GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Matsowa yayi gabanta zaiyi magana ta girgiza Masa Kai idanuwanta na kasa riqe Mata hawayen dataketa kokarin riqewa.

Cikin yanayi na tausasa harshe da damuwa yace”

Baby babu wani abinda yake faruwa anan,
She’s just a friend…..

Cikin baqin cikin abinda yafada Amal ta matso gaban Inayah tana kallon kyakkyawar fuskarta datai jajir tace”

Banajin fa tana fahimtar abinda kake fada besides inaga ba illa bane idan friends sunje gidan juna hakama ke da qawarki ke kwana gidanku ya damu daya tambaya abinda ke tsakaninku ne……

Wani mahaukacin Mari Inayah ta saukewa Amal sbd baqin cikin abinda take nufin fada akanta da Neesah,
Sai alokacin ta juyo ta kalleta cikeda tsana tace”

Banajin nayi magana dake bare kiban amsa.

Kan Zaid din ta maida kallonta a tsananin qyamace take kallonsa zuciyarta na tafasa da wani irin baqin ciki tace”

Me take dashi daka zabi rayuwar shashanci da ita akaina?
Tafini kyau ne kokuwa?
Ita wacece?
Daga Ina ta fito?
Ina Zata?
Kudi tafimu ne?

Cikin Dan daga murya Zaid din ya katseta da cewa”

Inayah please duk ba wannan bane,
Qaddara ce…

Ahankali ta iya bude Baki ta furta”

Neesah muje.

Juyawa tayi ta wuce tabar gurin ko ganin gabanta batayi sosai.

Amal dataga ba’ayi balai da masifar dataso ayiba ta tafi da sauri Tasha gaban Inayah tana cewa”

Idan na fahimci maganarki ta qarshe da kyau kina nufin son kudi yasa Zaid da iyayensa suke son aurenki??

Kina tunanin mahaifinki fin nasa mahaifin yayi kome?

A wulaqance da zafin kishi da baqin ciki tace”

Mahaifina ba abun wasar dazaki iya hadawa da tarkacen haukarki bane so better watch out you bitch….

Da mamaki Zaid ya katseta da cewa”

Kece Zaki San abinda zakina fada Inayah sbd Alan haukar kishi ko zafin kanki karki zaga nawa mahaifin..

Murmushin Jin Dadi Amal tayi sbd dama tasan babu Wanda zai dauka zancen banza akan mahaifinsa Musamman Inayah dako Wasa ba’ayi da sunan mahaifinta Dan kuwa Bata dauka ko kadan.

Tsoki Mai zafi Inayah tasake batareda tasan ta sakeba zuciyarta na tsananta kuna tace”

Ba karuwarka kadaiba ko Kai na haramtawa fadar sunan mahaifina a bakinka bare hadasa da kowa.

Juyawa tayi a zafafe tabar gurin tareda nufar mota.

Neesah ce ta iya tsayawa qarasa musu da cewa”

Zaka iya jawa budurwarka kunnen daina shiga abinda Babu ruwanta.

Juyawa tayi itama tabi bayan Inayah dake Jan numfashi cikin mawuyacin hali tamkar Mai Asthma.
Da sauri ta tada motar ta nufi hanyar gidansu Inayah din tana adduar kada su sama Abbi a gida.

Suna Isa gida umma yaganah na ganinsu tasan ankuma kenan.

Dakin umman suka kwantar da ita suna faman kwantar Mata da hankali da kokarin ganin tadawo daidai.

Wata irin weak heart gareta da bakomai take iya dauka ba na tashin hankali ko quncin shiyasa tunda take duniya mahaifinta AA MAJEED Bai taba Wasa da duk abinda ya shafi ‘yar tasaba,
Duk wani gata da walwalar rayuwa ya wadata Yar yasa dashi,

Sbd ita yayi gwagwarmaya da Fadi tashin rayuwa ba dare ba Rana Saida Allah yabasa arziki
Duk sbd wadatar da ‘yartasane gashi lokaci ‘daya wani qaton gardin banza zai lalata Masa rayuwar ‘ya.

Daqyar suka samu ta iya dawowa daidai tayi shiru daga kwance hawayen baqin ciki na gangara daga idonta suna jiqa pillon datake kwance akai.

Tunda suka dawo Bata iya fadar kalma ko dayaba sai hawayen baqin cikin datake zubdawa zuciyarta na quntatuwa da rashin Zaid da zatai ta bangare daya Kuma gabaki daya neman fita ranta yakeyi sbd Sam lokaci daya take tsanar duk Wanda ya nuna rashin girmamawa ga mahaifinta.

Har Neesah ta wuce gida Inayah taqi cewa komai saidai kukanma ta daina saidai dukkanin fuskarta ta Gama yin ja da kumburar data bayyanarda zallar kukan datasha.

