
Zandawo gida Nan da time kadan”
Yana fadar hakan suka kashe wayar kusan atare shi da ita.
Itama tana ajiye wayar anan palon tayi zamanta Saida zubbi tagama gyara koina har palo dasu dining room aka sake kunna abubuwan qamshi tukuna ta miqe ta nufi dakinta.
Tubewa tayi ta nufi toilet tashiga ruwan zafin bagaruwan da Anty Hafsat yauma tazo Mata dashi acikin roba ta shiga sbd Yana Bata toilet Dan haka tana Gama shigarsu a robar takira zubbi ta fice da qatuwar robar itakuma ta zare towel dinta tafara wanka.
Tana gamo wankan Mai kadan ta shafa da turare ta saka kayan bacci ta Dora abaya akai tayi sallar ishai
Tana idarwa ta haye gadonta ta zauna tareda rufe qafafunta ta dauki wayarta tafara duba chats dinsa da Bata samu damar bi ba yau sbd zuwansu umma Hadiza.
Tana cikin chatting sama sama bacci yafara daukanta ta sake Nemo numbern Abbinta tasaka kiransa ganin har time din be dawoba.
Wayar Bata shigaba Dan hakan ta sauko da qafafunta kan gado tareda miqewa ta zira slippers ta nufi dakinsa.
Haj umma tashige tuni Dan haka tsit ba kowa ta nufi palonsa ta bude tashiga Kai tsaye ta nufi bedroom dinsa.
Tana budewa Yana fitowa wanka daureda towel brown.
Fuskarsa ta kalla ko Bai fadaba taga alamar gajiya ataredashi Dan haka ta matso gurinsa tana cewa”
Abbi kaci abinci kuwa?
Lumshe fararen idanuwansa yayi tareda budesu akanta baice komaiba ya janyota jikinsa ahankali ya rungumeta tareda sauke ajiyar zuciya mara sauti dukkaninsu sukai shiru basuce komaiba suka jima ahakan Saida ya samu nutsuwa da Jin gajiyarsa ta rage sosai kafin ya saketa suka kalli juna
Ya maida kallonsa kan rigar jikinta Daya jiqa da ruwan wankan jikinsa Daya fito dasu.
Murmushi yasake Yana Kama hannunta suka nufi gaban mirror.
Mai ya Bata a hannunta
Ta kallesa ta cikin mirror kafin ta karba ta fara shafa Masa ahankali hannun na Dan rawa Wanda shikuma yanda takeyi ahankali kaman tana shafa baby dakuma Dan rawar da hannunta keyi yasashi jin jikinsa na sake mutuwa gabaki daya hakama zuciyarsa na sake raunana da tafiyar Nan data taso Masa wadda zaiyi gobe Inshallah.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[11/16, 9:23 AM] +234 806 494 4178: 68
Arewabooks@Mamuhgee
Tana Gama shafa masa man ya Jata ta tayasa saka kayan baccinsa Babu me doguwar magana acikinsu sbd gajiya dakuma lura datayi bayajin maganar kwata kwata da alama akwai abinda yake cizon ransa.
Kwantawa sukai yauma shine ya shige jikinta ta rungumesa tana shafa bayansa ahankali har bacci ya dauketa.
Jin bacci ya dauketa ya sanyashi zamewa ahankali ya gyara Mata kwanciyarta tareda shigar da ita jikinsa ya rungume bayan yayi kissing goshinta ahankali.
Bacci sukayi sosai har yaso lattin sallar asuba,
Tada ita yayi sukai sallar Suna idarwa ta matso jikinsa ta kwanta tana kallon fuskarsa ahankali cikin kulawa tace”
Abbi akwai abinda yake damunka ne?
Murmushi ya sake Mai kyau tareda saka hannuwansa cikin hijabinta Yana yawo dasu cikin rigarta yace”
Bakomai kawai tafiyane ya kamani tsawon sati biyu Ina tunanin ko Zan iya ne.
Kallonsa tayi fuskarta na narkewa tace”
Sati biyu Abbi? Nidai bazan iya sati biyu baka Nan umma yaganah Bata nanba.
Wani murmushin ya sake Yana zare hijabinta yace”
Zaki iya ga Haj umma Nan Zata kula dake tunda taga bama Nan.
Shiru tayi sbd kada ta fada abinda zai Sosa ransa Amma ai kowa yasan basa jituwa da Haj umma.
Jin tayi shiru ya sake matseta jikinsa tareda daukanta suka koma kan gado suka koma bacci Yana cewa”
Bazan sati biyun ba Zan dawo sbd nasan nabar patient ai.
