JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 52

saman gadon ya bi ta da ido har ta shiga bandaki, yana ta tsaye har ta fito daga bandakin amma ta ki karasowa cikin ward din, bayan few seconds yace “An kawo maki wani kayan ne?” Kasa kallonsa tayi kuma taki cewa komai, yace “Magana nake maki” bata dago kanta ba tace “Ai ban sani ba” ya nufi jakar da Maimoon ta kawo daxu ya bude, Hijab ya gani da doguwar riga sai undies da sabulu da sponge, satan kallonsa kawai Jiddah take, ya dau sabulun da sponge ya nufeta ya mika mata, amsa tayi ta juya

ta koma bandakin, ya karasa saman gadon ya cire bedsheet din ya bar shi saman gadon snn ya fita ward din, nurses dake reception ya samu bayan sun gaisa da wata yace “Plss ki tura cleaner ward din farko, the bedsheet needs to be changed” Tace “Alright” ya juya ya fita xuwa wani babban kanti dake cikin asibitin, babu abinda ba a siyarwa a wajen, yana kallon matar dake ciki yace “Do u sell Sanitary pads?” Matar tace “Yes” guda uku ya siya ya bata kudi sannan ya juya ya koma cikin asibitin, cleaner


din ya tarar a ciki tana canxa xanin gado, bayan ta gama ta fita da na da, ya xauna kan kujera, bayan kusan minti sha biyar Jiddah ta fito daga bandakin, pad din da ya ajiye saman table ya nuna mata ta dinga kallon ledan sai kuma ta karasa ta bude tana kallon abun ciki, bata yarda ta kalli inda yake ba ta tafi gun jakan kayanta ta dau pant tana bobboyewa shi dai kallonta kawai yake, ta mike ta dau pad din ta koma bandaki, bayan ta fito ta dau wani Hijab din ta sa, gaba daya ta kasa kallonsa don wani

kunyarsa taji take yi, yana kallonta yace “Kina jin ciwon cikin yanxu?” Ta girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba, bai kuma ce mata komai ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, ta gaji da tsayuwarta sannan ta koma kan gadon ta kwanta ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa…. Karfe goma Maimoon ta shigo ward din fuskar nan nata babu annuri ta mika masa kudin da Atm card dinsa, yace “A ina kika samo?” Tace “Nima ban san wajen ba” Ta nufi Jiddah tace “Har kinyi wanka?” Ganin bacci take Maimoon ta xauna kawai, Maimoon tace “Lah canxa xanin gadon aka yi?” Abuturrab dai bai ko kalleta ba, Hannu ta kai kan ledan pad dake ajiye tace “Meye wannan kuma?” Xaro ido tayi ganin pads har


uku, ta saci kallon Abuturrab sai kuma ta mayar ta ajiye sannan ta xauna kan kujera, mikewa Abuturrab yayi ya nufi kofa ya fita. Yana fita Maimoon ta shiga tada Jiddah a hankali, Jiddah na bude ido tace “Wa aka kawo ma pad Jiddah? Kuma wa ya kawo?” Jiddah ta bi dakin da kallo ganin Aliyu baya nan ta mike xaune, Maimoon dake ta kallonta ta xaro ido tace “Ko dai Period kika fara?” A hankali Jiddah ta gyada


mata kai, Maimoon ta kara xaro ido tace “Kar dai Ya Aliyu gani yayi yaje ya siyo maki pad din, gashi ma naga an canxa bedsheet” Jiddah ta d’an turo baki, Maimoon ta kyalkyale da wani dariya tace “Atoh wllh shi yaga duhu, amma ke garin yaya kika bari ya gani? Tabb” Jiddah ta marairaice tace “Na tashi na shiga bandaki ban san na ma yi stain ba, kuma bedsheet din ma yayi stain” Maimoon sai xare ido take, sai kuma ta kara fashewa da dariya tace “Toh sai yace maki me da ya gani?” Jiddah tace “Ni bai ce min


komai ba, kawai xuwa yayi yaje ya siyo pad din” Maimoon ta tabe baki tace “Ai ko shi yaga duhu, yanxu dai wannan pad din sai kiyi wata biyar ma kina amfani da kayanki bai kare ba, har mu ma mun samu, kinsan fa shi ya Aliyu bai iya siyayyan hankali ba, don ma ba pack din gaba daya ya siyo maki ba, amma don Allah da wani ido kika kallesa bayan yaga period dinki” Jiddah ta ji kamar ta fashe da kuka,


Maimoon tace “Idan nice ke wllh ko a gyalena fuskewa xanyi ai bani nace ya gani ba” Jiddah dai bata kuma cewa komai ba amma ita kanta tasan taji kunya sosai ba kadan ba, she wish that never happen… Har yamma da aka sallami Jiddah Abuturrab bai koma asibitin ba, Ahmad ne yayi driving dinsu ya maida su gida, Umma har lkcn bata san Jiddah ta fara period ba, balle Ahmad, suna komawa gida Jiddah ta wuce daki ta kwanta sai bacci…..

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button