GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Shine yafi kowa sanin Inayah sbd shine mahaifinta Dan haka fuskarta da yanayin shigarta ya bayyanar Masa da ‘yarsa na cikin damuwa…

Sake kallon yanayinta yayi yanda take cin abinci jikinta amatuqar sanyaye bakuma wai Dan tana jin yunwa ko dadin abincin ba,
Cusawa kawai takeyi.

Gun umma yaganah ya ‘dan maida kallonsa yaga yanda ita Kuma take Dan hada kokarin share guminta akai akai duk da tsananin sanyin Aircon da babu Inda babusa a cikin gidan…

Maida kallonsa yayi a natse kan Inayah da hankalinta Baya kan kowa saina abincin datake ci Shima bawai hankalinta na kan abincin bane.

Jin yayi kwata kwata abincin dayake gabansa fita ransa sbd yasan akwai abinda suke boye Masa Dan daga umma yaganah har Inayar babu Wanda Bai San halayensa ciki da wajeba,hakama kallo daya yake musu kowannensu ya gane halinda suke ciki sbd Sam Baya Wasa da kulawa dakuma tarbiyar gidansa Wanda umma yaganah ta jima da Zama cikin ahalinsa Dan haka itama duk da tana matsayin uwa shine Mai lurarda ita lokuta da dama.

Ruwan sanyi da aka Dan zubawa lemon ya dauka ahankali yakai bakinsa yasha tareda ajiyewa ya dauki tissue ya goge bakinsa ya miqe yabar dining din.

Daga umma yaganah har Inayah babu Wanda yayi Magana daya miqe din sbd hankalinsu Baya Kai Kuma hakan yasake tabbatar Masa da zarginsa akansu na akwai abinda suke boyewa basason ya sanin Dan Bai taba miqewa daga dining batareda dayansu ya ringa maimaita Masa ko ya qoshi da abincinba Dan sun San rashin zamansa yasa Baya wani samun damar cin abinci yanda ya kamata shiyasa daya miqe zasu fara tambayar ya koshi kokuwa ya zauna yaqara ci.

Yana barin dining din Umma yaganah ta kalli Inayah cikin qosawa tace”

Inayah kinason sakawa Abbinki tunanin akwai wata matsalar ne?

Ba nace Miki da kaina zan sanar Masa ba idan aka bada lokaci akasan Gaskiar lamarin¿

Kallon umman tayi tana jin damuwa sosai,
Ita sbd batada uwa batama San uwartaba shiyasa Abbinta takejin idan Abu ya sameta Bata sanar masaba kaman zuciyarta Zata buga.

Ahankali ta gyada Kai tana cewa”

Abbi fa kinsani kwana biyu cikakki bazamuyiba muna wannan boyon zai gano mu.

“Nasani shiyasa nakeson kiyi kokarin cire damuwar komai aranki.

Bata iya cewa komaiba ta miqe tana daukan tissue tace”

Zan kwanta da wuri umma,
Goodnight.

Daqyar ta iya tattara kanta ta nutsu yanda Abbinta bazai gano kamaiba ta qarasa palonsa cikin sanyi da shagwaba ta nuna Masa bacci takeji Zata kwanta da wuri tai Masa goodnight Shima ta fice.

Bai bi bayanta da kalloba sbd Baya buqatan qari fahimta yasan for sure akwai wani abu,

Idan irin hakan tafaru bayace musu komai sharesu yake sbd cikin kwana biyu yasan zai Gama sanin meke faruwa.

Tana barin palon Abbi taji idanuwanta na cikowa da hawayen rashin sanar dashi damuwarta sbd Abbinta shine maganin kowacce damuwarta Wanda Allah ne ya tsaya musu duka akan hakan.

MAMUH

LOVE

MARRIAGE

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810716
Arewabooks@Mamuhgee
Tana Isa bedroom dinta ta kwanta ko kallon Inda wayarta take bataiba.

Bata wani qin samun bacci ba,
Sosai tayi bacci kaman yanda ta saba saidai tana farkawa damuwar dake dabaibaye cikin ranta ta dawo Mata sabuwa fil harma wani ‘dacin maqoshi takeji sbd tsananin damuwa da fargabar abinda zaije yadawo,

Tanajin wani irin tsananin bacin Rai da zafin abinda Zaid din yayi Mata da har takejin bazata taba iya mantawaba Amma ta wani bangaren tana cikin tsananin fargaba da tsoron rasashi sbd girman son datake Masa.

Tayi lattin sallah Dan haka alwala tafara yowa tazo tayi sallar asuba tukuna tayi adhkar.

