GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Wani zafin gaske ne ya taso Mata daga qasan zuciya,
Duk lokacinda sunan zaid ya fado ranta Jin take tamkar Zata Kama da wuta sbd tsananin zafin kishi da baqin ciki.

Jefar da wayar tayi tareda nufar gaban madubu tafara shiryawarta.

Oil ta shafa tareda moisturizer kadan ta fesa su spray da body mist dinta ta nufi closet.

Sai after 9 tafito sanye cikin fitted long sleeve gown kalar blue sai qaramar scarf nade akanta.

Dakin umma yaganah take kokarin Isa Amma taji kaman muryan Abbinta a dining room Yana waya Dan haka ta juya ta nufi dining din.

Shi da umma yaganah ne zaune Dan haka itama ta qaraso tana cewa”

Tun yanzu anfara ware ni a gidan Nan.

Umma yaganah ce tayi Yar dariyar Jin Dadi ganin Inayar ta sake
Dama Allah Allah take MAJEED yafita gidan kafin ya dagosu su samu sugani idan zasu iya kashe zancen iya tsakaninsu.

Ita harga Allah babbar damuwarta irin fushi Mai tsanani da MAJEED din zaiyi idan yaji ‘yarsa da duk arzikinsa da zamansa busy Bai hanasa tsayawa yana ture komaiba Dan ginarda tarbiyarta tun tana jinjira har zuwa yanzu yaji sunje gidan saurayi tasan wlh ranar ransa qarshen bacin Rai zaije,
Hakama Kuma qarin abin bacin ran da baqin cikin yaji Inayar da bakinta tana fadar hannun Zaid acikin riga Yana latsa nonuwan wata,su kansu sun San ranar sai yanda Allah dai yayi dasu daga ita umman har Inayar.

Ata wani bangaren tasan Sarai Inayah Zata iya fadar hakan gaban Abbin nata.

Dan hakan yanzu ba qaramin farin cikin ganin Inayah ta sakeba tayi har Saida kusan Abbin yagane Amma dai baice komaiba har lokacin.

Breakfast sukai suka Gama ya fice zuwa aikinsa.

Yana fita Inayah ta tattaro bacin ran da baqin cikin dataketa dawainiyar boyewa cikin ranta kaman zai kasheta.

Bata wani tsaya dogon zanceba tacewa umma yaganah Zata gidansu Neesah tadawo Dan tanason Jin komai dalla dalla daga gareta idan ba hakanba zuciyarta tashiga tunani kala kala da zasu iya hallakata.

Sanin irin tsananin zafin kishi da Allah yayiwa Inayah yasa umma yaganah barinta zuwa gidansu Neesah din.

Tana barin gida batabi ta hanyar da saita bi ta anguwarsu Zaid kafin ta Isa gidansu Neesah ba Dan Bata buqatan ganin gidan ko kadan,
Jin take ta tsana gidan da anguwar gabaki daya.

Tana Isa gidansu Neesah itama Neesar na kokarin fitowa da motarta Zata gurin Inayah din.

Komawa ciki Neesah tayi da tata motar INAYAH taqarasa shigowa da tata motar sukai parking tare suka fito kusan lokaci daya.

Kallonta Neesah keyi lokacinda ta fito mota fuskarta duk babu walwala.

Cikin kulawa tace”

Hey babes,
Yaya?
Are you okay?

Wani kallo Inayah tai Mata tana qarasa Kama hannunta data miqo Mata tana cewa”

Nai Miki Kama da wadda take okay?

Kina tunanin zan Zama daidai bayan abinda idona ya ganarmin jiyan?

Ciki suka qarasa suna magana ahankali sbd rashin walwalar Inayah.

Momy na gurin dadyn Neesah Dan hakan Kai tsaye dakin Neesah suka wucewarsu.

Zama sukai Inayah na wurgi da handbag dinta da car key dinta ta kalli Neesah dake miqo Mata bowl din Candies tace”

are you for real?
Me zanyi da candies bayan ‘dacin da zuciyata take ciki.

Ajiyar zuciya Neesah tayi tana Zama cikin sautin Mai mahimmanci tace”

Maganar ‘dacin Rai ko baqin ciki bashine abinda yakamata ki fuskantaba,

Zaid dai wallahi Neman mata yake,
Nasha ganinsa da Amal a yanayi marasa kyan gani,
Nayi bibiyarsa Dan tabbatarwa Kuma na tabbatar Dan haka bawai maganar kishi ake ananba
Maganace ta ki nutsu kisan wanda Zaki aura da halayensa,

Bansan yaushe ya sauya yakoma hakan ba Amma a zahirance ya dade a wannan rayuwar da Amal Dan hakan maganar sauyawarsa lokaci daya zaiyi wuya….

