GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 11-20

*Maganar aure dole Abbinta ya aminta da ita aka tsaida lokacin auren wata biyar masu zuwa Wanda sukai daidai da kammala karatunta da wata daya kenan,
Dan haka tuni aka fara shirye shiryen Auren ta bangaren mata kenan suda sukeda hidimar yi ta shagalin biki.

Inayah tunda aka tsaida lokacin auren ta Zaid daga ita har Zaid din suke cikin wani irin tsananin farin ciki,

Iyayensama kaman zasu janyo lokacin sukeje musamman dad dinsa,

Umma yaganah ma kam fadar farin cikin datake kwana dashi tana tashi dashi bazai yiyuba,

Babban burinta a dah shine ganin ranarda MAJEED zaiyi aure ya ajiye mace da sunan matarsa kafin Auren Inayah yazo daga baya saigashi na Inayah dinne a gaba duk da hakan tana farin ciki,
Bare tunda auren Inayah Yana hanya Inshallah Shima nasa Yana hanya din.

A Nigeria Abbinta keson sukoma ayi auren acan kafin sudawo daga baya,
Aikuwa Murna kan Murna agurin Umma yaganah sbd tanason zuwa Nigeria dama sbd sada zumunta da jama’ar arziki da aka zazzauna tare acan baya.

Neesah da Inayah duk da irin yanda suka maida hankali sosai akan karatun yanzu hakan Bai hanasu tsananin Shirin gaske ba akan yawon shoppings da gyaran jiki duk da Abbin baisan tana zuwaba tunda ya hanata zuwa spa’s.

Amal kuwa daga hankalinta tayi akan auren Zaid Dan haka tafara kokarin tona asirin alaqarta da Zaid gurin Inayah Amma tana shakka sosai na mahaifin Inayah sbd ita batama da kowa qasar karatu kawai takeyi da watsewarta Dan haka take shakkar taba Inayah,Amma badan mahaifin Inayar ba da tuni ta yaga Mata rigar mutunci tasa anyi Mata kaca kaca da ita.

****Saura wata daya sufara exams Neesah ta aje Inayah gida da mota ta nufo hanyar gidansu taci Karo da motar Zaid a gabanta tareda Amal zaune gaban motar suna wani irin tuqi a hankali.

Sake kallon motar tayi da kyau ta tabbarda motar Zaid ce Kuma da mace aciki.

Bata kawo tunanin komaiba tayi over taking dinsa ta wuce motarsa tana Masa horn alamar gaisuwa.

Bai lura da motartaba sbd hankalinsa na kan Amal dake Masa wani shegen Wasa Yana dariya.

Amal din taga Neesah Dan haka take sake Matsoda fuskarta tayi kissing bakinsa tana lasar kumatunsa.

Wani shegen burki Neesah taja tana neman gefen hanya ta saukar da motarta sbd kokarin kufce Mata datake.

Kutttt…..”tafada cikeda mamaki da faduwar gaba sbd kasa yarda da abinda tagani,

Zaid?da wata macen Kuma?
Har suna irin haka?
Anya kuwa Zaid ne?
Zaid din Inayah da babu wata bayan Inayah agunsa.

“Oh my God, this is unbelievable” tafada zufa na Dan karyo Mata na tashin hankali,

“I can’t tell this to Inayah,
Bazata yardaba,Nima nakasa yarda da abinda nagani gskia.

Sosai takejin firgici da tsoron abinda tagani din,

Tun baayi aurenba Zaid ya iya cin amanan Inayah duk yanda take tsananin sonsa da kaunarsa,

Tabawa rayuwar aure datakeson yi Amana da yarda da burirrika
Tun yanzu hakan yafara faruwa to me Zata tadda idan taje gidan nasa?

Inayah nada tsananin zafin kishi na gaske ga zuciyarta nada rauni wlh bazata iya daukan hakan ba,

She is too weak to take this,

Tayaya Zata iya daukan wannan?

Daqyar Neesah ta iya tattara kanta ta tada motar ta nufi hanyar gida jikinta amace Dan Jin take Kamar itace akewa wannan cin amanar tunda aminiyarta akewa,

Ta yanke shawarar bazata fadawa kowaba Amma Zata saka Ido sosai tasan Gaskiar Zaid din tun kafin ayi auren.

Tun daga ranar Neesah tasaka ido sosai akan Zaid da Amal saigashi kuwa dai ta tabbatar da wata irin qazamar soyayya sukeyi Mai zurfi.,

Hankalinta ya tashi sosai saidai Kuma batason fadawa Inayah sbd ga karatu Mai nauyi agabansu ga tsoron halinda Zata shiga,

Gashi Abbi ma ba abun wasaba bare ta fada Masa.

