GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Tabbas tasan yanzu kam Abbinta dole zaisan komai Kuma hakan na nufin aurenta da Zaid ya Gama wargajewa Dan hakan zuciyarta tagama raunana,
Wuni tayi tana danne hawaye da baqin ciki.

Haka takuma kwana batareda Zaid ya biyota bada hakuri ba hakama koda ta kunna wayarta bataga kiransa ba Dan hakan taqara himmar kokarin fiddasa cikin ranta.

Ga Abbinta shima baice musu komaiba sai umma yaganah dayayi magana da ita ta zayyane Masa komai da komawarda Inayah takuma Yi gidansa.

Kwana biyu shiru ba Zaid ba wayarsa hakama Abbinta baice Mata komaiba duk saitabi taqarasa shiga wani hali.

Ta bangare daya basu daina shirye shiryen tafiya Nigeria ba Dan hakan takejin ko maganar aurenta da Zaid din tana Nan shiyasa wani bangaren takejin kaman zasu shirya komai ya wuce,taqi fidda rai.
Arewabooks for more pages

https://arewa-one.vercel.app/chapter?id=634d93b4bf002b318122db87

MAMUH

LOVE/AYSHATOUH INAYAH

ROMANCE/AA MAJEED

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810718
Arewabooks@Mamuhgee
Washe gari da safe tana zaune dakinta tana waya da Dr farhat kan itama Nigeria zataje saiga zubbi da soqo.

Sai data kammala wayar ta kalla zubbin tana cewa”

Yes zubbi?

Am Mr Zaid ne yazo Yana guestroom Yana buqatan ganinki.

Kallon bakin zubbin daya isar da sakon takuma Yi kafin ta Dan jinjina Kai ahankali tace”

Ok am coming.

Juyawa zubbin tayi ta fice tana cewa”

Ok Ma.

Zubbi na fita ta rintse idanuwanta tanajin yanayinta na sauyawa zuwa damuwar abinda yakawo Zaid din Kuma.

Bude idanuwan tayi tareda miqewa tsaye ta nufi gaban mirror takuma kallon kanta.

White Alexandra chiffon top ce ajikinta Mai tsada sai sky blue Levi’s ripped jeans,
Kanta qaramin farin silky scarf ne a daure,

Ko turare Bata buqatan qarawa sbd Qamshin dake tashi jikinta ahankali already Dan haka juyawa kawai tayi ta fice daga dakin ta nufi hanyar palon tana jin gabanta na faduwa kaman yaune ranar farko da Zata fara haduwa da Zaid din.

Tun kafin ta Isa take Jin muryarsa qasa qasa Yana waya Dan haka saita dakata Jin abinda yake fada a wayar..

“Nafada Miki karki Kira idan nafita daganan din zan kiraki,
Meyesa bakya ganewa ne Amal?
Abbinta ne Allah kadai yasan abinda yayiwa dad dina da duk yabi ya rude yasani zuwa Bata hakuri dole,

Nafada Miki zan kiraki idan nafita Dan haka banason damuwa,
Karki qaramun pressure akan Wanda Abbin Inayah ya dorawa dad shikuma ya Dora mun okay??

Kashe wayar yayi Yana sakin qaramin tsoki Dan Amal dinma gabaki daya tagama fita ransa Dan kuwa tsakanin jiya zuwa yau dad dinsa duk yabi yagama haukace Masa akan abinda yayiwa Inayah,

Shi kansa yasan Yana Sonta Amma Kuma bayajin zai Dora soyayyar Tasu akan burika ko ra’ayin iyayensu Wanda ita Kuma gareta da mahaifinta ganin sukeyi komai suke zasu iya samunsa sbd dukiya kokuma wani ikon dasuke gani.

Bata taba Jin Zaid yafita ranta kwata kwata ba sai yanzu din dataji irin fassarar daya yiwa mahaifinta da ita,

Wani sanyayyan numfashi ta sauke ahankali tareda qarasowa cikin palon batareda ta iya kallon fuskarsaba Dan Zata iya Masa tsana Mai girma.

Kan Luxury sofa dake gefe ta zauna tana ajiye wayarta gefenta ta waiwayo ta kallesa Kai tsaye tace”

Yes?gani ance kanason ganina?

Zuba Mata idanuwa yayi yanajin Sonta na qara Masa yawa Amma Kuma yanda mahaifinta yayi amfani da dama ya rikita nasa mahaifin akanta yasa yaji son nata na komawa fushi Dan haka shima ya Dan kame fuska sosai zaiyi magana ta katsesa da cewa”

Please Zaid idan hakuri zaka bani banajin akwai buqatan hakan sbd na Riga na yarda da matar mutum kabarinsa ne so ba buqatan mu…..

