GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

Mun wuni lfy umma yaganah?

Wata jarabawa kokuma ace lalura datake kansa tsawon shekaru shine Baya kallon mata kallon daya wuce daya zuwa biyu,

Sam ya dade da rufe shafin mace ata kowanne fani na rayuwarsa bayan ‘yarsa,
Duk huldar aiki dazata hadasa da mata Baya wani maida hankali sosai akansu Wanda Kuma kusan ba kowane ya fahimci hakanba tunda dama shi ba mutum ne Mai sakewa mutuneba shiyasa baa wani ganewa
saidai umma yaganah da Inayah dasuka Sansa ciki da Bai sune sukasan babu macen dayakewa kallon daya wuce biyu zuwa uku,

Umman ma haryanzu idan yayi mata kallo daya zuwa biyu koda suna magana ne Baya qarawa shiyasa da yawa idan kana Masa bayani saika dauka hankalinsa Baya kanka and yafi maida hankali kan wani abun daban ko waya haka Amma Kuma ahakan yafi fahimtar bayanin da ake masa.

Wainda suka ‘dan Sansa da kadan daga halayensa idan suna magana dashi sukaga Baya wani abun daban ya tsaya yana saurarensu to kuwa sun San tabbas Bayada niyar saurarensu ne,idan kanason Kama mutuncin kanka saika dakata kabar maganar Dan ba lokacinta zaiyiba.

Zama sukayi dukkaninsu a dining Inayah ta zubawa kowa abincin kafin Takoma ta zauna itama bayan ta zuba nata,

White rice ce da chicken vegetables with scrambled eggs.

Suna fara cin abincin Inayah ta kalli abbin dayakecin abincin a natse kunnuwansa na sauraren sautin yanayin cin abincinta take ya fahimci akwai maganar datakeson yi.

“Abbi” ta furta sunan ahankali cikin kulawa da bayyanarda ‘yar shagwaban data taso acikinta.

Kallonta umma yaganah tayi cikin kulawa ya katseta da cewa”

Ba yanzu ba Inayah,
Bakiga Abbinki yanacin abinciba?
Surutu lokacin cin abinci baida amfanin kinmatane?

Marairaice fuska tayi cikin son fadar abinda yaketa nuqurqusanta Kuma tasan Idan ba fada Masa tayiba Dad din Zaid yayi Masa zuwan Kai tsaye da bazata ransa zai baci akan da sanin ta akazo maganar,

Bazata iya daukan fushi ko bacin ran abbintaba akanta Dan haka Kai tsaye takuma kallonsa bayan tayiwa umma yaganah fuskar riqon tabarta tayi magana.

Abbi Dad din Zaid Yana gari yazo fa….

Ahankali ya qarasa hadiye sauran abincin dayake bakinsa ya dauki ruwa mara sanyi sosai dake gabansa cikin glass cup yasha ya ajiye sauran ya dauki tissue Saida ya goge bakinsa ya dago da manyan idanuwansa ya kalleta hankali kwance yace”

Yes,Uhum?
Dad din Zaid Yana gari zan Masa wani Abun ne?
Gurina yazo ne?

Abbi dama gurinka ne zaizo kuyi magana,karyazo ne baka saniba ranka ya baci Abbi shine nafada maka Kuma banice nace suzoba Abb…

Umma yaganah ya kalla Kai tsaye da tambayar

“Kinsan da hakan ne umma yaganah?
Ta sanar dake Zata basu Daman zuwa neman aurenta?

Ajiyar zuciya umman ta sauke cikin sanyin jiki sbd Inayah dai Bata gane kwaba,

Kallonsa take cikin sanyin jiki tace”

Ta sanarmun da mahaifin nasa zaizo Amma na kaina na Kira Zaid din nace su dakatar da zuwan sbd Jan magana daya koyaushe baida amfani tunda dai anbasu auren Inayar
Yin auren ne dai tunda anfada musu ba yanzuba na rasa naci irin na ‘yaran yanzu tunda ba cewa akai a gaban zaa fasaba…

Jin shirunsa Yana saurarensu yasa dukkaninsu suka Sha jikinsu sbd sanin hakan abinda yake nufi,

Dukkaninsu sun fahimci bacin ransa akan hakan shiyasa suka sake yin wani tsamo tsamo.

Cikowa idanuwan Inayah sukai da hawaye batareda ta saniba cikin sanyin murya da sigar ban hakuri ta taso tadawo gefensa tareda Dafa hannunsa ahankali tana cewa”

Abbi Banice nace suzoba wlh,
Nayiwa Zaid din maganar kada dad din yazo Amma baijiba,
Abbi wlh bani bace…

Batareda ya kalletaba yace

“It’s okay saiyaxo Ina jiransa.

