

    ” in kagaji ka sakeni kokuma ka auro mai yimaka bauta dan ni bazanyi ba…

      ” eh aure babu fashi wannan watan zan kainm kudi zan kawo wacce zan koya mata soyayyata…

     ” tsaki tasaka sannan tace kakaro uku idan ka’isa…

      Tana shiga daki mumy ta kirata tace mumy kuna lpya??

    ” lou tambayarki zanyi daman mijinki yayarda kidinga aikine kullum kina tafe? Banson hauka ramlat ina gayamiki gidan ki shine rufun asirinki kuma kawaye ba nakibani ba in bahaka ba sai sun kashe miki aure…

    ” mumy yafa yarda har kaini yakanyi..

      ” to Allah yarufa asiri…

  ‘” Nan takirawo rabia cikin rawar murya tace ke wai aure zai kara dr fa???

     ” haba? To kidaina gyara gidan kidaina girki kidaina komai kizama kazama hakan zai taimaka miki sosai yace yafasa??

     ” Tohm kawata angama!!!

  Yasmin ke kusa da mama tana karatu sai wayar mama tayi ringing tana dauka tayi salama yusra ce ta dauka tace kawata kina lafiya???

     ” yasmin tace kwana biyu shiru baki da kirki!

     ” kinsan ina benin sai next 4month zan dawo dama kiranki nayi ingaya miki wata magana Amma inaso ki fahimce ni kikuma yarda cewa matar mutum kabarinsa kuma mijin wata baya aurar matar wani, soyayyar da kukayi abaya ki dauka kaddara ce kuma kidaina damun kanki akan abu domin Almah kadaine keyi…

    ” Nifa bansan inda kika dosa ba?

      ” uncle nafee’u yayi aure suntafi tare da matar sudan tun 4days back!..

       ” Tohm nagode Allah yasaka min yaudarata da yayi…

     ” kitsaya ki saurare ni yasmin sannan ta katse wayar kan kafadar mama ta kwanta tana kuka nan tasanar da’ita…

     ” mama tace bakomai Allah yabaki wanda yafisa…

     “Tun daga ranar ta rage magana tama daina kula kowa sai gaisuwa yau baffa yana kan kujera mama tace kaga yasmin zata kashe kanta fa kullum kuka!

      ” Dak’in ta yashiga da kansa yace auta??

       ” Naam baffa..

Ki shirya zamuje benin gobe kuma kada nakara ganin ki kina wani tunanin kinji..

     ” tohm baffa inshaa Allahu fuskarta ta kumbura saboda kuka…

    Dr sageer yana zaune a office yace kai khalifa karin aure dole fa…

     ” please kabar zancen nan menene aibun ramlat???

    ” fitsara karya kazanta ….dan haka soon zankara aure…

   ” Toh Allah yabada tagari…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button