GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Cikin kwanaki qalilan aka Gama Shirin tafiyarsu Dan haka Abbi na wucewa Singapore suma suka wuto Nigeria itada Umma yaganah da zubbi.

Saukar dare sukai a Murtala Muhammed international airport dake Lagos.

CM Nuraddeen da kansa ne yazo daukansu daga airport cikin lafiyayyar Cclass dinsa.

Cikin kulawa sosai yake musu barka da sauka tareda gaida umma yaganah cikin girmamawa.

Inayah datake amatuqar gajiye ma cikin Dan yanayi na sanyin murya ta gaidasa kafin suka shiga mota suka Kama hanyar gidansu.

Orchid Est Ikeja GRA suka iso Lafiyayyan qaton gidansu Wanda suna can abbin ya mallakesa.

Akwai Mai aiki daya sai securities dasuka sama a gidan Dan haka CM na ajesu ya wuce gidansa Dan dare yayi sosai.

Suna tareda gajiya dan haka basu wani tsaya komaiba kowannensu ya nufi Inda ya tabbatar Nan ne dakinsa sbd yanayin gyaransa.

Bedrooms hudu ne a qasa kowanne da toilet na Inayah ne kawai keda closet room na musamman sbd sanin yanda tsarin dakinta na Australia yake.

Dakin umma yagana ma babba ne da toilet dinsa aciki Babu abinda babu na Jin Dadi da kwanciyar hankali acikinsa.

Dakinsu zubbi Yana daga baya ta hanyar backdoor na kitchen.

Shi Abbi hanyar shigowarsama daban take saidai daga palonsa zuwa nasu akwai kofar wadda ta Nan zai ringa shigowa cin abinci a dining room dake babban palon gidan.

Babu Wanda yayi yunqurin komai bayan wanka da sallah dakuma bacci dayake cin Inayah Dan Sam acan Bata doguwar tafiya irin wannan.

Wanka tayo tafito daga toilet daure da blue towel tana gyara qaramin towel dake daure akanta ta nufi gaban maduba tana goge jikinta ahankali Amma da Dan sauri sbd sallolin dake kanta.

Body mist kawai ta shafa tabar gaban madubin ta janyo daya daga jerin akwatinan datazo dasu ta bude ta dauka Riga da wando na bacci masu Dan kauri ta saka tareda jallabiyanta na sallah ta saka.

Fitowa tayi tana tafiya Kaman qaramar baby ta qwalawa zubbi Kira.

Allah yasa Salimat na kitchen tana musu warming abincin data girka musu tun dazu
Itace taji Kiran ta fito tana cewa”

Ma, zubbi na daki wanka takeyi.

A kasalance Inayah ta kalleta tace,

Dama ke zance ta kirawo,
Inane gabas??
I mean alkiblah.

Nuna Mata tayi tana cewa”

Nan Zaki kallah Ma.

Gyada Kai kawai tayi tareda juyawa ta koma tana Jan qafa.

Sallolin dake kanta tayi duka
Tana idarwa Bata tsaya adhzkar sosaiba ta miqe ta cire abayar ta fada dan bubbuga gadon alamar kakkabawa kafin ta fada tashige bargo take bacci Mai qarfi ya dauketa.

Dama kusan koina na gidan gyare yake fes daga qamshi sai sanyin AC ke tashi koina.

Umma yaganah ce dai data Gama salloli da wanka ta Dan huta kafin tasa suka Kai Mata abinci a dakinta taci Salimat ta tattara gurin kafin takuma brush ta kwanta.

Inayah kam Salimat na zuwa dakinta so daya ta dakatar da ita akan kada su sake zuwa tadata su dameta sai gobe Babu abincin da Zata ci a daren.

Washe gari qarfe goma na safe ta fito a shirye tsaf cikin Riga da wando marasa nauyi na zaman gida fuskarta fresh sbd isashen baccin data samu Mai nutsuwa.

Wayarta ce a hannunta wadda take kashe tun ranarda Zaid yayi Mata Kiran farko bayan rashin mutuncin dayazo yayi Mata har gida.

Tun a daki ta zare layin sbd Baida amfani anan.

Palon take kalla koina tana Yana tsarin gidan da komai na gidan da yayi Mata daidai da can data baro,

Salimat ce datake bin kyakkyawar surarta data Gama bayyana a shape na yanayin kayan jikinta
Cikin girmamawa da sakewa tace”

Barka da fitowa Ma.

Sai alokacin Inayah ta juyo tayi Mata kallon tsaf fuskarta a sake sosai tace”

Good morning Ms…..????