Inayah kina tunanin ahakan zamuyi auren duk abinda ya hadamu Zaki kwasa ki fadawa mahaifinki shikuma Yana yiwa nawa mahaifin barazana kokuma nuna iko akan wani abin?

Kina tunanin abinda kike samu koyaushe da kina gidanku shi Zaki samu a rayuwar aure?

Look bazan yarda Kuma bazan dauka ba rashin girmamawa ga iyayena da mahaifinki keyi sbd koba komai nawa iyayen sun girma naki mahaifin ko yayane…..

Miqewa tsaye tayi tana kallonsa da mamaki akan fuskarta tace”

Zaid Dan Allah katafi bana buqatan ganinka,
Kaje kaji da kunyar dayake dawainiya dakai na abinda kamun….

Nace Miki inajin kunyar abinda nayi ne?
Kinga alaman kunyar hakan ataredani ne?
Sbd me zanji kunya?
Sbd Ina tareda wadda tasan damuwana shine zanji kunyarki?

Nayi tunanin kece wadda yakamata tafara duba yanayin Dana shiga tun wancan lokacin Amma kika nunan Sam bazaki iya take doka ko sharadin Abbinki ba,
You can’t do sex before marriage,
You can’t do this sbd Abbi,
You can’t do that sbd Abbi,
You can’t,you can’t, you can’t,duk sbd Abbinki,
Abbinki Annabi ne shi da bazaa…..

Wani wawan Marin da batasan yaushe tasamu qarfin yinsaba ta sauke Masa tana Masa kallon zallar tsana Bata iya furta komaiba sai”

I hate you Zaid,
Na tsaneka sosai,
Ban tsaneka sbd kaci Amanata ba sai sbd kalamanka akan mahaifina,

Dan haka kaje dakai da wanda yaturoka ban hakuri ku daina wahalarda kanku akan Abbina sbd Abbina nada business daku ne kawai sbd Ni
Ayanzu Dana cirewa zuciyata Kai Abbi ko Inda kuke Kuma bazai sake kallaba,
So please Mr Zaid can you kindly see your self out…” Taqarasa fada tana nuna Masa hanyar kofa idanuwanta jajir.

Wani shegen murmushin takaici da baqin ciki ya sake kafin ya kalli kofar yakuma waiwayo ya kalleta yace”

Bakomai bane agurin ‘ya Dan ta gada ubanta,
Mahaifinki ma ya gagara Zama da mace tayaya kema ake tunanin kiyi aure ki zauna da wani?…

Wata irin tsawa Mai qarfi umma yaganah ta sakar Masa tareda Kiran sunansa da qarfi cikin tsananin fushi da bacin rai.

Kofa ta nuna Masa tana cewa”

Zaka iya ficewa rashin ‘da’an ya Isa haka.,

Juyawa yayi ya nufa kofa yanajin sautin kukan Inayah data sake na tsananin baqin ciki.

Wani sanyi da damuwa yaji aransa lokaci daya,
Shi mutum ne da Baya Bari idan anmasa saiya rama,
Dan hakan ramawace yayi akan rashin da’ar da akaiwa mahaifinsa,
Yanzu daya Rama yaji daidai Dan haka zuwa gobe yasan ta sauka zai kirata a waya ya lallabata su shirya Kuma yasan idan ta shirya dashi dole yaganah dama Abbinta su shirya dashi.

Wani irin kuka Inayah keyi tun daga qasan zuciyarta takejin zafi da ciwon abinda Zaid din yayi Mata.

Janta umma yaganah tayi sukai ciki saidai abinda basu saniba shine MAJEED na gidan yadawo sbd wasu baqinsa dazasu samesa gida yakuma ji duk abinda suke fada.

Sam har baqinsa sukazo suka tafi har dare Bai nuna musu yasan abinda yafaruba sai washe gari ya sanarda umma yaganah maganar auren Babu Dan hakan da ita da Inayah din zasu Nigeria hutu sbd Inayah ta sake karta shiga damuwa sosai.

Bayanda Abbinta ya sanar da ita da kansa ba maganar aurenta da Zaid tayi kuka sosai sbd Tasan yanzu batada ranar wani auren kuma Dan haka da akace Nigeria zasu Bata wani damuba saima matsuwa datai su tafi ko Zata samu sassaucin tsananin damuwar data shiga.

Neesah hankalinta ya tashi Jin tafiyarsu Inayah din Nigeria Dan batada qawa ko daya bare aminiya idanba Inayah ba,

Taso binsu Nigeria din Amma momynta tace ba yanzu sbd sunata kokarin ganin tafara aikine yanzu,

Itama Inayah sbd Nigeria da zasu koma yasa batai saurin fara aikinba saita dawo tukuna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button