INAYAH 11-20

Black Armani’s ne ajikinsa sosai yayi fresh acikin black kala din,
Cikin sanyi ta kallesa tanason shagwabe Masa Amma tunanin Tayi Masa laifi daren na jiya yasa ta Dan nutsu duk da hakan cikin marairaicewa tace”
Good morning Abbi” tana qarasowa gurinsa itama shirye cikin milk sleeves riga da skirt na Balenciaga.
Morning Inayah” ya amsa Yana kallon yanda idanuwanta sukai zuru zuru sbd daren jiyan da Bata samu bacciba.
Dining suka zauna bayan ya gaisa da umma yaganah yasake kallon Inayah din da itama taketa qara wani kalar tausayi ganin take ya nuna ya lura da yanayinta na rashin baccin da Bata samuba Kuma tasan dole zai nuna damuwarsa akan hakan shiyasa take sake yin kalar tausayi.
Black tea Ginger tea Mai zafi aka fara zuba Masa ya dauka yafara Sha ahankali tareda Dan sake kallon fuskar Inayah din ya dauke fuska Kai tsaye ya bude Baki cikin nutsuwa yace”
Inayah¿
A marairaice tace”
Yes Abbi¿
Kallonta yayi bayan ya aje cup din hannunsa fuska a Dan matse yace”
Next abinda zakiyi na soke alaqarki da kowanne namiji sai bayan kin Gama karatu kwata kwata shine kici gaba da saka damuwar soyayya aranki harya hanaki bacci irin haka,
Umma yaganah ya kalla cikin jaddada zancensa yace”
Yaushe tasan wani soyayya hakane?
Ki ringa Mata fada sosai idan ba hakanba zan tattara mubar qasar gabaki daya mu koma Nigeria ko Zata maida hankali a karatun can.
Hawaye takeson yi Amma tunowa da ya Hana yasata maida hawayen cikin sanyi tace”
Abbi Dan Allah kayi hkr,
Ba tunanin komaine yasa banyi bacciba inada test ne yau so I had to study all night…
Waiwayowa yai ya watsa Mata manyan idanuwansa ahankali Yana sake mamaki da jinjinawa sauyin sabbin halayenda Inayah ke dauka,
Yaushe Kuma ta iya harda yimasa qarya?
Sauke Kai tayi qasa tana Dan sosa wuyanta gabanta na faduwar kada yagane qaryarta saidai Batasan ta makaroba.
Qarasa Shan tea dinsa yayi Bai wani Abinci sosai ba ya kammala ya miqe Yana cewa”
Muje zan ajeki school.
Satar kallon umma yaganah tayi tana neman qaryar dazata Kuma shimfidawa yatafi yabarta ta tafi school din da kanta Dan dole tana buqatan biyawa gurin Zaid suyi magana.
Rasa abin fada tayi dole badan tasoba ta miqe suka bar gurin umma nai musu adduar dawowa lfy.
Shi kadaine ya amsa Banda ita data shiga tunanin abinyi Dan yanzu tasan kila Abbin zai qara Mata tsananin fita akan na dah.
Yau bashine yake tuqa motarba driver dinsa ne yake jansu.
Har suka Isa makarantar kame kamen basa hakuri takeyi Amma Bai wani bi takan zancen nataba saima zancen karatun dayayi Mata daban.
Suna Isa aka sauketa suka wuce sai alokacin yabi bayanta da kallo,
yanajin tausayin ‘yarsa fiyeda komai,
Hakama Baya iya hakurin damuwarta,
Ya rasa waye yake gurbata Masa tunani da tarbiyar ‘ya akan ire iren hakan,
Kwata kwata haryanzu bayajin sha’awar kowace irin mace bare marmarin ajiyeta shiyasa yake tsananin mamakin yanda Inayah ta qwallafa Rai a soyayya da son aure tunda ba ganin tayiba a gidansu ana soyayyar, hasalima shi soyayyarce sam baisan yama akeyintaba bare harka Gama macewa akan wani kaje kana Hana kanka bacci a wofi.
Motar Abbin na barin makarantar ta fito zuwa coffee shop din dake makarantar ta samu Neesah dake can ta zauna tareda fidda wayarta batareda ta iya wata doguwar maganar da Neesarba tafara saka Kiran zaid.
Kasa samunsa tayi dole qarshe tabar Masa sakon murya da cewa idan ya kunna waya yakirata Kuma ya tabbata Dad baije gurin Abbinta ba sbd zasu iya yiwa kansa Abbin ya dakatar da soyayyarsu sai gaba din.
Bayan Gama tura Masa sakon muryan aje wayar tayi gabanta zuciyarta ba wani Dadi ta Dan yamutsa fuska tareda Kiran sunan waiter a tushe tace”
2 Cappuccino’s please.
Kallonta Neesah tayi tana cewa”
Kodai zamu samesa ne?
