LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

???????????? LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA

BINTA UMAR ABBALE
~®BINTU BATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAG’A????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

NA FARA DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN K’AI ALLAH KAYI DAD’IN TSIRA GA ANNABI MUHAMMADU (SLW) DA ALIHIN SA DA SAHABBAN SA BAKI D’AYA

TSOKACI

WANNAN LITTAFIN K’IRK’IRAR RE NE DAGA NI MARUBUCIYAR BAN YI DAN WANI KO WATA BA, WANDA YAGA YAYI DAI-DAI DA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE

KUNA INA DUBUN DUBAN MASOYA NA, A DUK IN DA KUKE INA MUTUK’AR ALFAHARI DAKU WALLAHI KUNA DA DA BABBAN MATSAYI A CIKIN ZUCIYA TA, HAKIKA BANA RAINA MASOYI DUK INDA YAKE INA MUTUK’AR K’AUNAR KU SOSAI DA SOSAI

MACE MAI KARAMCI MACE MAI AMUNCI MACE ME MUTUNCI MACE MAI KIRKI MACE MAI DATTAKO MACE ME KYAWUN ZUCIYA MACE ME SON CIGABAN WANI MACE ME AIKI DA ILIMINTA


HAUWA S ZARIA MAMAN USUWAN


HAK’IKA WANDA BAI SANKI BA SHINE ZAI MIKI MUMMUNAR FAHIMTA, INA ROK’ON ALLAH YA SHIGA LAMURAN KI YA DAFA MIKI A DUKKANIN ABUNDA KIKA SA A GABA, UBANGIJI ALLÀH YA RAYA MIKI ZURI’AR KI

ALHERIN ALLAH YA ZO IN DA KIKE ZAINAB ABDULLAHI REAL SHAXXI KIN IYA KIN HUTA INA MIKI FATAN ALKAIRI A RAYUWAR KI PEGE D’IN FARKO NA SADAUKAR MIKI DASHI KIYI YADDA KIKE SO DASHI

ALLAH MAI MUTANE ALLAH D’AYA GARI BAM-BAM HAKA KURUM SAI UBANGIJI YA HAD’AKA DA MUTUM ME KARAMCI ME SONKA DA SON ABUNKA ALLAH NA GODE MAKA DA SAMUN KI K’AWATA TA KAINA INA MIK’O GAISUWA TA GARE KI


FAUZIYYA MU’AWUYA


ALLAH YA SHIRYA MIKI ZURIA YA BAKU ZAMAN LAFIYA DA MIJIN KI

BAZAN TAB’A MANCE ALKAIRIN KI BA


RAHAMA ALIYU


WANNAN MA NAKI NE INA YINKI IYA WUYA ANA TARE????????❤

????1

Misalin k’arfe biyar da rabi na yamma

Wasu yara na hango sun
yanko da gudu suna ihu! tare da fad’in “Ladidiya me kwarkwata a tab’a kad’an ta sosai kai, a tab’a ta kad’an ta ce kwarkwata ta dame ta a tab’a ta kad’an ta ciro kwarkwata,ladidiya me kwarkwata yeeeee!!! Ladidiya me kwarkwata!!! Da k’arfi suke fad’a suna gudu sosai dukanin su da allo a hannunsu da alama daga makarantar allo suka taso.

Can na hango wata yarinya ” yar kimanin shekaru tara zuwa goma ta yanko da gudu, daga kwanar da suka futo,hannunta rik’e da allo take gudu tun k’arfin ta k’okari kawai take ta riske su ta samu na duka ta daka babu abunda ya dame ta.

D’aya bayan d’aya suka dunga shigewa gida ba tare da ta kama ko d’aya ba, ya rage saura mutum biyu,, dukan su “yan hanyar sune,, gudu suke tana gudu, har ta riske su, rai a b’ace ta fuzgo hijab d’in d’aya daga cikin su, ta maka ta da k’asa,d’ayar kuwa ganin an kama ” yar uwar ta ya sa ta k’ara k’aimi gurin gudu sai da tayi nisa sosai ta tsaya ta tsinci dutsina ta dunga jefo wa Ladidi su, ko a jikinta, tunda Allah ya sa ta kama guda ta taki sa’a, hawa tayi kan “yar mutane ta shak’o wuyanta tace” Dan ubanki wa kuke tsokana kuna gudu kuna cewa me kwarkwata,, Alawiyya ta fara k’ifk’ifta ido saboda tasan halin bak’ar muguntar Ladidiya sai kace me aljanu haka take da mugun k’arfi sosai take faffasa wa mutane baki,, cikin inda-inda tace”Wallahi bani nace su Shatu ne da Habiba suka fara tsokanar ki, don Allah kiyi hakuri” Ko a jikinta ta kai mata duka a baki tana cewa”Da dai ban ganki bane yarinya ni zaki rainawa hankali wallahi yau he na lahira ya fiki jin dad’i kin tab’owa kan ki bala’in….k’aik’ayi da taji kanta na damun ta dashi ne yasa ta daki kan da hannunta ta sosa sosai gami da dukan in da yake mata k’aik’ayi,, sai da ta tabbatar ta daina jin sosar ta dawo kan Alawiya ta kai mata mari a fuska, tace”Wallahi kika sake CE min me kwarkwata sai na ciro guda goma na sa miki a kanki”

Alawiyya tace”Kiyi hakuri bazan k’ara ba”duka ta kai wa bakin tana fad’in ki k’ara mana sai na zubar miki da hak’ora shegiya mummuna kawai”

Alawiyya tasa kuka ganin yadda jini yake zuba daga bakinta, ga hakurin ta guda na girgid’i kuma na gaba ne, hakuri kawai take bata.

