![](https://iganyabusinesshub.org/wp-content/uploads/2022/12/IMG_20220909_164547_003-22233333.webp)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
0913484810769
Arewabooks@Mamuhgee
Da hannu daya ya riqe Dan qaramin qugunta zuwa bayanta Yana Dan sauke ajiyar zuciya a boye yasamu nutsuwa ko ahakan Dan hakan ya janyeta daga jikinsa Yana Dan wadata fuskarsa da kamilallan murmushi Yana kallon Dr iklimat da umma Hadiza dasuka gaidasa tareda Masa barka da dawowa.
Fuska asake cikin mutuntawa ya amsa Yana tambayar Ashe Bata koma Abuja ba tana Lagos har lokacin.
Suna Gama gaisawa dashi suka fito Inayah tabiyo bayansu tabarsa yasamu Daman Gaisawa dasu Haj umma a natse Dan idan tana gurin tana maqalqalesa ba tsayawa zaiyi sosai su Gama gaisawa zai sulale yabar gurin tun kafin mutuncinsa yagama watsewa agurin.
Har jikin motar umma Hadiza ta rakasu suka sake tsayawa magana Dr iklimat tasake nanata Mata zancen girkin datai Mata dazu sbd haryanzu su basuga ta Kama gidanta da kyau ta qarasa Zama cikakkiyar matar gidan koyaushe kaman ‘yar lelen gidan takeyi gwara dai tazama cikakkiyar matar gidan me iko da megidan da duk Wanda ke karshin gidan.
Suna wucewa tadawo ciki sai ta tadda har abbin ya shige baya palon.
Rasa abinyi tayi sbd taso binsa dakinsa Amma Kuma sai ta tuna da zancensu ummanta dasuka Bata tabbacin idan Bata karba har ragamar abincinsaba zaa iya samun damuwa Dan hakan saita wuce Kai tsaye duk da batasan me zatayi ba.
Zubbi tasa ta wanke Mata fresh veggies ta yanka Mata ita Kuma ta Dora spaghetti sbd ita tafi iyawa Kuma tafi sauki a lokacin tunda dare ne.
Brown vegetable spaghetti ta dafa Masa wadda kusan Naman kazar data zazzarewa qashi tafi veggies din yawa aciki.
Sosai abincin yayi Dadi sai qamshi kitchen din keyi Yana samma Palo Dan dama umma yaganah tayita koyar da ita girke girke itace kawai Bata maida hankali sakalcinta kawai tasaka agaba shiyasa girkin Bai wani kamata ba Amma idan ta dage taso tsaf zatayi abinci Mai Dadi da tsari.
Saida zubbi ta jera komai a dining kafin ta fito kitchen din ta wuce dakinta ta kwabe kayanta ta fada toilet.
Ta jima tana wanka sbd duk gajiyar aikin datayi takeji qafafunsa har ciwo taji sun Mata sbd tsayuwa a aikin.
Wankan tayi tana fitowa sai datayi sallar ishai tagama kafin ta shafa Mai kadan ta saka doguwar free wide neck English gown.
Qaramar hula kawai ta sako akanta ta fito ta nufi hanyar palonsa kenan sai gashi ya fito sanye cikin milk jallabiya me maiqo datai Masa kyau sosai yafito kaman balaraben uztaz.
Kallonta yayi a natse kafin ya miqa mata hannun damarsa yana cewa”
Zo Nan..
Tahowa tayi fuskarta na bayyanarda tsananin son datakewa halittar Dake gabanta ta Kama hannunsa tareda rungume hannun tana cewa”
Abbina harka Gama hutawan?
Muje yau nice nayiwa mijina girki me Dadi.
Dakin Haj umma suka nufa sbd ganin Salimat ta fito daukeda manyan kulas ta nufi dakinta.
Suna zuwa yaga alaman a daki zasuci abincin yace Salimat ta maida dining su fito duka suci acan tare kaman yanda aka Saba.
Inayah dake gefensa ta qaraso tana cewa”
Haj umma yau fa nice nayiwa Abbina girkin Amarya
Gwara kifito kici kiji dadinsa gskia sbd kada gaba nayi lefi kice ban iya abinciba Ina barin Abbina da yunwa adawo da maganar Dr farhat..
Wani mugun kallon takaicin rashin tsarkin bakin Inayah Haj umman tayi Mata tana cewa”
Ko yanzu ce miki akayi anfasa maganar Dr farhat dinne?
Zaro ido waje tayi a Rikice ta kalli Abbinta cikin mamaki da rikici..kafin tayi magana ya kamo hannunta ahankali yane cewa”
Muje naci abincin naji.
Dawowa tayi gefen Haj umma tana cewa”
Yanzu Haj umma duk wannan biyayar danake Miki da girki gashinan nayima
Harma da ‘yayan Abbi da kikace nace duk zanyi Haifa shine Baki yafe maganar Dr farhat ba.