Miqewa yayi tareda kallon umma kadan yace”

Mu kwana lfy umma yaganah.

Allah ya tashemu lfy” tafada itama tana bin bayansa da kallo ranta babu Dadi da yanayin,

Babbar matsalar basa wani gane bacin rai ko fushinsa bare kasan halinda kake ciki shiyasa koyaushe irin wannan kuskuren yafaru sun ringa Kara kaina kenan gurin samun sanin yanda ransa ya dauki Al’amari.

Bayan barinsa gurin Kallon umma yaganah Inayah tayi da raunannun idanuwanta zatai magana umma ta tareta da cewa”

Inayah meyasa kikai maganar Nan?
Maimakon ki dakatar dasu Zaid din shine Zaki Kuma kawo maganar gaban mahaifinki bayan kinsan bayason maimaicin zance,
Anyita maimaita zancen Nan Kuma kinfi kowa sanin mahaifinki magana daya yakeyi akanki meyasa bazakiyi respecting hakanba?

Yanzu gashinan zakiwa kanki Dan kuwa Abbin zai iya Hana auren gabaki daya yace su hakura suje su nema wata su aura idan sunaga bazasu iya jiranba
Kinga kuwa wa garin ya waya.

Batada abin fada sbd jikinta daya Gama mutuwa da yanayin mahaifinta daya qi barin su gane yanda ya karbi zancen.

Cikin sanyi ta dauki orange juice din dake gabanta ta Sha sosai ta aje cup din sbd bazata iya cin abincinba Kuma.

Miqewa tayi tareda yiwa umma yaganah Saida safe ta wuce dakinta itama.

Itama umman kammalawa tayi ta miqe tabar dakin ta dauki sauran abincin datasan zai moru takai fridge ta jera kafin ta wuce nata dakin zubbi tazo ta tattara gurin ta gyare Takoma dakinta itama.

Bayan isarta daki ta Gama duk abinda zatayi ta hau makeken gadonta ta kwanta tareda daukan wayarta ta saka Kiran Zaid.

Daukan wayar yayi tun kafin yayi wata magana tace”

Zaid please ka dakatar da zuwan dad gurin Abbi banason cigaba da Bata ransa akan maganar wani auren yanzu,
Nidai gskia mu haqura abari sai lokacinda Abbina yace koma yaushe ne zamu jira
I don’t want to stress him with unnecessary abubuwa kaman hakan tunda yace ajira kawai ajira
Dad dinka yakoma please…

Inayah are you out of your mind or what?”” yafada cikin Dan daga murya.

Kinajin kanki da abinda kike fada kuwa?
Dad ya taso all the fuckin way from Nigeria yazo kice yakoma sbd kada a dama Abbinki?
Are you for real?Kinajin kanki kuwa?

Zaid please karmu batawa juna Rai abanza mubar maganar auren Nan yanzu sai gaba….

Datse wayar yayi ya kashe gabaki daya ya jefar gefensa Dan zuciyarsa tafara baci sosai da yanda koyaushe Abbinta shine gaba shine yafi kowa mutunci,yanaji kaman mahaifinsa take kokarin ciwo mutunci Dan haka cigaba da wayarsu yanzu zai iya hadasu fada sosai shiyasa ya kashe din.

Inayah ma wayar tabi da kallo cikeda mamaki da Dan takaici,
Ita Zaid yake kashewa waya yau?
Wai kodai bayan matsalarsa ta buqatan aure yanada wata matsalar ne da ita Bata saniba Dan kuwa wlh bazata dauka wannan wulaqancin tun yanzuba tana magana ya kashe mata waya.

MAMUH

A MAJEED/AYSHATOUH INAYAH/LOVE/ROMANCE/MARRIAGE

RIBA BIYU

FOR MORE PAGES KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOKS@Mamuhgee

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK

4 BOOKS  4500
3 BOOKS : 3500
2 BOOKS : 2500
1 BOOK: 1500

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
[10/14, 2:23 PM] +234 806 831 3988: Mamuhgee 13
Arewabooks@Mamuhgee
Da ‘dacin Rai duka suka kwana a daren ,
Inayah Kuma harda matsuwa tayi garin ya waye ta nemesa taji dalilinsa na kashe mata waya sbd ko Abbinta baya kashe mata waya shi dayafi kowane namiji daraja agurinta da rayuwarta.

Duk yanda Abbi yakai ga bacin rai baya taba Bari agane Dan haka da safen koda ya fito kyakkyawar  fuskarsa na ayanda take koyaushe ba damuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button