GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Washe gari wuni tayi a daki tana dube dube a waya da laptop sbd asibiti da Zata fara zuwa,

Abbinta yafison tafara aiki a asibitin gwamnati kafin taci gaba dayi a asibitin kudi sbd shi qwarewarta yakeso a aiki bawai samun ilimin abuba kawai aiki dashi yafi buqata.

Kasancewar Bata Gama hada emails dinta aka fidda ba dama sauran uzurirrika yasa dole a satin Bata fara zuwaba Saida sukai kwana goma Sha biyu da Zuwa Nigeria din tafara fita.

MAMUH

A MAJEED/INAYAH

LOVE/MARRIAGE

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107
[10/20, 1:31 PM] +234 808 711 8630: 20
Arewabooks@Mamuhgee
Ranarda tafara fita aiki tareda Safnah sukaje sbd driving din Nan Sam batajin Zata iya,

Driver ne yakaisu babban Lagos State general hospital.

Dr Abdulsamad salees ne likitan da CM yayiwa magana Musamman Dan ya ringa kulawa da aikin Inayah din dakuma guiding nata sbd yanayin asibitin Nan da can Inda tayo karatunta dabam.

Dr Abdulsamad kallo daya yayiwa Inayah ya fahimci hankalinta ya ‘dan tashi da asibitin sbd yanayin hargitsinta,

Shima ba wani jimawa zaiyi a asibitin ba shekara daya zaiyi yakoma Abuja can asibitin dayake aiki,
Yanzu watanninsa hudu anan din.

Qayataccen murmushi ya sake Mata Yana kallon yanda hankalinta yake Neman sake tashi duk da yasan tasan duk Mai aikin ceton Rai da lafiya Baya kasancewa Mai tsananin qyanqyami sbd aikinsu Bai gadar musu da hakan ba.

INAYAH” yakira sunanta cikin kulawa da sakewa fuskarsa daukeda murmushi.

Kallonsa tayi da idanuwanta a natse itama ta amsa da”

Yes Doctor.

Muje afara shigarda isowarki da fara aikinki.

Wucewa sukayi a jere Yana sake Jan hankalinta gameda wasu abubuwa da yanayin asibitin.

Gyada Masa Kai takeyi tana saurarensa a natse har suka Isa sukai abinda zasuyi suka fito.

Safnah Bata tsaya jirantaba sbd dama iya rakiyarce tata Dan haka tareda driver suka koma gida sukabar Inayah din.

Har qarfe biyu suna tareda Dr Abdul suna fama da patients,

Ba laifi taji dan dadin aiki dashi Dan kuwa sosai ya Bata kulawa da tattali
Gashi ya kware sosai akan aikinsa.

Sai kusan karfe 3 tadawo gida a matuqar gajiye.

Wanka tafara yi tareda wanke jikinta sosai Dan kayan data dawo dasuma daga Palo ta ciresu tabawa zubbi akai laundry dasu.

Sallar la’asar da aka Gama tayi Dan tayi azahar acan.

Tana idarwa Bata nema abinciba kwantawa tayi tayi baccin awa daya da rabi kafin ta tashi Takoma toilet tayo brush ta wanko fuskarta ta fito tana duba wayarta dake silent.

Miscalls din Abbinta ne guda biyu saina Neesah ma kusan hudu saina Mimi mahaifiyar Safnah ‘daya.

Dakin umma yaganah ta nufa tana Kiran wayar Abbi.

Bai dagaba tasan dama zaiyi wuya ya daga waya lokacin Dan haka Bata sake Kiran kowaba ta ajiye wayar tana Zama gefen umma yaganah dake kallonta cikin kulawa tace”

Umma yaganah yunwa zai kasheni.

Murmushi umman tayi tana cewa”

Ahakan Zaki Zama yanda Abbinki keson ki Zama?

Bana gane wannan yanzu umma yunwa nakeji sosai fa,
Banci komaiba a asibitin
Bazan iya Shan koda ruwaba a asibitin Gaskia,
Dr Abdul yaso muje restaurant naci abinci Amma bazan iya cin komaiba batareda nazo na cire kayan jikina nayi wankaba.

Zubbi ta qwalawa Kira da muryarta Mai sanyi ta gajiya.

Zubbin a kusa take dama Dan tana Palo tana gyaran yamma shiyasa taji Kiran tazo.

Yes Ma gani.

Zubbi ki kawon abinci.

Ok.

Juyawa tayi ta fice tareda nufar hanyar kitchen.

Brown rice da chilled chicken akai su Kuma aka zubo Mata sai ruwa Mara sanyi sosai.

Taci abincin sosai ba laifi kafin Tasha ruwa ta bawa zubbi kayan ta maida.