Haka tanaji tana kallo Zaid nata yaudarar mata Inayah.

Ana cikin hakan suka fara exams dole ta tattarasa ta watsar suka maida hankali akan karatunsu.

Suna cikin exams Dr farhat taci gaba da Taya umma yaganah shirye shiryen biki da tafiyarsu Nigeria wadda zasuyi bayan Gama exams din Inayah.

Ta dayan bangaren Zaid yakasa rabuwa da Amal duk da kwata kwata ko Rabin matsayi Inayah aransa Bata kaiba Amma sbd mumunar jarabta yakasa rabuwa da ita.

****Ranarda su Inayah suka kammala jarabawa kwana sukayi farin ciki itada Abbinta da umma yaganah.

Kwana biyu tsakani suka wuce umrah,
Sati biyu acan suka dawo aka fara shirye shiryen zuwansu Nigeria sbd Saura sati uku bikin.

Koda suka dawo dayake tareda Neesah da Abbin da umma sukeje,

Tanata kiran Zaid Bata samu gashi baisan sun isoba,

Batada karyar dazataiwa Abbi ta fita ranar Dan haka tace itace Zata Kai Neesah gida.

Kai tsaye yace umma yaganah ce Zata kaita gida sbd yiwa iyayenta godia.

Bata damuba tace bakomai sbd tasan umma bazata hanata biyawa gidan Zaid dinba.

Sai yamma suka fito shiye take cikin riga da wando na Nike black da sneakers farare ta saka face mask da hular rigar kayan sbd batason kowa ya ganeta lokacinda Zata shiga gidan Zaid Dan kada afadawa Abbinta da Kaman duk motsinta Yana sane dashi.

Da farko umma yaganah qin yarda tayi abiya din suka ringa rokonta,

Musamman Neesah datakeson abiya din ko Allah zaisa yau kowa yasan mummunan rayuwar dayakeyi tun baayi aurenba Allah yaraba Inayah da rayuwar damuwa.

Cikin saa kuwa suna Isa motar Zaid na gida Dan haka Kai tsaye suka shiga itada Neesah Banda umma data zauna a mota.

Door bell suka ringa dannawa babu Wanda yazo ya bude Dan haka Inayah datasan password din kofar ta saka kawai ta bude suka shiga.

Da gudunta ta nufa kofar dakinsa tana Kiran sunansa.

Bakin kofar dakin ta tsaya batareda tashigaba sbd sanin Bai kamata tafara Kiran sunansa ahankali cikin shagwaba da soyayya.

Yana kitchen tareda Amal suna cin pizza dasukai order yagama ci yaje gidansu Inayah sbd yasan sun jima da isowa yanzu.

Neesah ce ta ringa Jin dariyarsu ta nufa kofar ta leqa ahankali aikuwa tagansu suna cin pizza kowanne babu wani kayan kirki jikinsu sai wasanni sukeyi hannuwansa na cikin fingilalliyar rigar baccin jikinta dake nuni da tun safe suna daki suna Abu daya.

Da sauri Neesah ta Isa kofar bedroom dinsa da Inayah take ta kamo hannunta tana cewa”

Yana kitchen.

Ha yar kitchen din suka nufa Inayah na Kiran sunansa da cewa”

Baby,
Baby where are you?
Bab…….

Cak ta tsaya kafin ta qarasa kitchen din ganin abinda takasa ganewa.

Da gudu ta qaraso cikin gurin tana kallon yanda yake kokarin ture Amal daga jikinsa hankali tashe Yana cewa”

Baby?
Me kikeyi anan?
Abbinki yasan kinzo kuwa?
Bakya tsoron yasan kin zo?

Amal ya kalla da sauri Yana cewa”

Inayah ba abinda kike tunani bane ki…..

Tsayawa gabansa Neesah tayi Rai abace tace”

Karma kayi wahalar bayanin komai,
Ni nasan wannan qazamar rayuwar da kakeyi bada sanin kowaba tuntuni yanzu Kuma Inayah tagani da idonta.

Jan hannun Inayah tayi suka juya suka fice.

Har mota Inayah kasa cewa komai tayi sbd cak kanta da tunaninta ya tsaya.

Umma yaganah sai tambayar abinda yafaru takeyi sunqi cewa komai sai ajiyar zuciya da Inayah ke jerowa cikin fita hayyaci.

Suna tsayuwa kofar gidansu Neesah
Sai alokacin Inayah ta juyo ta kalli Neesah murya a sarke tace”

Neesah Zaid nagani da mace right?

Numfashi Neesah tasake tareda kallon umma data gwalo Ido ta gyada Kai.

Wait wait wait,
Ina nufin mace Naga zaid da ita cikin yanayi na aikata wani Abu fa?

Kai tsaye tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button