Bazai tsaya sauraren wannan ba namafi zatan Dad din nasa ya riga Abbi Isa office dinsa jiransa.
Kasa cewa komai tayi Saida aka kawo Mata cappuccino din ta fara Sha ahankali kafin tace”
Banajin komai sai bacin ran mahaifina,
Zuwan dadyn Zaid zai fusata Abbi Kuma na fadawa Zaid kada yaje Amma Yana banza da zancen yakuma Dan akan Abbina bana daukan wannan so gwarama ya daina wannan saurin.
Bari naji Inda yake saimu samesa” cewar Neesah tana fidda wayarta daga qaramar Louis Vuitton handbag dinta.
Kinason Abbi ya daina kulani kwata kwata yayi fushi danine?
Kinsan halinda mahaifina zai shiga kuwa idan yaji naje gidan namiji
Gskia bazan iyaba,
Bari anjima idan Bai kiraba na sake kiransa.
Maida wayar Neesah tayi tana cewa”
Amma dai bafa lallai yazoba Sai sungama magana da Abbin hakan Kuma shine qarshen Bata komai.
A qasan maqoshi ta furta”
Allah ma yasa Abbi ya gaji da wannan zaryan ya amince musu ayi auren yanzu sbd Gaskia Ina son Zaid dina sosai,I can’t live without him, duk wannan fadan danake na qarfin haline Ina tsananin sonsa gaskia.
AAM’s BUILDINGs
Zaune Yake kan sofa dake makeken office dinsa hankali kwance ya jingina bayansa kadan yana sauraren Former Ambi Mukhtar Asheer mahaifin Zaid.
Gabaki daya idanuwansa dake Dan rikata wanda duk ya zubawa sbd kwarjini su ya zubawa Ambi din Yana kallonsa Yana saurare.
Da gaskiyarsa ta hakika yake sake tsaro jawabansa Dan shawo kan A MAJEED din ya amince da auren ‘yayan nasu a yanzu sbd kaucewa barna tunda yaran sun matsa sunason ayi.
Amma abinda Bai saniba gameda A MAJEED shine wannan zuba Masa idon da yayi baida niyar daukan zancen ne.
Qaramin numfashi ya sauke a natse kafin ya Dan dauke kallonsa daga Ambin ya dauki wayarsa dake gefensa ya ajiye gabansa cikin nutsuwa yakuma nagowa ya kallesa yace”
Kaman yanda nafada last time dakuma farkon zuwanku neman auren maganar dai tana Nan a hakan,
Hakuri zaa cigaba dayi inshallah babu wani abinda zai faru ko biyowa Baya dangane da wata barna ko makamancin hakan…
Inayah dai tunda nace nabawa Zaid aurenta bazan fasaba kokuma sauyawa matuqar ba itace tace ta fasa Dinba kokuma wani dalilin dazai iya hanawar Kuma ba’a fatan hakan,
Dan haka Ambi Ina sake baka hakuri kuci gaba da hakuri inshallah lokacin ya kusa sbd tana gab da kammala karatun tunda duka duka shekara dayane ya rage Mata inshallah…
Amma tunda Kai kana hango wata barna da Zata iya biyo bayan rashin auren da wuri
To inaga na dakatarda haduwarsu kawai su tsaya iya waya zuwa sbd kiyayewa sai a sanarda shi Zaid din
Inayah Kuma zan fada Mata
Daga yanzu haduwarsu iya wayane ya dakata da zuwa gurinta for now,
Allah yayi Mana jagora duka.
Sake da Baki Ambi yake kallon A MAJEED din Yana sauraron bayanansa dake fitowa suna zuwa Kai tsaye,
Yasani yakuma ji wainda suka San A MAJEED din suna fadar Kai tsaye yake magana Baya wani kwana kwana ko lanqwasa Musamman zancen daya shafa ‘yarsa dayake ganin baida abinda yafita.
Jin shiru yasa Ambi ya rufe bakinsa tareda sauke numfashi Yana yaqen dole yace”
Shikenan ba komai zamu cigaba da jiran tunda Shima akwai nasa programs din dazai kammala zuwa next year din
sai abin yazo musu duk a natse ma,
Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi.
Amin” ya furta Yana kallon ruwa da aka kawowa Ambi din Bai Sha ba yace”
Me zaa kawo maka?
Any drink, coffee or something?
No,no,no I don’t think i need anything
Thank you,
Ruwan ma is okay.
Daukan ruwan yayi yasha kadan tareda ajiyewa suka Dan fada wata firar daban wadda Bata shafi iyalansuba ta business industries ahakan har ya Dan ja lokaci sosai sai lokacin tashinsa suka fito tare ya maidasa har masaukinsa kafin ya wuce gida da driver dinsa.