Murmushi tayi tana sake lafewa tace”
Nidai kada kayi sati biyu Abbina kaji??
Bakinta ya Kama ya tsotsa sosai cikin nutsuwa kafin ya gyada Mata Kai.
Bacci suka koma har sai karfe goma kaman yanda suka Saba fitowa suka fito abbin Yana shirye tsaf cikin ash Armani’s fuskarsa a natse cikin sahirtaccen marmushin Dayake sake bayyanarda kyansa da kwarjininsa.
Hannunta cikin nasa suka nufi dakin Haj umma data fito dakin dan zuwa Kiran Salimat tazo tai Mata gashin qafafunta data kwana suna Mata ciwo sbd ciwon bayan da Inayah ta sakar Mata tun shekaran jiya gurin dawainiya da yaqin kulawa da ita ba masifar da basuyiba gurin shigar ruwan zafinta Wanda duk tabi ta jijjigata gashinan ta taso Mata ciwon baya da qafafu.
Kallon fuskar MAJEED dinta tayi taga kwanciyar hankaki da nutsuwa tareda kyakkyawan sahirtaccen marmushi akan fuskarsa Wanda ke bayyanarda nutsuwar zuciyar Daya samu.
Wani sanyi jikinta yayi tareda da farin cikin ganin ‘danta yafara komawa ABDULMAJEED dinta data sani ba AA MAJEED ba Wanda zuciyarsa take a kulle Babu farin ciki ko walwala acikinta ko kadan.
Inayah data wani narke a gefensa ta kalla a karon farko dataji Dan sanyin Inayar fuska a sake ta amsa gaisuwar MAJEED din tana kallon Inayah tace”
Lafiya kike yamutsa fuska kaman zakiyi kuka?
Sake riqe hannun Abbinta tayi tana sake Bata fuska tace”
Haj umma Abbi fa tafiya zaiyi har sati biyu abarki Dani
Bazaki iyaba kema ko?
Haj umma ko taso Jin sanyin Inayah iya shegenta kesawa suna watsewa da wuri,
Cikin gatse tace”
To idan bazan iyaba saiki bisa kokuma nace Karya tafi ko?
To yatafi Allah ya kiyaye Zan iya Dake din ai.
Kai Haj umma wato sbd kada aje Dani kokuma yadawo da wuri shine zakice Zaki iya Dani?
Abbi cewa fa tayi duka Zataiwa bakina idan Ina maganar da bataso tun a gabanka ma
Idan ka tafi kuwa kilama Koda zaka dawo Haj umma ta sauya maka kamannin baby Inayah dinka.
Wani kyakkyawan murmushi yasaki Yana kallon Haj umma data sake Baki tana kallon shegen bakinta da sai yanzu tasan me umma yaganah keji datake buge Mata bakin..
Inayah ta maidata gabaki daya kakarta ko alamar nuna a uwar miji ta dauketa batayiba,
Haqiqanin kakarta ta dauketa..
Cikin kulawa Yana sake fadada murmushinsa gaban Mata biyu dayafi so a rayuwarsa fiyeda komai da kowa,
Matan dazai iya komai akansa Banda sabon ubangiji Amma Babu abinda bazai iya badawaba akansu ciki harda tasa rayuwar,
Farin ciki da zuciyarsa ne tsaye a gabansa tsaye suna Rigimar tafiyar tasa,
Hakan yasake saka zuciyarsa farin ciki ya sake kallon Haj umma yakai hannunsa yakama hannunta cikin kulawa yace”
Haj umma karki biyewa Inayah so take tasaki kiyita magana,
Ki kula da ita tunda yanzu ke kadai take da ita umma…
Inayah ya kalla yace”
Ki lallaba Haj umma karkiyita sakata magana,
Idan kinsan Zaki fada abinda zai sakata fada ki dena fada kiyi shiru okay????
Gyada Masa Kai tayi tana sake janyo hannunsa daga na Haj umman ta riqe cikin nata tana cewa”
Haj batason ana riqe hannunta tace
Idan na rike cewa takeyi bataso damunta hakan keyi bataso.
Haj umma da Inayah tagama cika kanta ta janyota daga hannun Abbin tana cewa”
To ki barsa kema ya wuce kada yayi latti.
Mamaki suka fara basa Dan haka ya juya Yana cewa”
Muje breakfast zanyi tukuna kafin na fita.
Sbd tafiyar dazaiyi yasa Haj umma yin breakfast din tare dasu zuciyarta na sanyi da kaunar ‘danta sbd rabonta dataga farin ciki ko walwala a fuskar MAJEED tun kafin haduwarsa da Hadiza.