GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Sundada hotunanta da dama musamman na kammala karatunta dasuka Dan Yi yawo a tsananinsu sbd CM yaje taron kammalawar tasu har can qasar.

Haj Raliya da ake kira da Mimi mace ce da kusan komai nata take yinsa akan riba da qaruwa dakuma son yin suna acikin masu arziki,

Tunda dadewa takejin inama AA MAJEED nada Mata da duk yanda zatai saitayi sun Zama aminanai na gaske sbd abokanan huldarta duk matan manya ne,matan Naira.

Data Gama fahimta daga mijinta tako Ina AA MAJEED baida ra’ayin mace ko kadan yasa tasawa ranta burin ganin A MAJEED din ya aura yarta Safnah, wato babbar ‘yar CM din,

A MAJEED ya Haifa Safnah sosai tunda kusan tsarar ‘yarsace Inayah Amma ita agurinta shekaru ba komai bane idan har zaka sama miji cikakke,tsayayye,hadadde Kuma Wanda ya kafu kaman AA MAJEED.

Wannan burin nata yasa suna zuwa gidan taji duk duniya ba Wanda takeso irin Inayah sbd tasan ta hanyar yarsa komai zai iya faruwa.

Safnah Batasan burin mahaifiyarta ba sbd har lokacin karatu takeyi Kuma tanada saurayinta dasuka dade tare Dan haka Bata wani San menene yake faruwa Aran mahaifiyartaba.

Anty Hafsat ma tana ganin Inayah taji tana kaunarta saidai batai saurin saka wani buri ko qudirin komaiba akan Inayar
kaunace ta Gaskia ta shigeta ta ‘yarinyar data tashi a hannun ubanta batareda uwaba.

Ganin yanda suke nuna kulawa da kaunar Inayah sosai yasa umma yaganah sake Jin Dadi tana Kuma girmama mutuncin iyalan CM din.

Safnah ce take Jan Inayah din fira wadda take Dan amsawa sama sama sbd gabaki daya hankalinta yakoma kan rashin layi akwai wayoyin datakeson yi.

Wani qaramin lunch party sukai a gidan sbd abinci kala kala da aka dafa tareda snacks dasu Mimin sukazo dasu.

Bata saba da yaraba Amma Yar qaramar babyn Anty Hafsat da Bata wuce 3yrs ba Mai suna Siyama tashiga ranta sosai hakan ne ma yasake taimakawa tasake Dan sakewa dasu.

Da daddare ma saida sukai dinner kafin driver yazo daukansu suka bar gidan.

Umma yaganah saidai taiwa yaran kyautar kudi sbd basuda wata tsarabar badawa duk sai Bataji dadiba sbd ita mutum ce Mai kyauta Musamman yanzu da akazo takanas Dan Yi musu barka da zuwa.

Hakan yasa taji tana buqatan siyayyan Yan abubuwa su ajiye ko Dan masu zuwa din.

Inayah kam kanta dake Mata ciwon gajiya da hayaniyar da aka wuni anayi ta dafe ahankali ta nufi dakinta tayi wanka da ruwan dumi tareda fitowa ta saka kayan bacci ta kwanta.

Bacci ne ya dauketa take sbd tagaji sosai Dan Bata saba hayaniya irin wannanba.

Washe gari doma sunyi da Safnah Zata kawo Mata layuka har biyu saidai Kuma dole zasuje ayi Mata register din layin Dan haka suka fita zuwa MTN office har umma yaganah Dan itama tana buqatan layin.

Safnah ce tazo da driver din gidansu shine yakaisu akai musu register din bayan sun siya manyan layuka masu special numbers.

Suna baro MTN office Inayah taso suyi yawo taga garin Amma umma yaganah tace su koma gida sbd Abbinta baisan da fitarsuba ko yanzu din.

Haka suka dawo gida badan Inayah din tasoba.

Safnah Bata wuceba anan tasake yimusu wuni sbd Daddynta dayace ta Dan zagaya da INAYAH din tafara sanin gari saigashi baai fitar a sbd Abbinsu dabai saniba.

Inayah daqyar taga mintunan da aka dibar Mata sun cika da sauri ta saka layin tareda kunna wayar dama tun acan sun biya kudi an saka Airtime a layukan.

Numbern Abbinta akanta take Dan haka Kai tsaye shi tafara Kira.

A kowane yanayi ‘yarsa tazo Masa Allah na basa ikon ganeta ta hanyoyi da dama sbd sanin dayayi Mata ciki da Bai.

Lokacin Kiran ya duba ya auna yaga qarfe Tara da mintuna shida Yakama yanzu a Nigeria Dan haka yasawa ransa Inayah ce Mai Kiran.

A natse ya dauki wayar dake gefensa ajiye cikin palonsa Yana kallon wani conference,
A hankali cikin nutsuwa da kulawa yace”

Hello,Aslm alaikum.

