AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 51-60

*PAID.*????️=5️⃣3️⃣↪️5️⃣4️⃣

Cikin girmamawa Hadiza ta amsa da to, sannan ta yi waje can wajan kofar baya na kitchen, ta samu Azima zaune tana tsinke fulani tana wurgarwa, Hadiza ta ce

“Azima meke damunki?” ɗagowa tayi ta girgiza kai alaman ba komai

“To ki zo mu haura sama na nuna miki part din Oga Al’Mazeen zai dawo nan da sati biyu, Hajiya Lawiza tace

Ki fara karkaɗe kura” zunbur Azima ta miƙe  tana fadin “muje”

     saman suka haura step na hawan uku can ne part din Al’mazeen, kasancewar baya son hayaniyar gidan, shiyasa idan yana gari ya dawo office yake hawa ya zauna a can shuru abunsa, harta ƙaramin kitchen akwai a saman, shiyasa baya damuwa da a kawo masa abinci, dan baya so ma yana cin abincin gidan dan bai yarda dasu ba, suna iya zuba masa abinda ba haka ba a cikin abinci.

       Tunda suka fara taka step din bugun kirjin Azima ya tsananta, Hadiza ke gaba Azima na binta a baya, har suka je bakin kofar parlourn Hadiza tasa key ta buɗe suka shiga, duk da mai dakin ya shekara baya nan amma har yanzu da kamshin turarensa na tashi, sai kuma uban kura kasancewar idan baya nan babu mai cewa a dinga bude dakin ana karkaɗewa, Hadiza ce ta kalli Azima ta ce

“Azima bari na tayaki dan kuran yayi yawa”

“A’a ki bar shi kawai Hadiza, ai aikina ne je ki kawai” 

“Yanzu zaki iya wannan aikin ke daya?” shuru Azima ta yi bata ba wa Hadiza amsa ba,ganin haka yasa Hadiza ajiyewa Azima su tsintsiya da mopa dasu omo da dai kayan aiki, har Hadiza zata fita Azima tace

“Dama kin tafi da wa innan kayayyakin naki dan ba amfani zanyi dasu ba” da mamaki Hadiza ta juyo ta ce

“To idan ba kiyi shara da tsintsiya ba dame zakiyi?”

“Ban taba shara da tsintsiya ba” Azima ta faɗa tana zuwa wajan jikin hoton da ta hango, hannu tasa ta goge hoton, nan take fuskar AL’MAZEEN ya bayyana, rasssrasssrasss!! ƙirjinta ya buga ta ja da baya tana girgiza kai, Hadiza ta ce

“Karki tsorata, shine Al’mazeen ɗin, karki ga fuskarsa a haɗe mutum ne mai saukin kai, nan gidansa ne, amma idan kika ga yadda yake rayuwa a cikinta sai kin tausaya masa” Hadiza ta fada tana matsowa kusa da hoton tasa tsummar dake hannunta ta goge wani wanda suke su biyu ta ce

“Kinga wannan? Sunansa NAWAZ babban aminine ga AL’MAZEEN,idan har kika ga Al’Mazeen na fara’a to yana tare da Nawaz, shi Nawaz a kaduna yake,kuma dukkansu likitoci ne, sabida tsananin shaƙuwa da son da suke yiwa juna,bayan sun bude asibitinsu suka saka masa suna mai harufan sunayensu *ALWAZ HOSPITAL* na Nawaz na shi na kaduna, shi kuma Al’Mazeen na shi na nan kano, yana da kyauta,baya da kyashi, yana da taimakon duk wani na kasa da shi,duk yadda zan baki labarin Al’Mazeen yafi haka, amma idaa ya dawo zaki tabbatarwa kanki” Hadiza na gama fadi ta juya ta fice.

Girgiza kai Azima ta hau yi, Banju dake jikin Azima yaji a jikinsa tabbas idan bai bar gidan nan ba, AL’MAZEEN shine makarinsa na farko a karo na biyu, to amma taya zai bar gidan? dan ya sha yunkurin haka amma zaiji kafafunsa tamkar an dauresa ne.

  Baya-Baya Azima ta yi ta koma jikin kofa ta bude blue eye dinta ta zaro dogon harshenta tana busar da wani tururi shi ba fari ba, shi ba baƙi ba, shi ba blue ba, tana hura wanna iskan hayakin nan take parlour da dakin da toilet din da kitchen din suka zama sabbi dal, harshenta ta maida sannan ta saka key a kofar ta shige bedroom ta zama macijiya ta hau gado ta kwanta dan bacci take ji, a macijiyar tayi kwanciyarta ta hau bacci.

       ????????????????

