A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A BAKIN WAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

๐Ÿ‚A BAKIN WAWA๐Ÿ‚
Akanji magana
1
Tafiya take a hankali kamar bataso dukda kuwa da ranan da lokacin da’aka sauke ta,amma ahaka take tafiya tamkar bata taka ba,sai dai kuma duk takun da take ji take tamkar ana karawa zuciyar , wani tukukin bakin ciki take ji a duk sanda ta dawo gida,ta tsani gidan,ta tsani mutanen cikin gidan duk da kuwa cewa gida ne na gani na fada duk Wanda ya kalli gidan sai yakuma kalla amma ita bata ganin wannan, yafiye Mata ma ace a acikin daji take rayuwar ta. Tana tunanin da ya zame Mata jiki,ya zame Mata abokin hira ya zame Mata abokin shawara,har ta karaso bakin kofar gidan batare da tayi sallama ba kawai ta Shiga cikin katafaran parlourn,kamar yarda tasani hakan ta gani gaba daya Yan gidanne a zaune a parlour suna hira yaran kuma sun sa uniform na islamiyya,hirar su suke hankali kwance suna raha batare da ta kalli kowa ba ta fara hawa sama,Abban su ne ya ankara da ita,
yace’ Ummusalma,
Cak ta tsaya batare da ta juyo ba,be damuba yacigaba da cewa”
‘ kindawo kuma ko sallama babu zaki Shiga ciki kamar Baki ga kowa ba??
Batare da ta juyo ba kawai tayi nodding kanta ta wuce.
Mahaifiyar suce tace ohhh ni sha’anin yarinyar nan har tsoro yake bani Anya kuwa ba gamo tayi ba?
Abbanne yace ba wani gamo kawai iskanci ne da rashin mutumci kuma Zan sauke Mata shi bazan lamunta ba, tafadi Abinda ke damun ta amma taki,gar ta daurawa kanta hawan jini,

Nikuwa gani nake kamar mutanen boye ne haka kawai fah Rana daya ta dawo haka ai dole mu Mata uzuri ko de.
Be kaida magana ba daya daga cikin yaran

Yace’ Mama wai ita yaya salama bazata ke zuwa islamiyya bane ?
Daya yaranne yace ehhh mama Naga tunda muke ban taba ganinta taje ba sai dai mu muje ita kuma a Mata nata karatun a gida.
Daya yarinyar ce tace to ku ina ruwanku nima haka na taso na ganta bata zuwa.ku tashi ma mutafi kar muyi late,
Mamance tace kunga ku tashi maza maza ku tafi

Haka suka tashi suka yiwa iyayen sallama suka wuce,bayan sun tafi Abban ya kalli maman
Yace’ kinga saratu wannan yaran wataran sai sun mana tambayar bamu da amsar su na tabbata idan sun dawo sai sun nanata ta
Numfasawa tayi
tace’ Alhaji kyalesu Dani suke zancen ni bansan wannan wacce irin masifa bace yara sun bi sun damu da lamarinta,
Allah ya kyau haka kawai ya iya fada
Taci gaba kaga lokacin da tayi rashin lafiyan nan ma haka suka bi suka damu suka takurawa kansu kamar nice akace bani da lafiya
To ya zakiyi sai hakuri ai
Ahaka sukaci gaba da maganar su de

๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
Ummusalma kuwa a daki kawai uniform dinta ta cire ta Shiga wanka,ta dade kafin ta fito tana goge jikinta da karamin towel ta nufi gaban mirror ta zauna tana kallan kanta ta tunanin ta fara shin sai yaushe ne Zan Kara ganin murmushi a fuskata?yaushe Zan fita daga cikin damuwar da nake? Sai yaushe ne zanyi rayuwa irin ta kowa da yakeyi?????
Me ma zanyi don na Nemo wa kaina mafita?me nake so na zama don na cimma burukana? Wazan samu mai gaskiyar da zanyi sharing problem Dina dashi??????
Akoda yaushe idan har zata kalli kanta a mirror to wanan tambayoyin take yiwa kanta
Haka ta cigaba da tunanin daga nan kuma ta dauki spray na fesa tasa kaya,ta kwanta Kenan don ta samu tayi bacci sai kuma ta tuna yau malaminta zai dawo daga tafiyar da yayi,a hankali ta tashi ta dauko jakarta cikin wardruppe inda take boyewa don bata so asan tana karatu,ta dawo ta zauna bakin gado ta fara haddarta ta Qur’an har sai da taji ta iya sannan ta dauko sauran darasat din Suma tayi hadda tanan tanayi har aka Kira la’asar sannan tayi sallah ta zauna jiran malaminta don koda wasa bataso yanzu Karayin sakacin da tayi a baya bazata Kara bada wata kofar da za,a kuma yimata Abinda Akayi Mata ba abaya,tana nan tunanin da yazame Mata jiki har lokaci yayi bata sani ba sai da taji knocking sannan ta tashi taje ta bude mai aiki ce
Tace’ malamin ki yazo, nodding tamata kafin taje ta dauko jakarta
Itakuwa mai aikin yanzu mamakin ta take yanzu da Dane tace Mata haka batare da tace’ Mata madam ba shikenan aikinta ya kare a gidan,da sauri tabar wurin gudun kar ta fito.

Karatu take cike da nutsuwa tana fitar da kowanne harafi daya bayan daya kamar yarda yakoya Mata kuma ba laifi ta iya kuma tayi don ansamu cigaba sosai,harta Gama duka darasat din sannan malamin yace’ Alhamdulilla yanzu zamu Kara amaki shafi ko kuma shafi biyun za,a muyi
Biyu kawai tace
Jinjina Kai kawai yayi don mamaki take bashi da dane sai ta Gama shanya Shi sannan zata fito kuma tana zuwa zatace aya daya zai Kara Mata amma yanzu ita ce har shafi biyu abin sai godiyar Allah,haka ya Kara duk abubuwan da sukeyi har lokacin tashin su yayi har yayi addu’a zai tashi tace’ karka fada ina karatu,haka kawai ta fada ta shige cikin gida
Ikon Allah yace a cikin zuciyar sa kowa zai fadawa kuma?
Kasancewar a garden suke karatu hakan yasa ya fito don tafiya yafito harabar gidan yaga Alhaji zai fita da sauri ya karasa suka gaisa har ya Mike zai tafi sai yaji Alhajin nacewa ince de yanzu tana karatun,
Tunda yake da Alhaji beta tambayarsa tana karatu ba ko batatayi amma yau shine ke tambayarsa?
Bakaji ne bane
Da sauri yace ahh ai Alhaji lamarin ta sai addu’ah don shiru kawai take min ya fada cike da daridari
Cikin washe Baki Abba yace ahh to tototo Allah ya sauwake ya shige motarsa ya bar Malam da dunbin mamaki,shima haka ya nufi inda yayi parking din machine dinsa ya hau ya tafi.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page