W slm, Abbi kana planning yafemu ne?

Wani silent murmushi yasake Yana cewa”

Yes Mana tunda Inayah ta girma tafara iya zuwa gidan saurayi.

Wani qaran shagwaba ta sake tana cewa”

Abbi tsautsayi nefa,
Kuma banama son tunawa ko kadan sbd Abbi haryanzu fa nakasa daina tuna abinda nagani a gidan,
Hannuwan Zaid fa acikin rigar wata Yana taba No…..

Buge Mata Baki umma yaganah dake gefenta tayi Yana harararta qasa qasa tace”

Bazakiyi hankaliba ko Inayah?

Abbin kuwa shiru yayi na wasu sakanni kafin ya Dan gyara murya ahankali Yana cewa”

Ya wuce,
Daga yanzu karna Kuma Jin kin sake fadan haka da bakinki okay??

Bakisan kinfara girma bane?
Likita guda fa ake magana,
Dr INAYAH A MAJEED..

Jin dadin sunan daya kirata dashi yasata dariya tana cewa”

Yes,ok Sir.

Qaramar dariya Mara sauti yasake Yana cewa”

Yaya umma yaganah?
Ya kukejin yanayin?
Are you okay with everything there?

Numfashi ta sauke tana cewa”

Yes Abbi ba laifi komai yayi munata kewanka kawai,
Jiya CM’s family sunzo
We had a great day with them,
They’re nice and lovely.

So you like them right?

Yes Musamman Little Siyama Abbi she’s so cute,
Dama ace inada qanwa irinta danaji Dadi.

Tsit umma yaganah tayi tareda abbin sbd idanba Inayah ba lokuta da dama waye ya Isa yaringa Masa irin maganganun Nan haka?
Amma ita tausayima take basa duk lokacinda tayi magana irin hakan,

Tunda tafara wayo tun tana qanqanuwarta Bata taba Masa maganar Inda mahaifiyarta takeba sbd sanin yanda ya tsana kalmar,

Kwata kwata ta rufe babin tambayar mahaifiyarta kokuma yin maganar ma gabaki daya sbd kaucewa bacin ransa,

Ta Riga ta sakawa ranta shine uwarta shine ubanta,
Batasan Dadi ko kaunar uwa yanda takeba saidai ta uba Dan hakan Bata taba kafewa aranta Zata iya batawa Abbinta Rai sbd ambatar Inda mahaifiyarta take Dan kuwa koma menene ya rabata da mahaifiyarta tasan bamai Dadi bane sbd yanda mahaifin nata ya tsani koda Wasa a ambata kalmar mahaifiyar Inayah agabansa.

Umma yaganah ce Jin yayi shiru tasan kalmar ta sosa ransa Dan hakan tayi saurin saka baki a zancen da cewa”

Inayah wai kekam yaushe zakiyi hankali ne?

Ina maganar qanwa yanzu a gurinki ai saidai ki bada himma ki nutsu kisamo wani Natsatsen mijin ayi Miki aure ki Haifa ‘yayanki irin Siyama din,
Abbinki ma Kinga kin Haifa Masa jikoki acikinsu zai darje amaryarsa dal a leda.””

Da dariya ta qarasa zancen
Itama Inayah dariyar tayi tana kwatanta ranarda Zata Haifa nata ‘yayan,

Irin qaunar da Abbinta ke mata zatawa nata ‘yayan
Suma tasan Abbinta zai sosu tunda ‘yayan Inayarsa ne.

Haka kawai burin ganin hakan shima ya shigeta a fili ta tace”

Idan na haihu shikenan Abbi ka Zama grandfather?

Dariya yasake ahankali Yana cewa”

Inayahn Abbi ma shikenan ta Zama uwa ko?

Dariya tasake tana sake cewa”

Abbi zanji kunya idan kana fada da kanka fa.

Ok ya Isa haka Time to sleep,
Umma yaganah taje ta kwanta Inshallah zuwa gobe Zata fara fita asibiti.

Ok Tom Allah ya kaimu Saida safe.”” Cewar umma yaganah daya fadawa maganar.

Amin, goodnight Abbi.

Goodnight Inayah.

Suna Gama wayar Inayah ta saka numbern Neesah ta Kira.

Neesah ma tana ganin numbern Nigeria tasan Inayah ce Dan haka da sauri ta dauka tana cewa”

Meyesa kika dauka lokaci kafin ki Kira??

Dariya Inayah tasake tana miqewa daga palon ta nufa dakinta Dan tasan doguwar Hira zasuyi da Aminiyar tata.

Aikuwa sabuwar Hira suka dasa Dan tunda suka hadu basu taba tafiya Mai tsayin data rabasu ba irin wannan.

Sai dare sosai ta Gama wayoyinta ta miqe ta nufa toilet tayo wanka tazo ta kwanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button