JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 52

“Aa bai tafi ba” Ahmad yace “Ohk, na kira bai daga bane” Umma tace “Ko wayar na mota” Ahmad yace “Toh shkkn xan kira anjima” Umma tace “Allah ya kai mu” Tana katse wayar ta kalli Abuturrab tace “Aliyu ku koma gida kawai, tun da har ta samu bacci, she will get better in sha Allah… Daga nan ku ajiye Maimoon ma a gida” Abuturrab dai bai ce komai ba, Aneesah dake xaune kan plastic chair ta kalli

Abuturrab din ta gefen ido ta ji abinda xai ce, Yana kallon Umma yace “To shkkn, Allah ya bata lafiya” Umma tace “Ameen, Allah yayi albarka” Kallon Maimoon da ta mike yayi sannan ya nufi kofa, Aneesah ta mike tana kallon Umma tana kirkiran murmushi tace “In sha Allah, xan dawo anjima Umma, Allah ya bata lafiya” Umma tace “Ameen, mun gode Aneesah, Allah yayi albarka” Tace “Ameen” ko kallon

Jiddah bata yi ba ta fice daga ward din, Umma na kallon Maimoon tace “Ki dauko mata wani hijab din, may be with an extra clothe, sannan ki taho da toothpaste and brush, idan su Huraira sun gama breakfast sai ku kira driver ya taho da ku anjima, nima ki dauko min wani hijab din kar ki manta” Maimoon tace “Toh” sannan ta fita ward din. Karfe takwas da yan mintuna Abuturrab ya shiga dakinsa

bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, kwance ya tadda Aneesah har sannan tana bacci tun bayan da suka dawo wajen karfe shidda da asuba, Karasawa yyi saman gadon ya kai hannu ya buga gefen gadon, ta bude ido a hankali don tun bude kofar parlon da yayi ta farka, yace “Yanxu babu wani abu da xaki girka a kai asibiti??” Buda ido tayi sosai tana kallonsa sai kuma ta mike xaune tana ci gaba

da kallonsa keenly tace “Abu kamar me fa Captain?” Yace “Breakfast….” Bude baki tayi sai kuma ta tafe hannu tayi wani dariyar rainin hankali tace “Saboda Aisha ko Ramlah ce kwance gadon asibiti ba lafiya ko??” Kafeta yyi da ido, ta ja wani tsaki tace “Wllh ka xo da wata bidi’a Captain, kawai saboda ga kanwar uwata Safara’u kwance gadon asibiti sai in tashi da sassafe in fara hada breakfast, to bari kaji

wllh ko Maimoon ce bata da lafiya sai na ga dama xanyi girki a kai asibiti balle wata banxa can mara asali, gayyar…..” Dakatar da ita yayi cikin tsawa yace “Enough Aneesah, baxa kiyi ba baxa kiyi ba, final!! Kar ki gaya min maganan banxa…” Aneesah ta masa wani kallon banxa daga sama har kasa ta sauka kan gadon ta shige bandaki abun ta tana cewa “Ka xata tun farko da nasan ita ce ba lafiya xan ma fara katse bacci na in fita cikin dare…” juyawa yayi ya fita daga dakin xuciyarsa na tafarfasa, yana komawa downstairs ya kira layin Maimoon, tana dauka yace “Anyi breakfast ne a can gidan?” Maimoon tace

“Ehh driver muke jira yanxu ya kai mu asibitin” yace “Ohk, i am coming now” daga haka ya katse wayar, yana isa gidan Umma ya dau Maimoon da Safiyya suka wuce asibitin, har sannan Jiddah bata tashi ba, Umma na kallon Abuturrab yace “Ya ku ka koma gida” yace “Lafiya lau” Maimoon na kallon Umma tace “In hada maki shayin Umma?” Umma tace “Aa ai baxan iya sha a nan ba, tun da kun xo bari kawai in koma gida sai in dawo anjima idan na kintsa” Maimoon ta mayar da cup din tace “Toh shkkn” Umma ta

mike, Abuturrab ya kalleta yace “Toh bari in ajiye ki gidan Umma” tace “Toh nagode” Tare Umma ta koma da safiyya da tayi shirin Islamiyya, Abuturrab na kallonta yace “A Islamiyyan xa a ajiye ki ke?” Tace “Ehh” sai da ya fara ajiyeta a Islamiyyarsu sannan ya kai Umma gida, bayan ta sauka daga motar ta saka masa albarka ta wuce ciki, barin layin yayi yana hawa saman titi kiran Ahmad ya shigo wayarsa, dauka yayi ya daga ya kai kunne Ahmad yace “Ka koma asibitin ne?” Abuturrab yace “Aa” Ahmad yace “Ohk anjima xan shigo in sha Allah, ka tambayi Umma if there is anything sai kayi masu tunda kaga ba

