LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


ALHAMDULLAHI

HAUWA S ZARI’A
Maman Usuwan

Ina taya ki murnar kammala littafin ki HAKA ALLAH YA NUFA KADDARA TACE ALLAH YA KARA BASIRA YASA SAKON KI YA ISA INDA KIKE SO


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????14

Suna k’okarin shiga da ita cikin gidan tana turjewa D’alha ya kwad’e mata k’eya yana fad’in “Zaki wuce muje ko kuwa,? Kin tayar wa da mutane hankali, gidan buhun ubanki zaki je ne” Ihu! Ta kurma, wanda yasa Mai koko da sauran jama’ar gidan mik’ewa tsaye da sauri sukayo waje suna salati! Kafin su rufe bakinsu, sai ga Ladidi an shigo da ita tana turjewa! Mai koko ta bude baki zatayi magana D’alha ya katse ta hanyar cewa.” Don Allah kar Ku tsorata da ganin ta, dama na fada muku tana raye bata mutu ba, ga shi a can bakin titi d’an Fulani ya gano ta,wanda shima labari ne ya riske har inda yake kiwo cewar ta mutu.” Mai koko ta k’araso gurin da jiki a sanyaye zuwa yanzu itama ta fara tsorata da al’amarin Ladidi, da muryar ta wacce tasha kuka ta gaji tace. ” Ladidiya dama baki fad’a rijiya ba, me yasa kika yi min haka Ladidi”? Turo baki tayi tace.” Nifa ban fad’a rijiya ba, kinga gurin dana b’uyar miki fa” Mai koko tabi hannuta da kallo, cike da mamaki da al’ajabi Matan da suke tsatstsaye a gurin, duk suka tsure sai zare ido suke burin su kawai su bar gidan, Mai koko tace.” Me yasa to duk aka duba ba a ganki ba”? Shiru tayi mata, D’alha ya dubi matan dake tsatstsaye, yace.” Ko wacce tana iya tafiya” aikuwa kafin kace kwabo duk sun zura takalman su, suna bangazar juna suka futa daga gidan, ko wacce cikin ta ya d’uri ruwa. D’an Fulani yace.” Ku zauna zamuyi magana ta fahimta” Mai koko taja hannun Ladidi suka zauna kan tabarma. D’alha suka zauna gan benci, D’an Fulani ya kalli Mai koko a nutse yace.” Al’amarin yarinyar nan ya soma bani tsoro saboda haka na yanke wata shawara.” Mai koko tace.” Ai kana da iko akanta tunda kai ka haifi mahaifiyar ta.” Yace.” NA yanke shawarar cewa gobe insha Allahu zan kawo malamin ruk’iya zai yi mata idan da makarai a jikinta sai a sulhun ta dasu”

Shiru tayi na minti biyu, ta d’ago kai tana kallonsa, tace.” Ba wai nak’i taka bane, gaskiya ka janye maganar ruk’iyar nan,domin su wad’annan mutane ba a haka dasu, idan kuma basu suka rab’e ta b,kaga sai a jawo mata su da hujja, abar maganar ruk’iya mu cigaba da yi mata addu’a” Dan Fulani da D’alha suka kalli juna, girgiza kai kurum D’alha yake yasan dama Mai koko baza ta yarda ba, shi ko D’an Fulani saboda tsabar haushi da takaici bai sake cewa komai ba. Ya mik’e yana musu sallama, sama-sama Mai koko ta amsa masa, D’alha ya mik’e domin ya raka shi. Mai koko ta dinga rarrashin Ladidi, da lallab’ata tamkar ba wacce tayi mata laifi ba, tace.” Tashi ga ruwan zafi can muje kiyi Wanka ko”? Mak’ale kafad’a tayi. Tace.” Akwai miyar kifi nan a fulas na aje miki sai ki siyo buredi” Mik’ewa tayi zaune tana Sosa kai tace.” Amma ni zanyi wanka na gaskiya” tace.” E amma zan cud’a miki baya.” Mik’ewa tayi tana tube kayan jikinta ita kuma ta nufi kicin din, bakin rijiya ta tsuguna tana wasa da ruwan Wanka, Mai koko ta k’araso da abun sabulu a hannuta tace.”Ladidi waye ya fasa miki leb’e haka? Ko garin tsalle-tsallen ki ne”? Hannuta tasa ta shafo gurin, girgiza kai tayi tace.” Wani d’an burni ne, kawai babu abunda nayi masa don zalin ci.” “A’a Ladidi nasan halin ki fa”? Iya tafad’a tana murza sabulu jikin soso. ” Kawai don na shiga gonarmu shine ya doke ni” “Wace gona kuke da ita Ladidi’? Iya. Ta fada cike da mamaki! ” Ranan da zamu wuce Kawu ya nuna min gonar tun kafin a gina gurin yace.”Tasu ce da babana.” “To yanzu na gane inda kika dosa” Iya tafad’a tana durzar jikinta da soso, ta cigaba da cewa ” Ladidi kin cika futuna me ya kai ki gurin nan, yanzu bs gonar su bace, domin sun siyar da ita dalilin haihuwar ki, ranar bakiji Kawun ki yana fad’in wani mai kud’i ya siya har da tasu Malam Tanimu da Manu ba” girgiza kai tayi tace.” Ni babu ruwana ko sun siyar ko basu siyar ba, in naga dama zanje ne” Mai koko tace.” To sai ki kiyaye domin mutanan burni ba dai-dai suke da na k’auye ba.” Zumb’ura baki tayi tace.” Aiko sai na rama abunda yayi min ko shugaban k’asa ne ya haife shi.” Mai koko dai shiru tayi domin bata so ta tsanan ta mata kar ta sake guduwa.

Kawu D’alha kuwa akwai abunda ya k’udura a ransa kan Ladidi. Sai da ya tabbatar da sunyi bacci sannan ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mai koko ya nufa, dama duk ranar da tayi ibilincin ta. To in ta kwanta bacci bata motsawa sai gari ya waye, Mai koko ma bacci take sosai ansha fargaba an gaji, reza ya futo da ita daga cikin aljinunsa ya kwance d’aurin d’ankwalin Ladidi a nutse a shafa sabulu da ruwa ya soma yi mata aski babu abunda ya dame shi. Har D’alha ya gama aske mata kai bata motsa ba, ya mayar mata da dankwalin ta ya daure mata kanta kamar yanda tayi, ya sunkuya ya tattare gashin da zube k’asa ya zuba cikin leda shara ya zuba yasa omo ya wanke hannunsa tass!!! . Ladidi bacci tayi sosai da sosai sam bata san inda kanta yake ba, sai wajan shiga da rabi na safe ta tashi lokacin Mai koko ta Dade da tashi tana can tana hidimar huta huta domin ta d’ora ruwan kuka. D’ankwalin ta take laluba kan shinfid’ar ta d’auka zata d’aura akanta tana tab’awa taji sumul tamkar gwiwa hannuwa biyu tasa tana shafawa, Ihu!! Ta kurma tana fad’in “Wayyo!! Mai koko wani ya aske min kai na” Mai koko ta aje icen dake hannunta da sauri ta nufi dakin. Tana shiga taga Ladidi ta d’ora hannu aka tana kurma ihu! Ga kanta sumul! Babu k’wallin gashi ko d’aya, cikin mamaki tace.”Ladidi waye yayi miki k’wal kwabo hak….. Kafin ta k’arasa muryar D’alha ta katse ta inda yake cewa.” Iya nine nayi mata aski saboda in cika rantsuwa bayan haka kuma da wahalar da ta bamu jiya, shiyasa na yanke wannan hukuncin a kanta.”

COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button