“To yanzu Aziza a ganinki taya zamu je kano? Khalil ya hana, Mom kuma ta biye masa,kuma kinga yanzu ne nake da freedom bayan aure kuma sai abunda Allah ya yi, ga shi yanzu bikin saura wata daya da sati biyu, bai ma cika da sati biyun ba, wlh na rasa yanda zanyi” ajiyar zuciya Aziza ta sauke ta ce

“Anty Sulty, abubuwa suna shirin cakuɗe mana,ni a ganina ya kamata mu maida hankali a guda daya”

“To wanne kenan Aziza?”

“Bikinki! Kinga kamata yayi ace mu maida hankali a kan shirye-shirye,idan yaso bayan anyi auren a lokaci hankalu zai kwanta,idan ya so sai mu dubi gaba”

“Tabb lallai Aziza na tabbatar har yanzu da ƙuruciya na yawo a kanki, taya Khalil zai bar ni da aurena muje yawon gari ya gari neman Azima? A yanzu ma da ba ayi auren ba ya na ƙare? Gaskiya wannan shawara taki bata yi ba, ni wlh wannan biki da an bar sa idan na cika shekara ashirin sai ayi! tinda yanzu ina sha tara” ta faɗa da fuskar haushi, waro ido Aziza ta yi ta ce

“Cab Anty Sulty shekara ashirin fa kika ce? to wlh da a rugarmu na yankin kwana ne ace kamarki bata yi aure ba wollah ko zanar kofar gidanku bakki iya fita sabida gori da habaici da bakar magana, kin ganmu nida Azima, shekararmu sha biyar amma yadda kika san kamar mun shekara dari ne bamuyi aure ba, dan a al’adan rugar yankin kwana yarinya tana da shekara goma za a fara yi mata wankan kindirmo, tana shiga sha daya za a aurar da ita”

” a shekara sha dayan!?” Sultana ta faɗa tana zaro ido

Aziza ta ce

“Wlh da gaske Anty Sulty”

“Tabdijam, lallai kam, ai mu kam nan ke baki isa aure ba, amma da shike zamani ya canza ana iya miki, amma karatu ne yafi dacewa dake, ina son zuwa kauyenku”

“Tab to mu dai a can kinga bamu san wani abu karatun boko ba amma akwai manyan malaman Muhammadiyya,kasancewar muna can cikin jeji ne amma bamu da wannan duhun kan na jeji muna da ilmin addini sosai, amma In sha Allah idan na koma zan wayarwa da mutane mahaifata kai ta hanyar karantar dasu ilmi daga cikin wanda na samu daidai gwargwado, tabbas na yarda ilmi ginshiƙi ne na rayuwa,ilminka baya cika kuma sai ka haɗa duka biyu a kanka, farko sai ka ajiye ilmin da zai ceceka ranar lahira, sannan ka kara da na bokon wanda shima ta sanadinsa zaka iya shiga aljanna, Allah ya bamu ilmi mai albarka, rugarmu kuma In sha Allah idan Hamma Khalil ya bar ki zakije, amma fa karkije ki ƙi dawowa”????

“Amin ya Allah Aziza, hahaha taya zan ƙi dawowa?”

“Idan kikaji dadin rugarmu mana”

“Humm ke dai, ai kya bari naje na ganewa idanuna ko?” Aziza ta yi murmushi ta ce

“Ai shiyasa ban baki labarin ni’imar dake yankin sassaninmu ba” Sultana ta yi dariya ta ce

“To naji, kar dai ki shashantar da 

maganata”

“To abunyi shine kawai ki ƙara tuntubarsa” Sultana ta jinjina kai tana fadin

“Ok zanyi hakan In sha Allah,ina zuwa” ta faɗa tana ficewa a dakin.

      @@@@@@@

Kamar yadda Aziza ta cewa Sultana ta kara tuntubar Khalil da maganar ya bar su suje kano hakan kuwa akayi, ganin ta takura yasa yace ta bari to idan su Nawaz suka dawo aka karasa saita komai sai taje tayi kwana biyu idan ana biki saura sati daya, tasan halinsa baya canza magana dan haka ta amsa da to, amma a zuciyarta ta yi lissafin garin da zasuje ya kai shidda, tace ai ba ayi auren ba, balle idan ta tafi tana tafiya akan wutar jahannama (Allah ya kiyashemu amin).

        ????????????????

Tunda aka shiga saura sati su Nawaz su dawo, Mom dasu Sultana da Aziza wacce faduwar gabanta ya tsananta a kwana biyun nan wanda ta rasa dalili hakan, suke shirye-shiryen dawowarsu Nawaz da Al’mazeen, da aka shiga satin karshe murna a wajan Mom da sultana abun sai wanda ya gani, Aziza ta kasa gane ita wani hali take ciki, shin murna take yi ne ko akasin haka, ta bangaren Azima ma kullum tana sama part din Al’mazeen zata shiga ta gyara ta zama macijiya ta kwanta tayi baccinta.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button