Salimat Sharif”

salimat ta qarasa Mata.

Murmushi Mai kyau Inayah ta sake tana cewa”

Salimat ki kirani da Inayah,
Just Inayah okay?

Yes Ma.

Dakin umma yaganah ta nufa tana cewa”

Where’s zubbi?
Ina buqatan Nigerian simcard.

Dayake akwai wayar Salimat a kusa ita Inayah din ta karba ta saka numbobin Abbinta ta Kira.

Yana tareda abokan aikinsa Amma Yana ganin Kiran Salimat daidai wannan time din yasan Inayah ce Dan haka Kai tsaye ya miqe tsaye tareda daukan wayar ya fice zuwa office dinsa.

A natse ya dauka da cewa”

Yes,Ms Salimat.

Wata qaramar dariya Inayah ta sake ahankali Tana cewa”

Abbi kasan nice ba Salimat ba shiyasa ka dauka Kira daya.

Murmushi ya sauke Me qaramin sauti kafin yace”

Meyasa Zaki kirani da layin?

Ba layin Nigeria a wayarmu duka and Abbi Ina buqatan abubuwa da dama kamansu kayan wankana da….

Ok,ok,ya Isa
Ya kuke?
Kinajin nutsuwa da yanayin gidan?
Ina tareda mutane yanzu I will call you back anjima okay?

Okay Abbi” ta furta cikin rashin Jin dadin samun lokacinsa.

MAMUH

AA MAJEED

INAYAH

LOVE/MARRIAGE

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[10/20, 1:31 PM] +234 808 711 8630: 19
Arewabooks@Mamuhgee
Breakfast sukayi na Lafiyayyan abincin da rabon umma yaganah dataci sa harta manta,

Soyayyar doya da egg sauce dataji Qoda da veggies salimata tayi musu sai chips da plantains da ruwan tea masu Dadi Amma tea kam zubbi ce data San zabin Inayah din akan tea ta dafa.

Bataci doyarba sbd Bata wani Saba da itaba chips din kawai taci da sauce sai tea suka koma Palo ta zauna tanajin kadaicin Neesah da batada wayar kiranta.

Da Rana gabaki daya familyn gidan CM sukazo gidan Yi musu barka da zuwa Dan haka gidan nasu yake cikeda Baki duk da suma ba wai wani yawane dasuba,

Matansa ne biyu haj Raliya da Anty Hafsat sai ‘yayansa shida,
Biyu maza hudu Mata.

Babbar yarsa mace ce kusan sa’ar Inayah saidai tafi Inayah girman jiki sosai ta tsayi data jikin sbd Inayah rayuwar turaice atareda ita tana dieting sosai ba koyaushe takecin abinciba kokuma cin komai tasamu Anyhow
Dan hakan ita tana maintaining jikinta sosai sbd kaman yanda tafada so take jikinta yazama abinda zai qara haukatar Mata da mijinda Zata aura,

Tanason rayuwa shiyasa takeson Allah yasa ta aura mijinda yafita sanin cikakkiyar rayuwa.

Da farko zuwan baqin da hayaniyar da gidan ya dauka yasa taji kanta kaman zai fara ciwo sbd kwata kwata basu wani Saba da ganin baqi irin haka gidansuba musamman da Yara,

Ko gidajen friends nata da abokan hulda acan gida dayane take zuwa Mai Yara suma yaran biyu ne Kuma basada hayaniya kaman wainnan.

Umma yaganah kuwa Murna da farin ciki Kamar me sbd rayuwarta ta saba da hidimar mutane da hayaniyarsu Amma tunda suka bar qasar Takoma rayuwar kadaici ba mutane a rayuwarsu dagasu saisu sai qaidajjun mutane suma kusan duk turawane,

Hakan ne yasa cikeda Murna da farin ciki ta tarba baqin sunata gaggaisawa da firarraki duk duk da ita uwace garesu sai firar ta Zama ta mutunci ce sosai Dan kuwa bakowane yasan ba umma yaganah dince mahaifiyar AA MAJEED ba.

Inayah ma dole ta zauna tana Dan yaqen dole acikinsu sbd rashin sabo.

Matan Cm din kuwa kowaccensu kokarin jan Inayah take ajikinta sbd basu taba dauka haka Inayah din tasa takeba a fili,

Sunsha ganin hotunanta a media sbd mahaifinta da kowa ke mamakin son ‘yaya irin nasa dayake fifita ‘yarsa akan komai dakeda mahimmanci shiyasama duk Wanda yake hulda da AA MAJEED saiyayi Neman hoton ‘yarsa da yake ganin tafi sauran ‘yaya,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button