Sai alokacin tadawo daidai dan haka takuma daukan wayarta tafara Kiran Neesah.

Maganganunsu sukaita Yi tsayin lokaci kafin suka Gama wayar.

Bata Kira Mimi ba sai bayan sallar magrib shima sbd ta sake kirantane.

Gaisawa sukai a mutunce sai Mimin data ringa tambayarta aiki cikin nuna kulawa.

Sosai taji dadin yanda Mimin ta nuna kulawarta harma ta ringa janta hira.

Sun jima suna wayar kafin suka Gama bayan ta Bata Safnah sun sake gaisawa itama Tai Mata sannu da gajiyar yau.

Sbd tasan Zata fita ko goben yasata kwanciya da wuri bayan tayi sallar ishai.

Abbinta ma saidai Tai Masa text ta tura Masa ta kwanta.

Washe gari akan lokaci ta shirya ta fito cikin blue skinny jeans da farar laced chiffon top Mai Fadi sosai.

Black Prada strap sandals ne a qafarta sai black Prada handbag.

Ko data fito driver na jiranta Dan haka tea da cake kawai taci ta fice.

A hanya tayi waya da Abbinta harsuka Kai tana waya dashi
Saidata Isa office din Dr Abdul ta kashe wayar.

Cikeda nutsuwa tayi knocking tareda bude kofar ta shiga da sallama tana kallonsa Yana zaune Yana waya da mahaifiyarsa.

Ahankali bude Baki tayi cikin nutsuwa tace”

Good morning Dr.

Murmushi ya sakar Mata Yana cewa”

Morning Dr INAYAH.

Murmushi kawai tayi tana nufar gurin Zama ta zauna itama tana duba tata wayar.

Tanajin yanda yake waya da mahaifiyarsa cikin nutsuwa da tsananin so da kauna.

Yana gamawa basu wani Bata lokaciba suka fita zuwa aikinsu.

Yauma kaman jiya sai 3 suka baro asibitin.

Yau ko firar Bata samu damar tsayawa Yi da umma ba suna sallar ishai tashige ta kwanta Dan yau din hartafi jiya Shan wahala.

Cikin kwanaki kadan tafara sabawa da rayuwar fita aiki kan lokaci da Kuma sabo da shiga jama’a sosai sbd a asibiti Dr Abdul likitan jamaa ne yanada farin Jini da mutunci sosai a idon mutane Musamman patients dinsa,

Sam baida qyama ko kasalar aiki
Sosai yake sakewa da marasa lafiya ya dubasu yanda Yakamata.

Ita kanta zuwa lokacin tayi wani irin sabo dashi hakama itama sbd aiki tareda a qarqashinsa yasa ta koya sabawa da patients tana Dan sake musu haka.

Yanayinta da yanayin rayuwarta yasa kusan da yawa asibitin suka santa duk da tana sabuwar zuwa,

Yanda take gudanar da rayuwarta yasa kusan duk akasan ba anan tayi zamaba a waje,

Gashi batada wasu shekaru masu yawa Amma har ta kammala karatunta hakama ba laifi a iya Yan ‘daidaikun dasukasan mahaifinta sunsan ita kadaice ‘ya gurin mahaifin nata,

Batada wulaqanta mutane Amma tanada Dan wuyar sabo sbd rayuwar gata da shagwabar da ita da mahaifinta yayi
Duk da hakan Dr Abdul yana taimakawa sosai gurin koyar da ita yanda zatai hulda da jama’a Musamman patients sbd yanda zatai hulda da jama’a kam Abbinta Bai koyar da itaba sbd ko jama’ar Bata wani shiga sai yanzu da rayuwarta ta Zama ta jamaa cikin lokaci qanqani.

Dr Abdulsamad kyakkyawan matashin likita ne Dan asalin Adamawa,
Qwararre ne akan aikinsa haka Kuma yasamu nasarori da cigaban rayuwa ta fanni da dama sbd aikinsa.

Aikine kawai yakeyi a Lagos din Amma ba anan yake zaune ba tun farko.

Baida Mata Kuma Bai taba aureba hakama baida wata tsayayya dayake nema
Hasalima Bai taba Jin soyayyar mace sai akan Inayah wadda ganin farko da yayi Mata yakamu da
Love at first sight.

Ganin yanayin rayuwar Inayar yasa Bai nuna mataba Kuma Bai sanar Mata ba sbd Dan sanin dayayiwa mahaifinta na career dinta yakeson fara tsayar Mata kafin komai
Dan hakan shima ya tsaya akanta yaga komai ya tafi daidai.

A bangaren gida kuwa da qarfi da yaji su Mimi sun Zama iyayenta sbd wata irin kulawa da kaunar dasuke nuna mata daga Mimi har daddyn harma da anty Hafsat.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button