kowa…” Abuturrab dake ta sauraronsa ya tabe baki yace “Umma tace tana yawan ciwon cikin, and what is the cause?” Ahmad yace “Da ka shiga ka tambayi likitan da yayi admitting dinsu mana” Abuturrab yace “Kai na tambaya” Ahmad yace “Ohk tunda ni ka tambaya bari in baka amsa, duk xamanku tare da ita a gidanka ka ta6a ganin tayi Period?” Abuturrab ya juya ido yace “Period? Meye

hakan?” Dariya Ahmad yayi yace “Al’ada” Shiru Abuturrab yyi, Ahmad yace “Toh bata al’ada, da Umma ta ga hakan sai ta kai ta asibiti aka daurata kan magunguna, tun sannan kuma shine take ciwon mara…” Abuturrab yace “Toh dole ne sai anyi jinin?” Ahmad yace “Of course dole ne, although wasu matan

basa yi kuma suna haihuwa a haka, akwai mata da yawa da xaka ga a shekara sau biyu suke al’ada kuma suna haihuwarsu lafiya lau babu wani abun dake damunsu, so in her case….” Abuturrab ya katse sa yace “What i want to understand here now is, so ake ta fara al’adan yasa aka kai ta asibiti ko me?”

Ahmad yace “Eh mana, ana son sanin ko nata normal ne ko kuma Hormonal Imbalance ne ya janyo hakan, idan Hormonal imbalance ne kaga dole sai an ci gaba da yi mata medication har Allah yasa ta fara din, sannan ciwon maran da take ai jini ya kamata tayi ba ciwon mara me tsanani haka ba” Abuturrab ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Allah ya sauwake” Ahmad yace “Ameen…” Abuturrab yace

“Sai anjima” daga haka ya katse wayar. Asibitin ya sake komawa, yana shiga ward din Maimoon ta daga kai ta kallesa da mamaki, a ranta kuwa cewa tayi me kuma ya dawo da wannan mutumin nan, tunda Jiddah dake xaune saman gadon ward din hannunta rike da cup din shayi ta hada ido da shi ta sunkuyar da kanta taki dagowa, Maimoon ta mike tana kallonsa tace “Ga kujera yaya” Yace “Nace maki xan xauna?” Ta girgixa kai ta koma ta xauna a ranta tace oho dai, ya kalleta yace “Ke me ya hanaki xuwa islamiyyar?” Ta xaro ido tace “Toh ai yaya saboda xan tsaya da Jiddah a asibiti ne Umma xata koma

gida, kaga babu kowa a nan din” Ya d’an kalli Jiddah da taki dago kanta yace “Tace maki bata ji sauki bane?” Maimoon ta kalli Jiddah, ta washe baki tace “Wai kin ji sauki Jiddoh?” Ko kallonta Jiddah bata yi ba, Shi dai kallonta kawai yake, mika ma Maimoon cup din shayin tayi, Maimoon tace “Har yanxu kina jin aman?” Jiddah ta girgixa mata kai kawai, Maimoon tace “Amma ya isheki?” Jiddah ta gyada mata kai, Maimoon ta amsa Abuturrab yace “Mayar mata ta shanye” Maimoon ta d’an kallesa tace “Cika

mata cup din fa…” Dakatar da ita yayi yace “I said give it back to her” mika ma Jiddah tayi, Jiddah tace “Ni amai nake ji” Yace “Eh amsa idan kin shanye sai kiyi aman” Karban shayin tayi a hankali a hannun Maimoon, ya ciro ATM card dinsa a wallet dinsa ya mika ma Maimoon yace “Ki ciro min kudi” ta kallesa da sauri tace “A ina yaya? Ai babu Bank a kusa…” Yace “Ko ma ina xaki ciro kije ki ciro ba ruwana” nan da nan mood dinta ya canxa ta amshi Atm card din ta mike tace “Nawa xan ciro?” Yace “Talatin” Kofa ta

nufa tana cika tana batsewa, ya bi ta da kallo har ta bude kofar sai kuma ta juyo ganin kallonta yake ta seta fuskarta tace “Yaya pin din fa?” Yace “Ki kira Ramlah ki tambayeta” Ficewa tayi daga ward din ta kulle kofar, ya kalli Jiddah ganin ta ajiye cup din saman gado ta hade kai da gwiwa, karasawa yyi ya dauke cup din shayin ya ajiye a table yana kallonta, ta dago tana rufe idonta yace “Are u still feeling pain?” Da kyar kamar xata yi kuka tace “Yanxu ya fara” Kafin yace komai ta fara kokarin sauka daga

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button