LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

A mutuk’ar gajiye ya shiga gidan, Mai koko na tsaye tana aikin tata sai sauri take saboda magari ba tayi,, guri ya samu ya aje abun sana’ar tashi,, ya zauna kan tabarma cikin gajiya, yace”Iya sannu da gida da aiki”

“Yawwa Sannu ka dawo kenan”?
“Eh Wallahi Allah yayi mana dawowa”
“To masha Allah” Iya tafad’a ta cigaba da abunda take
Kishingid’a yayi yace”Iya ina Ladidi take ne? Yau naga aiki yayi miki dare, ko ta futa yawon da tasaba ne”?

Ajiyar zuciya ta sauke tace”Yanzu ta futa ashe ba ka ganta ba, tana futa kana shigowa”

K’wafa yayi cikin b’acin rai yace”Wato yarinyar nan bata jin magana ko Iya”?

“To yaya zakayi ne, sai kayi mata addu’a k’uruciya ce take damunta”

“Nifa Iya babban bak’in ciki na da Ita rashin kamun kai da wasa da maza da take in taje dandali babu shirmen da bata yi wallahi”

“To wai yaya zakayi ne D’alha, nifa bana son kana takura mata, nasan duk abunda take k’uruciya ce watarana zata daina”

Shiru yayi ya daina wahalar da bakinsa domin yasan duk surutun da zaiyi Iya sai ta kare Ladidi duk wani iyashege da yarinyar take itace take daure mata gindi.
Mik’ewa yayi ya d’auki buta ya futa waje domin ya d’aura alwala.

Suna zauna gidin wata k’atuwar bishiyar mangwaro, sun kai su Tara zuwa goma duk sun kewaye ta itace shugaba,, duk sun mimmik’e k’afafunsu suna wasan nanje na gidan gona in an cinye mutum sai su kwashe da dariya har da burgima,, ihu! Suke suna fad’in Ladidiya don Allah yanzu ki sauke a kaina,, muga wa za’a kad’awa barbad’in tusa”
“Ku tsaya!Ku tsaya kuji! Ku tsaya kuji”! Ladidi ce take fad’in haka.
Tsit! Sukayi suna sauraron ta,, k’aykayin da taji kanta nayi ne ya katse mata abunda take so tace, cire d’ankwalin tayi ta jefar k’asa ta sanya hannuwan ta biyu ta dunga kartar kan tana lumshe ido,, dad’i take ji sosai in tana sosawa, shiru sukayi kowa yana jin tsoro kar yayi dariya ta doke shi,, tafi minti biyar tana aikin sosa kanta sannan ta cire hannuta tana muzurai,, kallonsu take ta sha kunu domin shaf ta mance a inda take idan tana Sosa kai kwata-kwata mance komai take,, so take taga ko akwai wanda zai mata dariya a cikin su, sai taga duk sun nutsu,, ba tare da ta mayar da d’ankwalin nata ba tace” Ku san me”? Had’a baki sukayi gurin fad’in “A’a sai kin fad’a”

Dariya ta kece da ita tace”Wallahi duk wacce k’arshe ya sauka a kanta to ta saddak’ar da cewar sai anyi mata ihu an k’ada barbad’in tusa kuma har gida za’akai ta anai mata ihu! Kun yarda ko”?

Ihu! Suke suna fad’in “Mun yarda” Mun yarda”

“To kowa ya mike k’afarsa a sako daga farko”

Mik’e k’afafun su sukayi, ta fara yi musu,, duk wacce ta futa sai ta koma gefe tana murna ya rage saura mutum biyu Murja da Indo kenan duk sunyi tsuro-tsuro dasu,, ita ko Ladidi sai dariya mugunta take musu,, Nan je na k’arshe ya sauka a k’afar Indo ta mike da sauri tana murna,, Murja ta mik’e da sauri zata gudu,, Ladidi ta tad’o k’afar ta, tafad’i gurin ,sai suka dauk’i ihu!!!!! Yeeeee!! “Murja warin wando Murja mai wari tusa,akad’a mata barbad’in tusa, a kad’a mata bar bad’in tusa!!!! Su ka ture Murja suna yi mata ihu!! Suna ja mata k’afafu saurin muryar Ladidiya yafu na kowa tashi a gurin.

Hankalin masu sai da nama fura da nono da duk wani mai sana’a gurin ya dawo Kansu,, Mutari me nama yace ” Wannan yarinya baza ta tab’a barinmu mu huta ba wallahi duk itace shugaba” Haliru me fura da nono ya nufi gurin a fusace yana fad’in “Bari naje nayi maganin su” Yana zuwa gurin ya d’aga murya yana fad’in “Ke ” yar gidan mai koko, zan ci ubanki wallahi idan baki ja zugar ki ba kun bar gurin nan ko an fad’a miki kowa mahaukaci ne irin ki”?

