DOCTOR SAGEER HAUSA NOVEL

“Daga nan ya dauki motarsa direct sai gida bayan yagaisa dasu ummi sai yayi hanyar su yasmin yana shiga tazo fita zata karasa kenan ya riko hannun ta tajiyo tace lafiya???
” Yasmin zaki aure ne danAllah ki taimakawa zuciyar data dadi tana begenki tana kaunarki…
Kada kasoma kada kafara uncle yana cikin zuciyata bam tunanin akwai mai ciremin sonsa kagane…
” yasmin pleass kitsaya taja hannunta sannan tafice…
Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment…
Let me know what you think about this page…Ku gayan ra’ayoyin ku…
i request you to avoid spelling and grammar error….#TEAM DS
Urs Nana diso
Deejarh berver
http//:deejarhberver.wordpress.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 8:23 AM] +234 703 475 7034: 25-30
DOCTOR
SAGEER
NA NANA DISO
http://deejarhberver.wordpress.com
© HASKE WRITER’S ASSOCIATION
Dr sageer da yafi minti talatin atsaye bak’omai yake tunani ba face in Allah ya rubuta yasmin ba martar sa bace ba dole ne ya hakura, cikin yanayi yaja numfashin sa sannan yace ya Allah ka dubi ne, motar sa yakarasa ya bude bai isa ko’ina ba sai asubuti nan ya duba wasu marasa lafiya sannan ya huce office yana zama yana kokarin cike wasi files sai wayars tafara ringing dauk’a yayi yace hello ramlat ina lafiya??
” eh lafiya! Please ka tawo mana da abinci a resturant cuz bazan dawo da wuri ba!…
” wai ke ramlat zamanki nakeyi kokuma zamana kikeyi?? Tunda kikazo gida 3times kika dafa abinci kullum ina hanyar gidan ABinci yanzu abunda kikeyi adalci ne??
” Kaga dr gwara kadaina bata bakin ka cuz ba fahimtar maganganun ka zanyi ba danhaka sai kadaina yimun ihu aka idan kaga dama sai kasiyo wa kanka ni zanci anan…
” Dr sageer ne yace yayi kyau ramlat zaki gani k’urunki..
” wane tsaki taja mtseww na dade banganiba…
Juyawa yakeyi akan kujerar sa cike da tunanin mafita can nurse kwankwasa kofar..
” sir akwai marasa lafiyar da zakagani fa sunata jiranka..
” okay zasu iya shigowa wata matashiyar ce ta shigo tace ina yini dr?
” Lafiya file name?
” fatima idres..” meke damunki??
” wallahi dr inada matsala bakina sai ya dinga wari kuma gabana shima wani wari dr mijina bakaga yadda yake wulakanta ne ba doctor please ka taimaka min..
” okay zanyi miki abunda zan iya amma nafarko kinayin brush??
” eh doctor wane sa’in inayi amma ba sosaiba..
” to kice ke kazantar ki kikeyi kinsan kuwa babu abunda namiji ya tsana irin kazanta kidinga kokarin wanke bakinki ko sau biyu ne kuma kisiya mouth frshner kina kuskurewa kuma kada kici abinci kikwanta batare da kin kuskure bakinki ba inatunanin inkika bi hanyar nan bakin zai daina wari inshaa Allahu…
” Tohm likita zansiya brush ina fita inshaaAllahu sai dai kuma warin da gabana yakeyi likita…
” kafin nan amsamin tambayoyin nan idan kina shaving din gashin gabanki??