Hawaye ne ke Neman cikowa idonta abbin ya kalli Haj umman da alaman roko kafin yayi magana tace”
Naji to muje naci abincin naje idan yayi Dadi sai abar maganar Dr farhat din yanzu Amma dai bakinki idan Bai fara koyan maganaba akwai maganar a gaba Dan bazaa ringa Shiga mutane dakeba kina wannan sakarcin.
Wucewarta tayi gaba tanajinma ta Dena Jin yunwa da dokin cin abincin.
Tana ficewa Abbinta yabi bayanta sbd yasan rigima Zata fara Zata iya hautsinewa ta rikitasa.
Riqota yayi tareda dawowa da ita ta baya bayanta ya hadu da kirjinsa ya rungumeta Yana goga Mata fuskarsa ahankali Yana cewa”
Keda Haj Kun Zama kaman jika da Kaka ko?
Menene na tado maganan wata agaban mijin da kikasan Babu gurin kowa a zuciyarsa…
Uhumm?????
Shiru tayi tana danne abinda takeji din harya fada Mata ta sauke ajiyar zuciya ahankali itama kafin ta zame kadan ta juyo ta kallesa taga yanda shima yake kallonta tace”
Shikenan muje kaci abincin Amaryarka kaji.
Jan hannunsa tayi zuwa dining din da harsu Haj umma sun fito Ashe sun wucesu sun Isa dining din Basu luraba.
Zaunawa yayi ta janyo abincin tayi serving dinsa tana kallon yanda shima yake kallon abincin cikin bayyanarda Jin dadinsa na cin girkin Amaryarsa kaman yanda tafada.
Haj umma ta zubawa bayan tagama zuba Masa kafin ta zauna tana kallon fuskarsa data Haj umma tana cewa”
Kome kukaji ku fadamun Dan Allah kaji Abbi?
Murmushi kawai yayi tareda daukan fork ya fara cin abincin cikin nutsuwa hankali kwance da alaman abincin yayi Masa komai da komai.
Haj umma ce dai takasa shiru tace”
To ba laifi da Dan sauki tunda kin iya girkin…sauran iya Kama bakinki.
Dariya Inayah tayi tana Jin dadin Yana abincin da Haj umman tayi ta maida kallonta kan Anty safiyyah tace”
Anty safiyyah kefa?
Yayi Miki Dadi?
Sosaima Inayah”” tace sbd itakam babu abinda Inayah zatai yayi Mata ba daidaiba sbd son samun Shiga sosai agurin ‘dan uwanta Dan itakam bakin fama so take su daidaita fiyeda dah to kuma ta lura ka so Inayah na kaunaceta shine abinda zai baka samun shiga agun MAJEED.
Sosai yaci abincin daidai cikinsa yasha ruwa ya zari tissue ya goge bakinsa ya miqe yabar gurin.
Saida kowa ya kammala ta taya zubbi tattare gurin suka kai kitchen.
Tana baro kitchen a Palo ta taddasa zaune tareda anty safiyyah da Haj umma suna magana ko rumanah data girmeta Bata gurin Dan haka itama Bata zaunaba ta nufi hanyar bedroom dinta ta wuce tanajin idonsa akanta Yana binta da kallo harta bace daga palon.
Zaunawa tayi ta dauki wayarta taga misscalls din Umma yaganah tasaki murmushi tana bin bayan Kiran da nata Kiran..
Basu jimaba suna wayar suka Gama ta ajiye wayar ta miqe ta nufi toilet ta tayo brush da alwalar bacci data Saba ta saka kayan bacci masu santsi Riga da wando farare tas ta shafa turare ta haye gadonta tashige bargo ta lafe sbd Abbinta har lokacin magana sukeyi dasu Haj umma a Palo basuda lokacin gamawa..
Baccintane ya dauketa me Dadi bayan ta kashe wutar dakin….
cikin baccin taji mutum na kwanciya a bayanta tareda rungumeta sosai jikinsa Bata wani motsaba sbd baccin dayayi Mata qarfi shikuma sbd kada ya takura Mata tana baccin yasa Bai tashetaba kokuma yimata abinda Zata tashin ya rungumeta kawai sukai baccinsu cikin nutsuwa da kewan dumin juna.
Washe gari 10 tafito daga dakinta sanyeda kayan baccinta ta nufi kitchen tasaka hannu a aikin breakfast dinsa Dan kusan angama komai Amma Saida tayi Masa Honey pancakes da kanta ta dafa Masa tea dinsa suka jere a dining Amma nasa pancakes din bayan ta zuba Masa zuma a wani farin kyakkyawan tray ta jera tareda qaramin cup din tea dinsa ta nufi bedroom dinta da tray din.