Bayan tafiyar Neesah umma yaganah tasata taje tayi wanka da sallah tayi kwanciyarta daki abincima taqi ci tace Bata buqatan komai.

Har dare Inayah din Bata fitoba har Abbinta yadawo baisan abinda yake faruwaba dayake latti yadawo gidan Dan hakan yasan sun Riga sunci abincinsu sun kwanta.

A cikin daren daqyar Inayah ta iya bacci sbd tsananin ciwon Kai na kuka da damuwar data cikata.

Gari na wayewa har 10 Abbin baigantaba Kuma baiga kirantaba Dan hakan Kai tsaye ya daga waya ya Kira wayarta amma yaji akashe.

Da Dan mamaki ya kalli wayar tareda ajiyewa ya miqe tsaye Kai
Tsaye ya nufi hanyar bedroom dinta.

A hanya ya hadu da umma yaganah zubbi na biyeda ita da tray a hannu jere da breakfast zaa kaiwa Inayah din.

Da mamaki ya kalli umman Yana sake maida kallonsa kan abincin da zaa kaiwa Inayar harda maganin da tunda safe umma yaganah tasa Dr farhat takawowa Inayah din Dan basuso ya sani.

A natse ya bude Baki yace”

Meyake faruwa anan?
Inayahn batada lafiya ne?
Meya sameta?

Ajiyar zuciya umman tasake sbd tasan yanzu kam Babu wani sauran boye boye Dan dama ciwon Inayah mahaifin natane yasan yanda yakeyi da ita Tasha magani.

Jiki amace tace”

Ciwon Kai ne taketa fama dashi Mai Dan tsanani,
Dr farhat takawo wannan maganin abata.

Manyan fararen idanuwansa ya zubawa umman batareda zallar mamakin dake ransa ya bayyanaba ko kadan sbd qwarewarsa gurin riqe emotions.

Kai tsaye dakin ya bude yashiga da nutsatsiyar sallama.

Jin muryar Abbinta yasata bude idanuwanta ahankali ta kallesa tanajin wata sabuwar karyewar zuciya da kuka na zuwar Mata.

Fuskarta da idanuwanta ya kalla take yasan Bata rintsaba kuka tayi Wanda Bai taba barin tayiba shida yake ubanta,
Uban waye yasaka ‘yarsa a wannan halin ya furta a zuciyarsa data dauki ‘daci da mamaki.

Maida kallonsa yayi kan umma data sake shiga kame kamen Inda Zata fara bayani.

Gurin Inayar ya qarasa ya tsaya akanta Yana sake kallon yanda fuskarta ta kumbura.

Zama yayi bakin gadon tun kafin yace wani Abu ta fashe da kuka tana cewa”

Abbi zaid yaci Amanata….

Ahankali yasake ajiyar zuciya sbd yasan zaa Rina ganin yanda Inayah take tsananin sonsa tun farko.

Ahankali ya Kai hannu ya zari tissue dake gefen gadon yafara share Mata wahaye Yana sake sakin ajiyar zuciya kafin ya kalleta cikin kulawa da kwantar Mata da hankali yace”

Ya Isa haka,
Tashi ki wanke fuskarki kizo kici abinci da magani zamuyi maganar daga baya.

Bata musawa Abbinta Dan hakan ta miqe tsaye sanyeda Riga da wandon bacci masu santsi ta nufi toilet.

Sunanan zaune duka ta fito ta zauna gefen abbin Ta karba abincin tafara da tea Mai zafi da umma yaganah ta dafa Mata da kanta.

Tana cikin cin abincin aka Kira wayarsa yamiqe ya fice daga dakin yabarsu.

Kallonta umma yaganah tayi tana cewa”

Inaga Inayah ki hakura da Zaid tunda dai da alama na Jin nasiha ko magana zaiyiba,
Nifa da kaina tun ranarda abin Nan yafaru kullum saina kirasa na Masa nasihu da nuni kan hanya Mai kyau Amma shine Dan baida niyar daidaituwa kullum Ina Masa nasiha yanacan Yana cigaba da aikata alfasharsa,

Tsakani da Allah da saninka dai auren mazinaci baida wata riba ko kwanciyar hankali,

Tunda baijiba Kuma baida niyar dainawa ki hakura ki cirewa zuciyarki ki dangana Allah yakawo Miki wani mijin Wanda yafisa kyawawan halaye..

Qala Inayah Bata iya cewaba saima danne ‘dacin dayake taso Mata takeyi tana jinjina kanta.

Duk abinda umma yaganah ta fada akan kunnuwansa Dan hakan take ya dauki hannun abinda yake faruwa.

Fasa juyowa yayi ya juya ya komawarsa.

Gabaki daya wunin qin Kunna wayarta tayi sbd ko sunan Kiran Zaid Bata qaunar yi akan wayarta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button