Tana gamawa ta koma kan gadonta tashige bargo tana son komawa bacci.

Rufe idanuwanta tayi tana sake gyara kwanciyarta Amma takasa Jin dadin kwanciyar,

Sake juyawa tayi dayan banagren tana Dan yamutsa fuska cikin yanayi na qosawa.

Jin duk batajin dadin kwanciyar yasata yaye bargon datake rufe dashi tareda tashi zaune ta kalli wayarta dake kan bedside, takuma dauke Kai tana Dan sake yamutsa fuska.

Mintuna biyu ahakan kafin ta qarasa yaye bargon tayi gefe dashi tareda ziro qafafuwanta qasa tana daukar wayarta ta kunna ko duba wayar bataiba daga kunnawan darai ta ajiyeta Nan Inda ta dauka ta miqe tsaye tareda nufar Inda tarin jerin takalmanta suke jere Kaya guda,kusan babu designer shoe brand dinda batada masu zallar tsada.

Time ta kalla taga yanzuma 6:30 tayi Dan haka tasan har yanxu dadynta Yana geam,

Riga da wandon Nike ta saka black da Triple S Balenciaga sneakers farare ta fito ta nufi gym Dinsu dake gidan Wanda saika ratsa palon daya raba palonsu Dana Abbinta zaka Isa watadaccen gym din Mai girma da tsari.

Tana Isa knocking daya tayi ta tura kofar da kusan tafi karfinta sbd qarfin kifar tashiga tana gyara qaramar Vandanar dake kanta.

Sanye yake da black Lululemon wears na exercise,
Bench press yakeyi da nannauyan qarfe a hannayensa Yana dagawa da dawowa,

Shigowarta baisa ya dakataba Kuma Bai waiwayo ya kalli Wanda ta shigoba Dan yasan babu Mai shigowa Nan din kaf idan ba ‘yarsaba.,

Cikin kauna da kulawa ta qaraso gurinsa tana cewa”

Good morning Abbi”

A natse ya qarasa abinda yakeyi ya ajiye qarfen tareda tashi zaune wasu qananun zufa abinda ya Gama suna gangara kan lafiyayyar fresh fatarsa ya kalleta lokacinda take daukan ruwa tana basa takuma cewa”

Abbi ka tashi lfy?

Idonta yafara kalla baiga alamar rashin bacci atareda itaba Dan haka Kai tsaye cikin nutsuwa da kulawa yace”

Morning Inayah,
Lfy kalau alhmdllh,
Me zakiyi da gymin yanzu?
kinason ki rage keda kike amarya?
Ko Kin manta kin daina zumudin auren ne tun yanzu?” ya qarasa cikin yanayi na Wasa da ‘yar tasa tilo.

‘yar qaramar dariya tayi tana hawa kan leg press machine tafara ahankali tana cewa”

Abbi naji banason auren Kuma yanzu
Banason tafiya nabar gida,
Abbi kullum zanyi missing naka,
Gskia Zaid zai ajeni a Inda zanna ganinka.

Murmushi kawai yasake ahankali Yana goge qananun zufansa da wata farar towel qarama yace”

Zaki Saba ahankali musamman idan kika Zama uwa,
And kafin can ma you will be busy with your work bazaki samu lokacin tunanin kewan gidaba.

Abbi duk da hakan nasan kullum sainayi kewanka,Dan Allah Abbi kace musu anan zasu ajiyeni.

Girgiza Mata Kai yayi Yana murmushin wautarta da har take cewa ta girma yanzu idan Yana Mata fadan wani abun,

Haryanzu jinjira ce shi agabansa Dan ko wannan auren Dan kawai ta nace tanaso ne yanzu yasa zaiyi Mata Amma tabbas da saita sake wayo da girma sosai
Aqalla saita fara aiki tasan ciwon kanta Dana rayuwama Dan kuwa haryanzu Batasan komai na rayuwaba,
Babu abinda tasani daga mahaifinta sai mahaifinta tukuna sauran abubuwan.

Tare suka qarasa gymin din suka fito itace mai surutu Yana saurarenta hankali kwance daga shi har ita skin Dinsu glowing kawai suke gasa ta tsantsar hutu da wadata kasancewar shi rigarsa armless sai dogon wando,
Itama rigarta qaramin hannu me da ita sai dogon wando.

Kowannensu hanyar dakinsa ya nufa,
Wanka tafara tubewa tayo ta fito kenan wayarta tahau ringing ta qarasa tana dubawa taga Zaid ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button