Tsittt! Sukayi jin abunda Halliru yake fad’a, Ladidi ta kura masa ido tana jin takaicin zagin da yayi mata, amma tasan abunda zata yi masa,, ganin sun daina ja mata kafa yasa ta mike da sauri zata gudu, Ladidi tayi saurin damk’e ta tana fad’in ” Murja me warin wando Murja me warin tusa yeeee! a kad’a mata barbad’in tusa!!! Aikuwa sauran suka d’auka gurin ya k’ara kacamewa da ihu!! Halliru ya gama b’ab’atun sa ya hak’ura ya tafi domin ko sauraron sa ba suyi ba, haka suka tasa Murja suna ihu! gami da dungure mata kai, har suka kai ta gida,, sai kuka bak’in ciki take,,nan ta basu umarni tafiya kowacce ta kama hanyar gidan su, ita kuwa dandali ta k’ara komawa domin ta aiwatar da k’udirinta. Kan Halliru a ganinta tana raye babu wanda ya isa ya zagar mata iyaye ba ta hukun tashi ba,,

Ta bayan gatangar da suke zaune ta bi,, sosai gurin yake da kwazazzabai gami da ra muka katangar ta d’ane sosai ta hau ta dura, a hankali ta tsuguna tana tattaro k’asar gurin,, zanin ta ta kwance ta zuba k’asar a kai ta nufi inda suke zaune,, Halliru na can gurin wani mai rake suna magana, shi kuma Mutari mai nama kasuwa ta bud’e ana ta cini ki,, da sauri ta bud’e doguwar robar dake cike da nono ta zazzage wannan k’asar me uban yawa da ta d’ebo ta cikin zaninta, ba tare da ta d’aura zanin ba ta bar gurin kamar walk’iya.
Halliru ya dawo gurin da sauri hannunsa rik’e da wata roba me kamar kwanon sha, da ledoji a hannun sa,, wasu matasa na bin bayan sa, da sauri ya bud’e robar nono sa ya zura k’aton ludayi da yake motsa wa,, sai yaji gurin-gurin d’in dutsina da k’asa a ciki,, salati ya rafka da sauri ya zaro cocilan d’insa daga cikin aljuhu yana haskawa, innallahi wa’inna ilahi raji’un , nono ya rine! Ya koma jajazur dashi, ya kalli Mutari mai nama dake hada-hadar sallamar jama’a yace”Mutari”!!!!!

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/23, 7:47 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

Komai yayi tsanani yana tare da sauk'i, cikar muminin mutum yarda da k'addara mai kyau da mara kyau, idan ubangiji ya jarrabe ka, da musiba ka karb'a hannu biyu kar kace wani ne yayi ma, ko da wani mutum ne silar faruwar haka to kasani babu abunda bawa ya Isa yayi face da sanin mak'agin ka, Ubangijin baiwa kenan alimul gaibu washahadati, ka mik'a masa al'amarin da sannu zai yaye maka damuwar ka, Allah kasa mu dace

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????4

Da sauri Mutari ya juyo jin irin kiran da Halliru ya kurma masa, baki na rawa yace”Akwai wanda yazo gurin nan bayan naje guri Umaru mai rake yanzu”?

Cikin mamaki Mutari yace”Gaskiya babu wanda yazo kan kayan ka ina kallo tun d’azu”

Kamar ya fashe da kuka yace”Zo kaga abunda akai min”
Mutari ya baro gurin sa da sauri yazo yana dubawa,, salati yasa yana mamaki tare da fad’in”Wannan aikin Ladidi ne wallahi, d’azu ba kaje har inda suke ba, ina jin kana zaginta” Halliru yace”To kuma da kace baka ga wanda yazo gurin ba”

“Tabbas ban ga kowa ba, amma na tabbatar da cewar Ladidiya ce zatayi maka wannan aikin, wallahi kasan ta kamar aljana take, sam ba’a ganinta a guri” Cikin fushi Halliru yace”Billahillazi sai sun biya ni kud’in nono na, idan ta saba yi wa wasu suna k’yaleta to ni wallahi bazan d’auki asara ba”

Murmushi Mutari yayi yace”Shiyasa d’azu kamar in ce maka kar kaje inda suke saboda nasan halin yarinyar bata da mutum ci wallahi shiyasa kaga ni bana shiga sabgar ta, ko kaman ta lokacin da ta watso min ruwan kwata kaina kasan ranar har nama da gurasa basu tsira ba sai da ruwan kwatar ya same su,, ko da na je na fadawa kakarta hakuri kawai ta bani, da k’yar na kara tayar da wani jarin”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button