Kasa magana Inayah tayi ta zubawa Neesah idanuwanta dasukai jajir sbd tsananin baqin ciki da zafin zuciya.

Cikin takaici da masifa tace”

Shine Baki taba fadanba?
Da banganiba da kaina ahakan Zaki Bari ayi auren nagama haukacewa a sonsa shikuma Yana can Yana kwanciya da wata macen?

Cikin damuwa Neesah tace”

Inayah Kona fada ba ganewa zakiyiba sbd idonki ya rufe akan Zaid,
Tayaya Kai tsaye zance Miki Zaid is sleeping with another woman?
Zaki yarda ne idan nafada?

Kalman “sleeping with another woman” shine yafi komai gigita dukkaninta Dan hakan Batasan lokacinda hawayen baqin ciki Mai qarfi suka fara gangaro mataba.

Sanyi jikin Neesah yayi ta matso kusada ita cikin tausasa murya tace”

Inayah wannan shine Namiji,
Duka wannan kadan ne idan baka nutsu kasamu mijin dakakeson more rayuwan aure dashi,

Inason aure nima kinsani sosai Amma Kuma bazan iya auren Wanda nakewa so irin hakan dakikewa Zaid ba sbd disappointments na cikin irin wannan son..

Gudu hawayenta suka qara sbd ba itace ta sawa kanta son Zaid ba Allah ne ya jarabceta da irin wannan son datake Masa,
Uwa uba ga zafin kishi datakeji Kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu.

Rarrashinta Neesah tafara yi Amma Sam takasa Jin sassauci Dan hakan ta miqe tareda daukan Jakarta da key dinta tana nufar kofa.

Binta Neesah tayi tana cewa”

Babes Ina Zaki?

Cikin qunci tace”

Zanje naji daga bakinsa meyesa zaimun hakan.

No Inayah please karki Kuma zuwa gidansa sbd kada komai ya qarasa lalacewa,
Qazantar da baka ganiba tsaftane.

Bata sauraretaba tayi gaba tana cewa”

Idan bazakiba please kibarshi a iya.

Bazan iya Bari kije ke kadaiba Kuma ai dole zanbiki,
Bani key din I will drive.

Miqa Mata key din tayi tareda budewa ta shiga kafin Neesah din tashiga mazaunin driver ta tada motar suka fice daga gidan.

Tafiya suke zuwa gidan Amma babu wadda zuciyarta Bata bugawa acikinsu,
Neesah tasan tabbas sai sun samu Amal a gidan.,

INAYAH Kuma fargaba da shakkar samun mace take agidan tareda zaid sbd wannan karon bazata iya daurewaba komai zai iya faruwa Dan kuwa zuciyarta Zata iya bugawa.

Kuma ganin Zaid da wata tamkar qarasa buga zuciyarta ne zatai.

A slow Neesah ke tafiyar itama tanata adduar Allah yasa kada su tadda Zaid a gidanma gabaki daya bare wata Amal.

MAMUH

AA MAJEED

AYSHATOUH INAYAH

MARRIAGE

LOVE/ROMANCE

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810717
Arewabooks@Mamuhgee
Suna Isa kofar gidan dake cikin jerin irin tsarin gine ginen turawa da basada gate sai harabar gida.

Parking Neesah tayi tana kallon motar Zaid data tabbatar da Yana gidan,

Kallon Inayah da idanuwanta sukai jajir tayi duk saitaji ranta yasake dugunzuma itama,

Allah yasani tafi kowa sanin irin son da Inayah kewa Zaid tunda itace aminiyarta,
Mahaifinta yasan tana son Zaid shiyasa dole shima yake kaunar Zaid
Hakan yasa duk suma suke kaunar zaid sbd Inayah na sonsa.

Wannan abin dayayiwa Inayah yasa taji duk ya fita ranta,

Takuma San tata tsanar Mai saukice akan wadda mahaifin Inayah zai Masa duk ranarda yasan abinda yayiwa ‘yarsa.

Motar INAYAH ta bude Kai tsaye tareda nufar hanyar kofar gidan
Neesah ta fito da sauri tabi bayanta tana cewa”

Inayah give him a call atleast yasan da zuwanki,
Banason asake samun…….

Maganarsu ce ta katse daidai bude kofar da Zaid yayi zai fito Amal na bayansa riqeda hannunsa tana Masa magana Kamar wata karuwa.

Ba zato ba tsammani yagansu kofar,

Qwace hannunsa yayi da sauri daga na Amal Yana kallon Inayah dake kallonsa cikin Ido da jajayen idanuwanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button