” Wallahi likita banayi tunda nayi kafin haihuwata naga kuraji sunfito min sai kawai nadaina…
” Ai ko amusulci babu kyau barin gashi yahuce 40days kuma babban abunda ke kawo warin gaba harda rashin aske duk wata kazanta ta dank’are agurin kuma dazarar kinsa pant zakiga yayi datti dan..kuma zancen kuraje dakikeyi halittane wane idan ya aske bayayi wani kuma yanayi dan haka yanzu sai ki aske sai kishafa mai agurin kuma kina askewa akai akai…
” tohm likita inshaa Allahu…
” idan kikayi fitsari bayan kinyi tsarki kidinga barin ruwan yana kafewa saboda wannan danshin da ragowar ruwan da zai jika miki pant dinki shima yana saka wari sosai kuma zaiyi miki illah..yana da kyau kidinga canja wando sau biyu kuma kidaina zama akasa kokuma guri mai danshi kidinga wanke gabanki da ruwa sosai kina canja sabon wando akai akai..kuma kidinga wanka janaba da wuri dan rashin wank’an da wuri kan iya saka warin gaba shima kodan ka kasance cikin tsarki da rahamar Allah kayi wankan da wuri..kuma ki daina yawo babu takalmi kina saka safa inda hali kuma kidinga yawan shan kayan marmari wayo fruit zasu taimaka miki inshaa Allahu in dai kika lura da wannan to zaki daina wari…
” To likita hammata fa?
” ita kuma menene matsalarki??
” wallahi babu wuya nayi wanka ko 1daya banayi sai wari har banaso nashiga cikin mutane kuma koyaya nasaka kaya wari mai idan nasaka turaren warinsa daban warin hammatar daban warin sure daban…
“eh gaskiya abunda ke kawo warin hammata shine rashin askewa dazarar gashi yafito mutum sai ya aske zaiga baya irin warin nan amma idan gashi yayi yawa kowanne irin sure zaki saka bazai dauka ba, Amma idan kinayin wanka kisa soso kidirje hammatar sai ki aske kikara wankewa inkika fito ki shafa turaren hammatar ki ko baki shafa ba indai bakya barin gashi yayi yawa to zakiga bakya warin nan dan haka sai kikula da aske da kuma shafa turaren hammata da dirje hammatar idan anje wanka kuma ku masu miji kudinga daurewa kuna wanka sau biyu…
” likita me zance maka da wannan sharawa naje asubuti da yawa babu wanda yagayamin gaskiyar daka fadamin nagode nagode kuma inshaa Allah zanyi yadda kace daman sonjiki ne irin nawa Amma yanzu naga son jiki baidace ga mace ba…
” juya kujerar sa yayi sannan ya danna bell dinsa next person ya shigo…
Yasmin ke zaune k’an sallaya tagama sallar walhar ta sai jin wayatayi cikin rashin kulawa ta dauka tace yaya aisha kuna lafiya??.
” bansaniba wai meke damunki kowa yazo kice bakya sonki abunda makiya sukeso kenan wayagamiki asiri akai miki ke ma harda halinki idan anyi miki asirin kema sai kina kokartawa ai amma kowa yazo sai kice bakyaso ba dole suji dadi ba sudinga tunani mugun tuggun da suka hada yayi ba..
” Haba yaya aisha ke fahimce ne mana wallahi…
” dakata yasmin dazu mama takirani kin dage ke sai nafee’u mutum makaryace mara sonki wanda yayi miki karya yace karatu zaitafi bayan aure zaiyi kina tunanin miji to wallahi kiyi tunani kuma kikula kada mama ciwon ta yatashi akankk kowa ai mijinsa yake aure inma abun duniya kike hanga sai ki daina shi arzuki na Allah ne kiyi fata kisamu mai addini mai kuma rufin asiri ba mai kudi ba…
” Cikin kuka tace nagode sannan ta katse wayar cikin kuka mai ban tausayi tace yaAllah in zunubi nakeyi dan yarasulillahi ka yafemin kayimin afuwa ya Allah kazabamin abunda yake alkhairi agareni…
” mama ce ta liko au kukan kikeyi uwar kuka kidaije kisawa kanki ciwo…
” sauri tayi ta goge fuskar tace aa mama..
” To ki bari kije ki doramana abinci Allah yana sane dake!..
” tashi tayi ta sun kuyar dakanta..
” Mama da hawaye ya wanke mata fuska ta goge tace Allah yayi miki albarka yasmin..