Sai da ta gama dukanta iya son ranta sannan ta d’aga ta, ta gyara d’aurin zanin ta Wanda ya d’angale sama har kusan cinyar ta ana hangowa ta d’auki allon ta ta k’ara gaba ta bar Alawiyya kwance a gurin,, Can ta hango gefan Hijab d’in Habiba ta b’uya a wani lungu da alama b’uya tayi ganin ta wowar LADIDI, sad’af-sad’af ta k’arasa gurin ta jawo hijab d’inta sai ga Habiba kwance a k’asa ihu ta kurma ta mik’e a sittin ta ranta ana kare Ladidi ta rufa mata baya.

Tun daga nesa Lado me icce yace”Ga sababbiya nan fitanniya me k’arfin jinnu ta biyu maka “yar zata daka”

Da Sauri Malam Harisu ya kalli inda Lado yake kallo aikuwa ya hango “yar sa Habiba na gudu Ladidi na bin ta a baya, mik’ewa yayi da sauri yana fad’in ” Wallahi Ku bushiyar kuka ce a kan yarinyar nan bata Isa ta dukar min yarinya na na k’yaleta”

Kai tsaye gurin babanta ta nufa tana baki! Tasan k’aryar Ladidiya ta k’are tunda ga ta ga Babanta bata Isa ta dake ta ba,, kafin Malam Harisu ya an kara kawai yaji an in gije shi guri guda saura kad’an ya fad’i LADIDI tayi kukan kura ta dura kan Habiba ta kwantar da iita k’asa gami da haye wa ruwan Cikin ta ta kama dukan kayanta.

Cikin k’arfin Hali Lado me ice ya k’arasa gurin yana fad’in “Ke Ladidi me tayi miki kike k’okarin raunata ne, d’aga musu yarinya Dan ubanki in kin kashe ta Kakar ki me koko kika sa a bala’in”

Hannun guda tasa ta daddaki inda yake mata k’ai k’ayi ta Sosa ta sosa yadda ya kamata. Ta cire hannun ta tana fad’in “Kai lado me ice babu ruwanka kuma kar ka k’ara zagin Ubana idan ba haka ba zaka fuskanci hukunci ………Lado ya zare ido yana kallon ta da jin abunda tace wai zai fuskanci hukunci Lallai Ladidi kunyar ta ragaggiya ce, yace”Au! Nima zaki zage ni ne mara kunyar banza da wofi”

K’unk’uni Ladidiya ta fara yi tana fad’in “Wallahi ni ba mara kunya bace,shikkenan dan suna da gata sai su tsokane ni su gudu su masu iyaye nima ai ba daga sama na fad’o ba, Allah ne ya amshi ran iyaye na”

Sam! Lado bai ji abunda take cewa ba,yasan dai bazai wuce zaginsa take ba, sai yaja bakin sa yayi shiru gudun ta zage can gurin sana’ar shi ya koma ya zauna,, yana kallo Malam Harisu ya nufi gurin yana zagin Ladidi aikuwa ta hau dukan “yar sa tana rama zagin akanta, fad’i take” Haka kawai ai uba bai fi uba tana dukan Habibu tana ambato sunan Harisu tana zagi babu abunda ya dame ta, ya k’araso gurin gami da Kai mata duka ta goce ya samu “yar sa,dariya ta kwashe da ita mik’e daga kan Habiba ta d’auki allon ta sai dariya take k’yalk’yalawa ta mayar dashi mahaukaci tace” Wai shi dole sai yayi irin dukan su Salman Khan da Ashe kumar mutanan hindiya hahahahaha, Habiba Baban Ku Ashe d’an hindiya ne”” Malam Harisu kamar ya d’ora hannu aka don bak’in ciki, yana kallon ta wuce bagaz!-bagazan! Tana tik’ar dariya.

Lado yana gefe shima dariya kamar ta kashe shi fad’i yake”Kad’an daga iya shegen Ladidiya ta gidan Iya me koko kenan shiyasa na k’yaleta nayi zamana,, hahahaha” ya k’arashe maganar yana dariya

A fusace Harisu yace”Ai wannan yarinyar dole ne ma inje in ja mata kunne gaban kakar tata me koko idan ba haka ba wallahi sai na kai k’arar ta gurin me gari”
Ya k’arashe maganar yana d’ago Habiba dake kwance tana rik’e da bakinta inda leb’an ta na sama ya kumbura suntum!

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button